Yah 7

7
'Yan'uwan Yesu Ba Su Gaskata da Shi Ba
1Bayan haka, Yesu ya riƙa zagawa a Ƙasar Galili, bai yarda ya zaga ta Yahudiya ba, don Yahudawa suna neman kashe shi. 2#L.Fir 23.34; M.Sh 16.13 Idin Bukkoki na Yahudawa kuwa ya gabato. 3Sai 'yan'uwansa suka ce masa, “Tashi daga nan mana ka tafi ƙasar Yahudiya, almajiranka su ma su ga ayyukan da kake yi. 4Ai, ba mai aiki a ɓoye in yana so ya shahara. Tun da yake kana yin waɗannan al'amura, to, sai ka bayyana kanka ga duniya.” 5Domin ko dā ma 'yan'uwansa ba su gaskata da shi ba. 6Sai Yesu ya ce musu, “Lokacina bai yi ba tukuna, amma ku, koyaushe lokacinku ne. 7Ba dama duniya ta ƙi ku, amma ni take ƙi, don na shaide ta a kan ayyukanta mugaye ne. 8Ku dai ku tafi idin. Ni ba za ni ba yanzu, don lokacina bai yi sosai ba tukuna.” 9Da ya faɗa musu haka, ya dakata a ƙasar Galili.
Yesu a Idin Bukkoki
10Bayan 'yan'uwansa sun tafi idin kuwa, shi ma ya tafi, amma a ɓoye, ba a fili ba. 11Yahudawa suna ta nemansa a wurin idin suna cewa, “Ina yake ne?” 12Taro kuma suka riƙa maganarsa a raɗe, waɗansu na cewa, “Mutum ne nagari.” Waɗansu kuma na cewa, “A'a, ai, ɓad da jama'a yake.” 13Amma ba wanda ya yi magana tasa a fili don tsoron Yahudawa.
14Wajen tsakiyar idin sai Yesu ya shiga Haikali ya koyar. 15Yahudawa suka yi mamakin abin, suka ce, “Yaya mutumin nan yake da karatu haka, ga shi kuwa, bai taɓa koyo ba?” 16Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, ta wanda ya aiko ni ce. 17Duk mai son aikata nufin Allah zai san koyarwan nan ko ta Allah ce, ko domin kaina nake faɗa. 18Mai magana don kansa, neman ɗaukakar kansa yake yi. Amma mai neman ɗaukakar wanda ya aiko shi, shi ne mai gaskiya, ba kuwa rashin gaskiya a gare shi. 19Ashe, ba Musa ne ya ba ku Shari'a ba? Duk da haka ba mai kiyaye Shari'ar a cikinku. Don me kuke neman kashe ni?” 20Taron suka amsa suka ce, “Kana da iska! Wa yake neman kashe ka?” 21Yesu ya amsa musu ya ce, “Aiki ɗaya kawai na yi, dukanku kuwa kuna mamakinsa. 22#L.Fir 12.3; Far 17.10 Musa ya bar muku kaciya, (ba ko shi ya fara ba, tun kakannin kakanni ne), ga shi kuma, kukan yi wa mutum kaciya ko a ran Asabar ma. 23#Yah 5.9To, in ana yi wa mutum kaciya ran Asabar don gudun keta Shari'ar Musa, kwa yi fushi don na warkar da mutum sarai ran Asabar? 24Kada ku yi hukunci da zato, amma ku yi hukunci da adalci.”
Wannan Almasihu Ne?
25Sai waɗansu mutanen Urushalima suka ce, “Ashe, ba wannan ne mutumin da suke nema su kashe ba? 26Ga shi nan kuwa, yana magana a fili, ba su ce masa kome ba! Ya yiwu kuma shugabanni sun san lalle wannan shi ne Almasihu? 27Wannan kam, mun san daga inda yake, amma sa'ad da Almasihu ya zo ba wanda zai san daga inda yake.” 28Yesu yana koyarwa a Haikalin ke nan, sai ya ɗaga murya ya ce, “Kun dai san ni, kun kuma san daga inda nake. Ban fa zo domin kaina ba. Wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, shi kuwa ba ku san shi ba. 29Ni na san shi, domin daga wurinsa na fito, shi ne kuwa ya aiko ni.” 30Don haka suka nema su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi, domin lokacinsa bai yi ba tukuna. 31Duk da haka mutane da yawa cikin taron sun gaskata da shi, suna cewa, “Sa'ad da Almasihu ya zo, zai yi mu'ujizai fiye da na mutumin nan?”
