Far 3
3
Faɗuwar Mutum
1 #
W.Yah 12.9; 20.2 Maciji ya fi kowace dabba da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa matar, “Ko Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga wani itacen da yake a gonar ba?’ ”
2Sai matar ta ce wa macijin, “Mā iya ci daga cikin itatuwan gonar, 3amma Allah ya ce, ‘Ba za ku ci daga cikin 'ya'yan itacen da yake tsakiyar gonar ba, ba za ku taɓa shi ba, don kada ku mutu.’ ”
4Amma macijin ya ce wa matar, “Hakika ba za ku mutu ba. 5Gama Allah ya sani a ranar da kuka ci daga itacen nan idanunku za su buɗe, za ku kuwa zama kamar Allah, ku san nagarta da mugunta.”
6Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, 'ya'yansa kuma kyawawa, abin sha'awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga 'ya'yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci. 7Sai dukansu biyu idanunsu suka buɗe, sa'an nan suka gane tsirara suke, sai suka samo ganyayen ɓaure suka ɗinɗinka suka yi wa kansu sutura.
8Da suka ji motsin Allah yana yawo a gonar da sanyin la'asariya, sai mutumin da matarsa suka ɓuya wa Ubangiji Allah cikin itatuwan gonar. 9Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin, ya ce, “Ina kake?”
10Sai ya ce, “Na ji motsinka cikin gonar, na kuwa ji tsoro, domin tsirara nake, na kuwa ɓoye kaina.”
11Ya ce, “Wa ya faɗa maka tsirara kake? Ko ka ci daga cikin itacen da na ce kada ka ci ne?”
12Mutumin ya ce, “Matan nan da ka ba ni, ita ce ta ba ni 'ya'yan itacen, na kuwa ci.”
13 #
2Kor 11.3; 1Tim 2.14 Ubangiji Allah kuma ya ce wa matar, “Mene ne wannan da kika yi?”
Matar ta ce, “Macijin ne ya yaudare ni, na kuwa ci.”
14Ubangiji Allah ya ce wa maciji, “Tun da ka aikata wannan, za a hukunta ka. Kai kaɗai wannan la'ana za ta bi. Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya, turɓaya za ka ci muddin rayuwarka. 15#W.Yah 12.17 Zan sa ƙiyayya tsakaninka da matar, tsakanin zuriyarka da zuriyarta, shi zai ƙuje kanka, kai za ka ƙuje diddigensa.”
16Ga matar kuwa ya ce, “Zan tsananta naƙudarki ainun, da azaba za ki haifi 'ya'ya, duk da haka muradinki zai koma ga mijinki, zai kuwa mallake ki.”
17 #
Ibr 6.8
Ga Adamu kuwa ya ce, “Ka kasa kunne ga muryar matarka, har ka ci daga 'ya'yan itacen da na dokace ka, ‘Kada ka ci daga cikinsu.’ Tun da ka aikata wannan za a la'antar da ƙasa saboda kai, da wahala za ka ci daga cikinta muddin rayuwarka.
18“Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za ta ba ka, za ka kuwa ci ganyayen saurar. 19Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.” (2Tas 3.10; Far 2.7; Zab 90.3; 104.29; M.Had 12.7)
20Mutumin ya sa wa matarsa suna Hawwa'u, domin ita ce uwar 'yan adam. 21Ubangiji Allah kuwa ya yi wa mutumin da matarsa tufafi na fata, ya suturce su.
An Fitar da Adamu da Hawwa'u daga Gonar
22 #
W.Yah 22.14
Sa'an nan Ubangiji Allah ya ce, “Ga shi, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san nagarta da mugunta, yanzu fa, kada ya miƙa hannunsa ya ɗiba daga cikin itacen rai ɗin nan, ya ci, ya rayu har abada.” 23Domin haka Ubangiji Allah ya fisshe shi daga cikin gonar Aidan, ya noma ƙasa, wato inda aka ɗauko shi.
24Ya kori mutum kuma a gabashin gonar Aidan, ya kafa kerubobi, da kuma takobi mai harshen wuta wanda yake jujjuyawa ko'ina don su tsare hanya zuwa itacen rai.
Aktuálne označené:
Far 3: HAU
Zvýraznenie
Zdieľať
Kopírovať
Chceš mať svoje zvýraznenia uložené vo všetkých zariadeniach? Zaregistruj sa alebo sa prihlás
@Bible Society of Nigeria 1979