Chapa ya Youversion
Ikoni ya Utafutaji

Far 4

4
Kayinu da Habila
1Adamu kuwa ya san matarsa Hawwa'u, ta kuwa yi ciki, ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Na sami ɗa namiji da iznin Ubangiji.” 2Ta kuma haifi ɗan'uwansa Habila. Habila makiyayin tumaki ne, Kayinu kuwa manomi ne. 3Wata rana, sai Kayinu ya kawo sadaka ga Ubangiji daga amfanin gona. 4#Ibr 11.4 Habila kuwa ya kawo nasa ƙosassu daga cikin 'ya'yan fari na garkensa. Ubangiji kuwa ya kula da Habila da sadakarsa, 5amma Kayinu da sadakarsa, bai kula da su ba. Saboda haka Kayinu ya husata ƙwarai, har tsikar jikinsa ta tashi.
6Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Me ya sa ka husata, me kuma ya sa har tsikar jikinka ta tashi? 7In da ka yi daidai, ai, da ka yi murmushi. Amma tun da ka yi mugunta, to, zunubi zai yi fakonka don ya rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so ya mallake ka, amma tilas ne ka rinjaye shi.”
8 # Mat 23.35; Luk 11.51; 1Yah 3.12 Kayinu ya ce wa ɗan'uwansa Habila, “Mu tafi cikin saura.” A lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa ɗan'uwansa Habila, har ya kashe shi.
9Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina Habila ɗan'uwanka?”
Ya ce, “Ban sani ba, ni makiyayin ɗan'uwana ne?”
10 # Ibr 12.24 Sai Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Muryar jinin ɗan'uwanka tana yi mini kuka daga ƙasa. 11Yanzu fa, kai la'ananne ne daga cikin ƙasar da ta buɗe baki, ta karɓi jinin ɗan'uwanka daga hannunka. 12In ka yi noma, ƙasar ba za ta ƙara ba ka cikakken amfaninta ba, za ka zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya.”
13Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Hukuncina ya fi ƙarfina. 14Ga shi, yanzu ka kore ni a guje daga fuskar ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, mai kai da kawowa a duniya, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”
15Sai Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Wanda duk ya kashe Kayinu, za a rama masa har sau bakwai.” Ubangiji kuma ya sa wa Kayinu tabo, domin duk wanda ya iske shi kada ya kashe shi.
16Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya zauna a ƙasar Nod, gabashin Aidan.
Zuriyar Kayinu
17Kayinu ya san matarsa, ta kuwa yi ciki ta haifi Anuhu, ya kuwa gina birni ya sa wa birnin sunan ɗansa, Anuhu. 18An haifa wa Anuhu ɗa, wato Airad. Airad ya haifi Mehuyayel, Mehuyayel kuwa ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifi Lamek. 19Lamek ya auri mata biyu, sunan ɗayar Ada, ta biyun kuwa Zulai. 20Ada ta haifi Yabal, shi ne ya zama uban mazaunan alfarwa, makiyayan dabbobi. 21Sunan ɗan'uwansa Yubal, wanda ya zama uban makaɗan garaya da mabusan sarewa. 22Zulai kuwa ta haifi Tubal-kayinu, shi ne asalin maƙeran dukan kayayyakin tagulla da na baƙin ƙarfe. Sunan 'yar'uwar Tubalkayinu Na'ama ne. 23Lamek kuwa ya ce wa matansa, “Ada da Zulai, ku ji muryata, ku matan Lamek ku ji abin da nake cewa na kashe mutum domin ya yi mini rauni, saurayi kuma don ya buge ni. 24Idan an rama wa Kayinu sau bakwai, hakika na Lamek, sai sau saba'in da bakwai.”
Zuriyar Shitu
25Sai kuma Adamu ya san matarsa, ta kuwa haifi ɗa, ta raɗa masa suna Shitu, gama ta ce, “Allah ya arzuta ni da ɗa maimakon Habila wanda Kayinu ya kashe.” 26Ga Shitu kuma aka haifi ɗa, ya kuwa raɗa masa suna Enosh. A wannan lokaci ne mutane suka fara kira bisa sunan Ubangiji.

Iliyochaguliwa sasa

Far 4: HAU

Kuonyesha

Shirikisha

Nakili

None

Je, ungependa vivutio vyako vihifadhiwe kwenye vifaa vyako vyote? Jisajili au ingia