An Aiki Dogaran Haikalin Su Kamo Yesu
32Farisiyawa suka ji taro suna raɗeraɗinsa haka, sai manyan firistoci da Farisiyawa suka aiki dogaran Haikali su kamo shi. 33Sai Yesu ya ce, “Saurana ɗan lokaci kaɗan tare da ku, sa'an nan zan koma wurin wanda ya aiko ni. 34Za ku neme ni, amma ba za ku same ni ba. Inda nake kuwa ba za ku iya zuwa ba.” 35Sai Yahudawa suka ce wa juna, “Ina za shi da har ba za mu same shi ba? Za shi wurin Yahudawan da suka warwatsu a cikin al'ummai ne, ya koya wa al'umman? 36Me kuma yake nufi da cewa, ‘Za ku neme ni amma ba za ku same ni ba’? da kuma cewa, ‘Inda nake ba za ku iya zuwa ba’?”
Kogunan Ruwan Rai
37 # L.Fir 23.36 A ranar ƙarshe ta idin, wato babbar ranar, sai Yesu ya tsaya, ya ɗaga murya ya ce, “Duk mai jin ƙishirwa yă zo gare ni yă sha. 38#Eze 47.1; Zak 14.8 Duk mai gaskatawa da ni, kamar yadda Nassi ya ce, ‘Daga zuciyarsa ne kogunan ruwan rai za su gudana.’ ” 39To, wannan shi ne ya faɗa game da Ruhu, wanda masu gaskatawa da shi za su karɓa, domin har yanzu ba a ba da Ruhu ba, saboda ba a ɗaukaka Yesu ba tukuna.
Rabuwa ta Shiga Tsakanin Mutane
40Da jin maganan nan waɗansu daga cikin taron suka ce, “Hakika wannan annabin nan ne.” 41Waɗansu kuwa suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma waɗansu suka ce, “Me? Ashe, Almasihu daga ƙasar Galili zai fito? 42#2Sam 7.12; Mika 5.2 Nassi ba cewa ya yi Almasihu zuriyar Dawuda ne ba, daga kuma Baitalami yake, ƙauyen da Dawuda ya zauna?” 43Sai kuma rabuwa ta shiga tsakaninsu a kansa. 44Waɗansunsu suka so su kama shi, amma ba wanda ya taɓa shi.
Shugabanni Ba Su Gaskata da Yesu Ba
45Daga nan dogaran Haikali suka koma wurin manyan firistoci da Farisiyawa, su kuwa suka ce musu, “Don me ba ku kawo shi ba?” 46Sai dogaran suka amsa suka ce, “A'a, ba mutumin da ya taɓa magana kamar wannan!” 47Sai Farisiyawa suka amsa musu suka ce, “Af! Har ku ma an ɓad da ku ne? 48Ashe, akwai wani daga cikin shugabanni ko Farisiyawa da ya gaskata da shi? 49Amma wannan taro da ba su san Attaura ba, ai, la'anannu ne.” 50#Yah 3.1,2 Nikodimu kuwa da ya je wurinsa dā, yana kuwa ɗaya daga cikinsu, ya ce musu, 51“Ashe, shari'armu takan hukunta mutum tun ba a ji daga bakinsa ba, an kuma san abin da yake ciki?” 52Suka amsa masa suka ce, “Kai ma Bagalile ne? Bincika mana ka gani, ai, ba wani annabi da zai bayyana a ƙasar Galili.”
Matar da aka Kama da Zina
53Sai kowa ya tafi gida.

ಪ್ರಸ್ತುತ ಆಯ್ಕೆ ಮಾಡಲಾಗಿದೆ:

Yah 7: HAU

Highlight

ಶೇರ್

ಕಾಪಿ

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in