Far 10
10
Zuriyar 'Ya'yan Nuhu, Maza
(1Tar 1.5-23)
1Waɗannan su ne zuriyar 'ya'yan Nuhu, da Shem, da Ham, da Yafet. Bayan Ruwan Tsufana sai aka haifa musu 'ya'ya. 2'Ya'yan Yafet ke nan, da Gomer, da Magog, da Madai, da Yawan, da Tubal, da Meshek, da Tiras. 3'Ya'yan Gomer kuma Ashkenaz, da Rifat, da Togarma. 4'Ya'yan Yawan kuma Elisha, da Tarshish, da Kittim, da Rodanim. 5Daga waɗannan ne mazauna a bakin gāɓa suka yaɗu bisa ga ƙasashensu, kowanne da harshensa, bisa ga iyalansu da kabilansu.
6'Ya'yan Ham su ne Kush, da Mizrayim, da Fut, da Kan'ana. 7'Ya'yan Kush kuma Seba, da Hawila, da Sabta, da Ra'ama, da Sabteka. 'Ya'yan Ra'ama kuwa Sheba da Dedan. 8Kush ya haifi Lamirudu, shi ne mutumin da ya fara ƙasaita cikin duniya. 9Shi riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji, domin haka akan ce, “Shi kamar Lamirudu ne riƙaƙƙen maharbi ne a gaban Ubangiji.” 10Farkon inda ya kafa mulkinsa a Babila, da Erek, da Akkad, da Kalne ne, dukansu a ƙasar Shinar suke. 11Daga wannan ƙasa ya tafi Assuriya ya gina Nineba da Rehobot-ir, da Kala, 12da Resen wadda take tsakanin Nineba da Kala, wato babban birni.
13Mizrayim shi ne mahaifin Ludawa, da Anamawa, da Lehabawa, da Neftuhawa, 14da Fatrusawa, da Kasluhawa (inda Filistiyawa suka fito) da kuma Kaftorawa.
15Kan'ana ya haifi Sidon ɗan farinsa, da Het, 16shi ne kuma mahaifin Yebusiyawa, da Amoriyawa, da Girgashiyawa, 17da Hiwiyawa, da Arkiyawa, da Siniyawa, 18da Arwadiyawa, da Zemarawa da Hamatiyawa. Bayan haka sai kabilan Kan'aniyawa suka yaɗu. 19Yankin ƙasar Kan'aniyawa kuwa ya milla tun daga Sidon, har zuwa wajen Gerar, har zuwa Gaza, zuwa wajen Saduma, da Gwamrata, da Adma, da Zeboyim, har zuwa Lasha. 20Waɗannan su ne 'ya'yan Ham, bisa ga iyalansu, da harsunansu da ƙasashensu, da kabilansu.
21An kuma haifa wa Shem, wan Yafet, 'ya'ya, shi ne kakan 'ya'yan Eber duka. 22'Ya'yan Shem su ne Elam, da Asshur, da Arfakshad, da Lud, da Aram. 23'Ya'yan Aram kuma Uz, da Hul, da Geter, da Meshek. 24Arfakshad ya haifi Shela, Shela ya haifi Eber. 25An haifa wa Eber 'ya'ya biyu, sunan ɗayan Feleg, gama a zamaninsa aka raba ƙasa, sunan ɗan'uwansa kuwa Yokatan. 26Yokatan ya haifi Almoda, da Shelef, da Hazarmawet, da Yera, 27da Adoniram, da Uzal, da Dikla, 28da Ebal, da Abimayel, da Sheba, 29da Ofir, da Hawila da Yobab, dukan waɗannan 'ya'yan Yokatan ne. 30Yankin ƙasar da suka zauna shi ne ya milla tun daga Mesha, har zuwa wajen Sefar, ƙasar tudu ta gabas. 31Waɗannan su ne 'ya'yan Shem bisa ga iyalansu, da harsunansu, da ƙasashensu, da kabilansu.
32Waɗannan duka su ne zuriyar Nuhu, bisa ga lissafin asalinsu, bisa ga kabilansu. Daga waɗannan ne al'ummai suka yaɗu bisa duniya bayan Ruwan Tsufana.
موجودہ انتخاب:
Far 10: HAU
سرخی
شئیر
کاپی
کیا آپ جاہتے ہیں کہ آپ کی سرکیاں آپ کی devices پر محفوظ ہوں؟ Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979