YouVersion
Pictograma căutare

Yah 21

21
Yesu Ya Bayyana ga Almajirai Bakwai
1Bayan haka Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiran a bakin Tekun Tibariya. Ga kuwa yadda ya bayyana kansa. 2Bitrus, da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai, da Nata'ala na Kana ta ƙasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma waɗansu almajiransa biyu, duk suna nan tare, 3#Luk 5.5 Sai Bitrus ya ce musu, “Za ni su.” Suka ce masa, “Mu ma mā tafi tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgi. Amma a daren nan ba su kama kome ba.
4Gari na wayewa sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran ba su gane Yesu ne ba. 5Sai Yesu ya ce musu, “Samari, kuna da kifi?” Suka amsa masa suka ce, “A'a.” 6#Luk 5.6 Ya ce musu, “Ku jefa taru dama da jirgin za ku samu.” Suka jefa, har suka kāsa jawo shi don yawan kifin. 7Sai almajirin nan da Yesu yake ƙauna ya ce wa Bitrus, “Ubangiji ne dai!” Da Bitrus ya ji, ashe, Ubangiji ne ya yi ɗamara da taguwarsa, don a tuɓe yake, ya fāɗa tekun. 8Sauran almajirai kuwa suka zo a cikin ƙaramin jirgi, janye da tarun cike da kifi, don ba su da nisa daga gaci, kamar misalin kamu ɗari biyu ne.
9Da fitowarsu gaci sai suka ga garwashi a wurin, da kifi kai, da kuma gurasa. 10Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifi a na waɗanda kuka kama yanzu.” 11Sai Bitrus ya hau jirgin, ya jawo tarun gaci, cike da manyan kifaye dari da hamsin da uku. Amma duk da yawansu haka, tarun bai kece ba. 12Sai Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Daga cikin almajiran kuwa ba wanda ya yi ƙarfin halin tambayarsa ko shi wane ne, domin sun sani Ubangiji ne. 13Sai Yesu ya zo ya ɗauki gurasar, ya ba su, haka kuma kifin. 14Wannan ne fa zuwa na uku da Yesu ya bayyana ga almajiran bayan an tashe shi daga matattu.
Yi Kiwon Tumakina
15Da suka karya kumallo Yesu ya ce wa Bitrus, “Bitrus ɗan Yahaya, ka fi waɗannan ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon 'ya'yan tumakina.” 16Ya sāke faɗa masa, faɗa ta biyu, “Bitrus ɗan Yahaya, kana ƙaunata?” Ya ce masa, “I, ya Ubangiji, ka dai sani ina sonka.” Yesu ya ce masa, “Ka kiyaye tumakina.” 17Yesu ya faɗa masa, faɗa ta uku, “Bitrus ɗan Yahaya, kana sona?” Sai Bitrus ya yi baƙin ciki don a faɗar nan ta uku ya ce masa, “Kana sona?” Shi kuwa ya ce masa, “Ya Ubangiji, ai, ka san kome duka, ka kuwa sani ina sonka.”
Yesu ya ce masa, “Ka yi kiwon tumakina. 18Lalle hakika, ina gaya maka, lokacin samartakarka kakan yi wa kanka ɗamara, ka tafi inda ka nufa, amma in ka tsufa, za ka miƙe hannuwanka, wani ya yi maka ɗamara, ya kai ka inda ba ka nufa ba.” 19(Ya faɗi wannan ne yana kwatanta irin mutuwar da Bitrus zai yi ya ɗaukaka Allah.) Bayan ya faɗi haka, ya ce masa, “Bi ni.”
Almajirin da Yesu Yake Ƙauna
20 # Yah 13.25 Sai Bitrus ya waiwaya ya ga almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana biye da su, wato wanda ya jingina gab da Yesu lokacin cin jibin nan da ya ce, “Ya Ubangiji, wane ne zai bāshe ka?” 21Da Bitrus ya gan shi, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, wannan fa?” 22Yesu ya ce masa, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki? Kai dai, bi ni!” 23Saboda haka maganan nan ta bazu cikin 'yan'uwa, cewa almajirin nan ba zai mutu ba. Alhali kuwa Yesu bai ce masa ba zai mutu ba, ya dai ce, “In na nufe shi da wanzuwa har in zo, mene ne naka a ciki?”
24Wannan shi ne almajirin da yake ba da shaida a kan waɗannan al'amura, ya kuma rubuta su, mun kuwa sani shaida tasa tabbatacciya ce.
25Akwai waɗansu al'amura kuma masu yawa da Yesu ya aikata, in da za a rubuta kowannensu ɗaya ɗaya da ɗaya ɗaya, ina tsammani ko duniya kanta ba za ta iya ɗaukar littattafan da za a rubuta ba.

Selectat acum:

Yah 21: HAU

Evidențiere

Partajează

Copiază

None

Dorești să ai evidențierile salvate pe toate dispozitivele? Înscrie-te sau conectează-te