1
Kol 2:6-7
Littafi Mai Tsarki
Da yake kun yi na'am da Almasihu Yesu Ubangiji, to, sai ku tsaya a gare shi, kuna kafaffu, kuna ginuwa a cikinsa, kuna tsayawa da bangaskiya gaba gaba, daidai yadda aka koya muku, kuna gode wa Allah a koyaushe.
Compare
Explore Kol 2:6-7
2
Kol 2:8
Ku lura fa, kada kowa ya ribace ku ta hanyar iliminsa na yaudarar wofi, bisa ga al'adar mutane kawai, wato, bisa ga al'adun duniyar nan, ba bisa ga koyarwar Almasihu ba.
Explore Kol 2:8
3
Kol 2:13-14
Ku kuma da kuke matattu saboda laifofinku, marasa kaciya ta jiki, Allah ya raya ku tare da Almasihu, ya yafe mana dukkan laifofinmu, ya kuma yanke igiyar nan ta Shari'a da ta ɗaure mu da dokokinta, ya ɗauke ta, ya kafe ta da ƙusa a jikin gicciyensa.
Explore Kol 2:13-14
4
Kol 2:9-10
Domin a cikinsa ne cikin jiki dukkan cikar Allahntaka take tabbata. A gare shi ne aka kammala ku, wanda yake shi ne shugaban dukkan sarauta da iko.
Explore Kol 2:9-10
5
Kol 2:16-17
Saboda haka, kada ku damu in wani ya zarge ku a kan abin da kuke ci, ko abin da kuke sha, ko kuwa kan rashin kiyayewar wani idi, ko tsayawar wata, ko Asabar. Waɗannan kam, isharori ne kawai na abin da zai auku, amma Almasihu shi ne ainihinsu.
Explore Kol 2:16-17
Home
Bible
Plans
Videos