Yah 14
14
Yesu Ne Hanya zuwa Wurin Uban
1“Kada ku damu. Ku gaskata da Allah, ku kuma gaskata da ni. 2A gun Ubana akwai wurin zama da yawa. Da ba haka ne ba, da na faɗa muku, domin zan tafi in shirya muku wuri. 3In kuwa na je na shirya muku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, domin inda nake, ku ma ku zama kuna can. 4Inda za ni kuwa kun san hanya.” 5Sai Toma ya ce masa, “Ya Ubangiji, ba mu san inda za ka ba, ƙaƙa za mu san hanyar?” 6Yesu ya ce masa, “Ni ne hanya, ni ne gaskiya, ni ne kuma rai. Ba mai zuwa wurin Uba sai ta wurina. 7Da kun san ni, da kun san Ubana ma. Amma daga yanzu kun san shi, kun kuma gan shi.”
8Sai Filibus ya ce masa, “Ya Ubangiji, ka nuna mana Uban, bukatarmu ta biya ke nan.” 9Yesu ya ce masa, “Na daɗe tare da ku haka, amma har yanzu ba ka san ni ba, Filibus? Duk wanda ya gan ni, ai, ya ga Uban. Yaya za ka ce, ‘Nuna mana Uban’”? 10Wato ba ka gaskata ba cikin Uba nake, Uba kuma cikina? Maganar da nake faɗa muku, ba domin kaina nake faɗa ba, Uba ne da yake zaune a cikina yake yin ayyukansa. 11Ku gaskata ni, a cikin Uba nake, Uba kuma cikina, ko kuwa ku gaskata ni saboda ayyukan kansu.
12“Lalle hakika, ina gaya muku, duk wanda yake gaskatawa da ni ayyukan da nake yi shi ma haka zai yi. Har ma, zai yi ayyukan da suka fi waɗannan, domin zan tafi wurin Uba. 13Duk abin da kuka roƙa da sunana kuma zan yi, domin a ɗaukaka Uban ta wurin Ɗan. 14Kome kuke roƙa da sunana, zan yi shi.”
Alkawarin Zuwan Ruhu Mai Tsarki
15“In dai kuna ƙaunata, za ku bi umarnina. 16Ni ma zan roƙi Uba, zai kuwa ba ku wani Mai Taimako ya kasance tare da ku har abada. 17Shi ne Ruhu na gaskiya, wanda duniya ba ta iya samunsa, domin ba ta ganinsa, ba ta kuma san shi ba. Ku kam, kun san shi, domin yana zaune tare da ku, zai kuma kasance a zuciyarku.
18“Ba zan bar ku marayu ba, zan zo wurinku. 19Saura ɗan lokaci kaɗan duniya ba za ta ƙara ganina ba, amma ku za ku gan ni. Saboda ni a raye nake, ku ma za ku rayu. 20A ran nan ne fa za ku sani, ni cikin Uba nake, ku kuma a cikina, ni kuma a cikinku. 21Duk wanda ya san umarnaina, yake kuma binsu, shi ne mai ƙaunata. Mai ƙaunata kuwa, Ubana zai ƙaunace shi, ni kuma zan ƙaunace shi, in bayyana kaina gare shi.” 22Sai Yahuza (ba Iskariyoti ba) ya ce masa, “Ya Ubangiji, me ya sa za ka bayyana kanka gare mu, ba ga duniya ba?” 23Yesu ya amsa masa ya ce, “Kowa yake ƙaunata, zai kiyaye maganata, Ubana kuwa zai ƙaunace shi, za mu zo wurinsa mu zauna tare da shi. 24Wanda ba ya ƙaunata, ba ya kiyaye maganata. Maganar da kuke ji kuwa ba tawa ba ce, ta Uba ce wanda ya aiko ni.
25“Duk wannan na faɗa muku ne tun muna tare. 26Amma Mai Taimako, Ruhu Mai Tsarki, wanda Uba zai aiko da sunana, shi ne zai koya muku kome, ya kuma tuna muku duk abin da na faɗa muku. 27Na bar ku da salama. Salamata nake ba ku. Ba kamar yadda duniya take bayarwa nake ba ku ba. Kada ku damu, kada kuma ku ji tsoro. 28Kun dai ji na ce muku zan tafi, in kuma dawo wurinku. Da kuna ƙaunata da kun yi murna saboda za ni wurin Uba, domin kuwa Uban ya fi ni. 29To, yanzu na faɗa muku tun bai faru ba, domin sa'ad da ya faru, ku ba da gaskiya. 30Ba zan ƙara yi muku magana mai yawa ba, domin mai mulkin duniyan nan yana zuwa, ba shi kuwa da wani hannu a kaina, 31sai dai domin duniya tă sani ina ƙaunar Uban, ina kuma yin yadda Uba ya umarce ni, ku tashi mu tafi daga nan.”
Selectat acum:
Yah 14: HAU
Evidențiere
Partajează
Copiază
Dorești să ai evidențierile salvate pe toate dispozitivele? Înscrie-te sau conectează-te
@Bible Society of Nigeria 1979