Yah 2
2
Biki a Kana ta Galili
1A rana ta uku sai aka yi bikin aure a Kana ta ƙasar Galili. Uwar Yesu kuwa tana nan, 2aka kuma gayyaci Yesu da almajiransa. 3Da ruwan inabi ya gaza, uwar Yesu ta ce masa, “Ba su da sauran ruwan inabi.” 4Yesu ya ce mata, “Iya, ai, wannan magana ba taki ba ce. Lokacina bai yi ba tukuna.” 5Sai uwa tasa ta ce wa barorin, “Duk abin da ya ce ku yi, sai ku yi.” 6A wurin kuwa akwai randuna shida na dutse a ajijjiye, bisa ga al'adar Yahudawa ta tsarkakewa, kowacce na cin wajen tulu shida shida. 7Sai Yesu ya ce musu, “Ku cika randunan nan da ruwa.” Suka ciccika su fal. 8Sa'an nan ya ce musu, “To, yanzu ku ɗiba, ku kai wa uban bikin.” Sai suka kai. 9Da uban bikin ya kurɓi ruwan da yanzu aka mayar ruwan inabi, bai kuwa san inda aka samo shi ba (amma barorin da suka ɗebo ruwan sun sani), ya yi magana da ango, 10ya ce, “Kowa, ai, kyakkyawan ruwan inabi yakan fara bayarwa, bayan mutane sun shassha, sa'an nan kuma ya kawo wanda ya gaza na farin kyau. Amma kai ka ɓoye kyakkyawan ruwan inabin sai yanzu!”
11Wannan ce mu'ujizar farko da Yesu ya yi, ya kuwa yi ta ne a Kana ta ƙasar Galili, ya bayyana ɗaukakarsa. Almajiransa kuma suka gaskata da shi.
12 #
Mat 4.13
Bayan haka sai ya tafi Kafarnahum, da shi da uwa tasa, da 'yan'uwansa, da kuma almajiransa, suka zauna a can 'yan kwanaki.
Yesu Ya Tsabtace Haikali
(Mat 21.12-13; Mar 11.15-17; Luk 19.45-46)
13 #
Fit 12.1-27
Idin Ƙetarewa na Yahudawa ya matso, sai Yesu ya tafi Urushalima. 14A cikin Haikali ya sami waɗansu dillalan shanu, da na tumaki, da na tattabarai, da kuma 'yan canjin kuɗi zaune wurin aikinsu. 15Sai ya tuka bulala mai harsuna ta igiya, ya kore su duka daga Haikalin, har da tumakin da shanun, ya kuma watsar da kuɗin 'yan canjin, ya birkice teburorinsu. 16Ya ce da dillalan tattabarai, “Ku kwashe waɗannan daga nan, kada ku mai da Haikalin Ubana kasuwa.” 17#Zab 69.9 Sai almajiransa suka tuna a rubuce yake cewa, “Kishin Haikalinka ya ci raina matuƙa.” 18Sai Yahudawa suka amsa masa suka ce, “Wace mu'ujiza za ka nuna mana da kake haka?” 19#Mat 26.61; 27.40; Mar 14.58; 15.29 Yesu ya amsa musu ya ce, “Ku rushe Haikalin nan, ni kuwa in ta da shi a cikin kwana uku.” 20Yahudawa suka ce, “Sai fa da aka shekara arba'in da shida ana ginin Haikalin nan, kai kuwa a cikin kwana uku za ka ta da shi?” 21Amma haikalin da Yesu ya ambata jikinsa ne. 22Saboda haka bayan an tashe shi daga matattu, almajiransa suka tuna ya faɗi haka, suka kuma gaskata Nassi da maganar da Yesu ya faɗa.
Yesu Ya San Zuciyar Kowa
23To, sa'ad da yake Urushalima lokacin Idin Ƙetarewa, mutane da yawa suka gaskata da sunansa, saboda ganin mu'ujizan da ya yi. 24Amma Yesu bai amince da su ba, 25domin ya san zuciyar kowa, ba kuma sai wani ya shaidi mutum a wurinsa ba, domin shi kansa ya san abin da yake zuciyar ɗan adam.
@Bible Society of Nigeria 1979