Kol 2
2
1To, ina so ku san irin yawan shan faman da nake yi dominku, da waɗanda suke a Lawudikiya, da kuma duk waɗanda ba su taɓa ganina ba. 2Sona a ƙarfafa musu zuciya, ƙauna tana haɗa su, har su sami dukkan mayalwaciyar fahimta tabbatacciya, da sanin asirin nan na Allah, wato Almasihu, 3wanda shi ne taska, wato maɓoyar dukkan mafifitan hikima da sani. 4Na faɗi wannan ne don kada kowa ya hilace ku da maganar yaudara. 5Don ko da yake a jiki ba na nan, ai, ruhuna yana nan tare da ku, ina kuwa farin cikin ganin kyakkyawan tsarinku, da dagewarku a kan bangaskiyarku ga Almasihu.
6Da yake kun yi na'am da Almasihu Yesu Ubangiji, to, sai ku tsaya a gare shi, 7kuna kafaffu, kuna ginuwa a cikinsa, kuna tsayawa da bangaskiya gaba gaba, daidai yadda aka koya muku, kuna gode wa Allah a koyaushe.
Dukkan Cikar Rai ga Almasihu Take
8Ku lura fa, kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al'adar mutane kawai, wato, bisa ga al'adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba. 9Domin a cikinsa ne cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata. 10A gare shi ne aka kammala ku, wanda yake shi ne shugaban dukkan sarauta da iko. 11A cikinsa ne kuma aka yi muku kaciya, ba kuwa yin mutum ba, amma wadda Almasihu ya yi muku ce, ta wurin tuɓe halinku na mutuntaka. 12#Rom 6.4 An kuma binne ku tare da shi a wajen baftisma, inda kuma aka tashe ku tare da shi saboda bangaskiyarku ga ikon Allah, wanda ya tashe shi daga matattu.
13 #
Afi 2.1-5
Ku kuma da kuke matattu saboda laifofinku, marasa kaciya ta jiki, Allah ya raya ku tare da Almasihu, ya yafe mana dukkan laifofinmu, 14#Afi 2.15 ya kuma yanke igiyar nan ta Shari'a da ta ɗaure mu da dokokinta, ya ɗauke ta, ya kafe ta da ƙusa a jikin gicciyensa. 15Ya ƙwace makaman masarauta da na masu iko, ya kunyata su a fili, da ya yi nasara a kansu a kan gicciyen.
Ku Ƙwallafa Ranku a kan Abubuwan da Suke a Sama
16 #
Rom 14.1-6
Saboda haka, kada ku damu in wani ya zarge ku a kan abin da kuke ci, ko abin da kuke sha, ko kuwa kan rashin kiyayewar wani idi, ko tsayawar wata, ko Asabar. 17Waɗannan kam, isharori ne kawai na abin da zai auku, amma Almasihu shi ne ainihinsu. 18Kada ku yarda kowane mutum ya ɓata ku, da cewa shi wani abu ne saboda, ya ga wahayi, ya kuma lazamta da yin tawali'un ƙarya, in ji shi kuma yana yi wa mala'iku sujada. Irin wannan mutum kumbura kansa yake yi ba dalili, sai ta son zuciya irin na halin mutuntaka, 19#Afi 4.16 bai kuwa manne wa kan ba, wanda ta gare shi ne dukkan jiki yake amfana, yake kuma a haɗe, ta wurin gaɓoɓi da jijiyoyi, yake kuma girma da girman da Allah yake sawa.
20Idan mutuwarku tare da Almasihu ta 'yanta ku daga al'adun duniyar nan, me ya sa kuke zama har yanzu kamar ku na duniya ne? Don me kuke bin dokokin da aka yi bisa ga umarnin 'yan adam da koyarwarsu, 21kamar su, “Kada ka kama, kada ka ɗanɗana, kada ka taɓa”? 22(Wato, ana nufin abubuwan da, in an ci su sukan ruɓa duka). 23Irin waɗannan dokoki kam, lalle suna da'awar hikima ta wajen yin ibadar da aka ƙago, ta wurin yin tawali'un ƙarya da kuma wahalar da jiki, amma ko ɗaya ba su da wata daraja ga sarrafar halin mutuntaka.
Currently Selected:
Kol 2: HAU
Highlight
Share
Copy
![None](/_next/image?url=https%3A%2F%2Fimageproxy.youversionapi.com%2F58%2Fhttps%3A%2F%2Fweb-assets.youversion.com%2Fapp-icons%2Fen.png&w=128&q=75)
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979