Logoja YouVersion
Ikona e kërkimit

Farawa 4

4
Kayinu da Habila
1Adamu ya kwana da matarsa Hawwa’u, ta kuwa yi ciki ta haifi Kayinu. Sai ta ce, “Da taimakon Ubangiji na sami ɗa namiji.” 2Daga baya ta haifi ɗan’uwansa, ta kuma ba shi suna Habila.
Sa’ad da suka yi girma sai Habila ya zama makiyayin tumaki, Kayinu kuwa ya zama manomi. 3Ana nan sai Kayinu ya kawo waɗansu amfanin gona a matsayin hadaya ga Ubangiji. 4Amma Habila ya kawo mafi kyau daga ’ya’yan fari na garkensa. Ubangiji ya yi farin ciki da sadakar da Habila ya kawo, 5amma bai yi farin ciki da sadakar da Kayinu ya kawo ba. Saboda haka Kayinu ya ji fushi sosai, fuskarsa kuma ta ɓace.
6Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Don me kake fushi? Don me fuskarka ta ɓace? 7Da ka yi abin da yake daidai, ai, da ka sami karɓuwa. Amma tun da ba ka yi abin da ba daidai ba, zunubi zai yi fakonka don yă rinjaye ka kamar naman jeji. Yana so yă mallake ka, amma tilas ka rinjaye shi.”
8To, Kayinu ya ce wa ɗan’uwansa Habila, “Mu tafi gona.”#4.8 Rubuce-rubucen hannu na Fentatut na Samariyawa, Seftuwajin, Bulget da Siriyak; Rubuce-rubucen hannu na Masoretik ba su da “Mu tafi gona.” Yayinda suke a gona, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya buge shi ya kashe.
9Sai Ubangiji ya ce wa Kayinu, “Ina ɗan’uwanka Habila?”
Sai Kayinu ya ce, “Ban sani ba, ni mai gadin ɗan’uwana ne?”
10 Ubangiji ya ce, “Me ke nan ka yi? Saurara! Ga jinin ɗan’uwanka yana mini kuka daga ƙasa. 11Yanzu, kai la’ananne ne, an kuma kore ka daga ƙasa wadda ta buɗe bakinta ta shanye jinin ɗan’uwanka daga hannunka. 12In ka nome ƙasa, ba za tă ƙara ba ka hatsinta ba. Za ka kuma zama mai yawo barkatai a duniya.”
13Kayinu ya ce wa Ubangiji, “Horon nan ya sha ƙarfina. 14Ga shi, yau kana kori na daga ƙasar, zan zama a ɓoye daga fuskarka, zan kuma zama mai yawo barkatai, duk wanda ya same ni kuwa zai kashe ni.”
15Amma Ubangiji ya ce masa, “Ba haka ba ne! Duk wanda ya kashe Kayinu, za a ninƙa hukuncinsa har sau bakwai.” Sa’an nan Ubangiji ya sa wa Kayinu alama don duk wanda ya same shi kada yă kashe shi. 16Saboda haka Kayinu ya yi tafiyarsa ya rabu da Ubangiji, ya je ya zauna ƙasar Nod#4.16 Nod yana nufin yawo (dubi ayoyi 12 da 14). a gabashin Eden.
17Kayinu ya kwana da matarsa, ta kuwa yi ciki, ta haifi Enok. A lokacin Kayinu yana gina birni, sai ya sa wa birnin sunan ɗansa Enok. 18Aka haifa wa Enok Irad, Irad kuma ya haifi Mehujayel, Mehujayel kuma ya haifi Metushayel, Metushayel kuma ya haifin Lamek.
19Lamek ya auri mata biyu, ana ce da ɗaya Ada, ɗayan kuma Zilla. 20Ada ta haifi Yabal, shi ne mahaifi waɗanda suke zama a tentuna, suna kuma kiwon dabbobi. 21Sunan ɗan’uwansa Yubal, shi ne mahaifin dukan makaɗan garaya da masu hura sarewa. 22Zilla ma ta haifi ɗa, Tubal-Kayinu, shi ne wanda ya ƙera kowane iri kayan aiki daga tagulla da kuma ƙarfe. ’Yar’uwar Tubal-Kayinu ita ce Na’ama.
23Wata rana, Lamek ya ce wa matansa, Ada da Zilla,
“Ku saurara, matan Lamek, ku ji maganata.
Na kashe#4.23 Ko kuwa zan kashe wani saboda ya yi mini rauni,
na kashe wani saurayi saboda ya ji mini ciwo.
24Idan za a rama wa Kayinu har sau bakwai,
lalle za a rama wa Lamek sau saba’in da bakwai ke nan.”
25Sai Adamu ya sāke kwana da matarsa, ta haifi ɗa, aka kuma ba shi suna Set, gama ta ce, “Allah ya ba ni wani yaro a madadin Habila, tun da yake Kayinu ya kashe shi.” 26Set ma ya haifi ɗa, ya kuma kira shi Enosh.
A lokaci ne, mutane suka fara kira ga sunan Ubangiji.

Aktualisht i përzgjedhur:

Farawa 4: SRK

Thekso

Ndaje

Copy

None

A doni që theksimet tuaja të jenë të ruajtura në të gjitha pajisjet që keni? Regjistrohu ose hyr