1
Markus 9:23
Sabon Rai Don Kowa 2020
Yesu ya ce, “ ‘In za ka iya’? Ai, kome mai yiwuwa ne ga wanda ya gaskata.”
Compare
Explore Markus 9:23
2
Markus 9:24
Nan da nan mahaifin yaron ya faɗa da ƙarfi ya ce, “Na gaskata, ka taimake ni in sha kan rashin bangaskiyata!”
Explore Markus 9:24
3
Markus 9:28-29
Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a ɓoye, suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da shi ba?” Ya amsa ya ce, “Sai da addu’a kaɗai irin wannan yakan fita.”
Explore Markus 9:28-29
4
Markus 9:50
“Gishiri yana da daɗi, amma in ya rabu da ɗanɗanonsa, ta yaya za a sāke mai da ɗanɗanonsa? Ku kasance da gishiri a cikinku, ku kuma yi zauna lafiya da juna.”
Explore Markus 9:50
5
Markus 9:37
“Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”
Explore Markus 9:37
6
Markus 9:41
Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ba ku ruwan sha a sunana, saboda ku na Kiristi ne, lalle, ba zai rasa ladarsa ba.
Explore Markus 9:41
7
Markus 9:42
“Idan kuma wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan ’yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyarsa, a jefa shi cikin teku.
Explore Markus 9:42
8
Markus 9:47
In kuma idonka yana sa ka zunubi, ƙwaƙule shi. Ai, gwamma ka shiga mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka cikin jahannama ta wuta, da idanu biyu
Explore Markus 9:47
Home
Bible
Plans
Videos