Luk 10
10
Yesu Ya Aiki Saba'in Ɗin
1Bayan wannan Ubangiji ya zaɓi waɗansu mutum saba'in, ya aike su biyu biyu, su riga shi gaba zuwa kowane gari da kowane wuri da shi kansa za shi. 2#Mat 9.37,38 Ya ce musu, “Girbin na da yawa, amma masu yinsa kaɗan ne. Saboda haka ku roƙi Ubangijin girbi ya turo masu girbi, su yi masa girbi. 3#Mat 10.16 To, sai ku tafi. Ga shi na aike ku kamar 'yan tumaki a tsakiyar kyarketai. 4Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko burgami, ko takalma. Kada ku yi doguwar gaisuwa da kowa a hanya. 5Duk gidan da kuka sauka, ku fara da cewa, ‘Salama alaikun mutanen gidan nan!’ 6In akwai da ɗan salama a gidan, to, salamarku za ta tabbata a gare shi. In kuwa babu, za ta komo muku. 7#1Kor 9.14; 1Tim 5.18 Ku zauna a gidan, kuna ci kuna shan duk irin abin da suka ba ku, domin ma'aikaci ya cancanci ladansa. Kada ku riƙa sāke masauki. 8Duk garin da kuka shiga, in an yi na'am da ku, ku ci duk irin abin da aka kawo muku. 9Ku warkar da marasa lafiya da suke cikinsa, ku kuma ce musu, ‘Mulkin Allah ya kusato ku.’ 10#A.M 13.51Amma duk garin da kuka shiga ba a yi na'am da ku ba, sai ku zaga kwararo kwararo, kuna cewa, 11#Mat 10.7-14; Mar 6.8-11; Luk 9.3-5 ‘Ko da ƙurar garinku da ta ɗafe a jikin ƙafafunmu ma, mun karkaɗe muku. Amma duk da haka ku sani Mulkin Allah ya kusato.’ 12#Far 19.24-28; Mat 11.24; Mat 10.15 Ina dai gaya muku, a ran nan, za a fi haƙurce wa Saduma a kan garin nan.”
Tsawata wa Garuruwan da ba su Tuba Ba
(Mat 11.20-24)
13 #
Ish 23.1-18; Eze 26.1—28.26; Yow 3.4-8; Amos 1.9,10; Zak 9.2-4 “Kaitonki, Korasinu! Kaitonki, Betsaida! Da mu'ujizan da aka yi a cikinku, su aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba, sun zauna sāye da tsumma, suna hurwa da toka. 14Amma a Ranar Shari'a, za a fi haƙurce wa Taya da Sidon a kanku. 15#Ish 14.13-15 Ke kuma Kafarnahum, ɗaukaka ki sama za a yi? A'a, ƙasƙantar da ke za a yi har Hades.
16 #
Mat 10.40; Mar 9.37; Luk 9.48; Yah 13.20 “Duk mai sauraronku, ni yake saurare. Mai ƙinku kuma, ni yake ƙi. Duk mai ƙina kuwa, wanda ya aiko ni ne ya ƙi.”
Komowar Saba'in Ɗin
17Sai kuma saba'in ɗin nan suka komo da farin ciki, suka ce, “Ya Ubangiji, har aljannu ma suna mana biyayya albarkacin sunanka!” 18Sai ya ce musu, “Na ga Shaiɗan ya faɗo daga sama kamar walƙiya. 19#Zab 91.13 Ga shi, na ba ku ikon taka macizai da kunamai, ku kuma rinjaye a kan dukan ikon Maƙiyi, ba kuwa abin da zai cuce ku ko kaɗan. 20Duk da haka, kada ku yi farin ciki aljannu na yi muku biyayya, sai dai ku yi farin cikin an rubuta sunayenku a Sama.”
Yesu Ya Yi Farin Ciki
(Mat 11.25-27; Mar 13.16-17)
21A wannan lokaci ya yi farin ciki matuƙa ta Ruhu Mai Tsarki, ya ce, “Na gode maka ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, domin ka ɓoye waɗannan al'amura ga masu hikima da masu basira, ka kuma bayyana su ga jahilai. Hakika na gode maka ya Uba, domin wannan shi ne nufinka na alheri. 22#Yah 3.35; Yah 10.15 Kowane abu Ubana ne ya mallaka mini. Ba kuwa wanda ya san ko wane ne Ɗan sai dai Uban, ko kuma ya san ko wane ne Uban sai dai Ɗan, da kuma wanda Ɗan yake so ya bayyana wa.”
