1
Farawa 26:3
Sabon Rai Don Kowa 2020
Ka zauna a wannan ƙasa na ɗan lokaci, zan kuwa kasance tare da kai, zan kuma albarkace ka. Gama zan ba da waɗannan ƙasashe gare ka da kuma zuriyarka. Zan kuma cika rantsuwar da na yi wa mahaifinka Ibrahim.
비교
Farawa 26:3 살펴보기
2
Farawa 26:4-5
Zan sa zuriyarka ta yi yawa kamar taurari a sararin sama zan kuwa ba su dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin ’ya’yanka kuma za a albarkaci dukan al’umman duniya, domin Ibrahim ya yi mini biyayya ya kuma kiyaye umarnaina, ƙa’idodina da kuma dokokina.”
Farawa 26:4-5 살펴보기
3
Farawa 26:22
Sai Ishaku ya matsa daga can ya sāke haƙa wata rijiyar, babu wani kuma da yi faɗa a kanta. Sai ya ba ta suna Rehobot, yana cewa, “Yanzu UBANGIJI ya ba mu wuri, za mu kuwa yi ta haihuwa a ƙasar.”
Farawa 26:22 살펴보기
4
Farawa 26:2
UBANGIJI kuwa ya bayyana ga Ishaku ya ce, “Kada ka gangara zuwa Masar; ka yi zauna a ƙasar da zan faɗa maka.
Farawa 26:2 살펴보기
5
Farawa 26:25
Sai Ishaku ya gina bagade a can, ya kuma kira bisa sunan UBANGIJI. A can ya kafa tentinsa, a can kuma bayinsa suka haƙa wata rijiya.
Farawa 26:25 살펴보기
홈
성경
묵상
동영상