23Sai ya juya wajen almajiransa, ya ce musu a keɓance, “Albarka tā tabbata ga idanun da suka ga abin da kuka gani. 24Ina gaya muku, annabawa da sarakuna da yawa suna son ganin abin da kuke gani, amma ba su gani ba, suna kuma so su ji abin da kuke ji, amma ba su ji ba.”
Basamariyen da Ya Nuna Jinƙai
25 #
Mat 22.35-40; Mar 12.28-34 Sai ga wani masanin Attaura ya tashi tsaye yana gwada shi, ya ce, “Malam, me zan yi in gaji rai madawwami?” 26Yesu ya ce musu, “Me yake rubuce a Attaura? Yaya kake karantawa?” 27#M.Sh 6.5; L.Fir 19.18 Sai ya amsa ya ce, “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukkan zuciyarka, da dukkan ranka, da dukkan ƙarfinka, da dukkan hankalinka. Ka kuma ƙaunaci ɗan'uwanka kamar kanka.” 28#L.Fir 18.5 Yesu ya ce masa, “Ka amsa daidai. Ka riƙa yin haka, za ka rayu.”
29Shi kuwa mutumin, don yana son baratar da kansa, ya ce wa Yesu, “To, wane ne ɗan'uwa nawa?” 30Sai Yesu ya amsa ya ce, “Wani mutum ne ya tashi daga Urushalima za shi Yariko. Sai 'yan fashi suka fāɗa shi, suka tuɓe shi, suka yi masa mugun dūka, suka tafi suka bar shi rai ga Allah. 31Daga nan ya zamana wani firist ya biyo ta wannan hanya. Da ya gan shi sai ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa. 32Haka kuma wani Balawe, da ya iso wurin ya gan shi, shi ma ya zaga ta ɗaya gefen, ya wuce abinsa. 33#2Tar 28.15 Ana nan sai hanya ta kawo wani Basamariye inda yake. Da ya gan shi, sai tausayi ya kama shi, 34ya je wurinsa, ya ɗaɗɗaure masa raunukansa, yana zuba musu mai da ruwan inabi. Sa'an nan ya ɗora shi a kan dabbarsa, ya kai shi masauki, ya yi ta jiyyarsa. 35Kashegari ya ɗebo dinari biyu ya ba maigidan, ya ce, ‘Ka yi jiyyarsa, duk kuma abin da ka ɓatar bayan wannan, in na dawo sai in biya ka.’ 36To, a cikin ukun nan, wa kake tsammani ya zama ɗan'uwa ga wanda 'yan fashin suka faɗa wa?” 37Sai ya ce, “Wanda ya nuna masa jinƙai.” Sai Yesu ya ce masa, “Kai ma, ka je ka riƙa yin haka.”
Yesu Ya Ziyarci Marta da Maryamu
38 #
Yah 11.1
Suna tafiya, sai ya shiga wani ƙauye, wata mace kuma mai suna Marta ta sauke da shi a gidanta. 39Tana kuwa da 'yar'uwa mai suna Maryamu, wadda ta zauna a gaban Ubangiji tana sauraron magana tasa. 40Marta kuwa yawan hidimomi ya ɗauke mata hankali, sai ta je gunsa, ta ce, “Ya Ubangiji, ba ka kula ba, 'yar'uwata ta bar ni ina hidima ni kaɗai? Gaya mata ta taimake ni mana.” 41Amma Ubangiji ya amsa mata ya ce, “Marta, Marta! Hankalinki a tashe yake, kina kuma damuwa kan abu da yawa. 42Bukatu kima ne, ta ainihi ɗaya ce. Maryamu ta zaɓi abu mai kyau, ba kuwa za a karɓe mata ba.”
Selectat acum:
Luk 10: HAU
Evidențiere
Partajează
Copiază
Dorești să ai evidențierile salvate pe toate dispozitivele? Înscrie-te sau conectează-te
@Bible Society of Nigeria 1979