Far 1

1
Allah ya Halicci Duniya ya kuma Halicci Mutum
1A sa'ad da Allah ya fara halittar Sama da duniya, 2duniya ba ta da siffa, sarari ce kawai, duhu kuwa yana lulluɓe da fuskar zurfin teku, Ruhun Allah kuma yana shawagi bisa ruwayen. 3#2Kor 4.6 Allah ya ce, “Bari haske ya kasance,” sai kuwa ya kasance. 4Allah ya ga hasken yana da kyau. Allah ya raba tsakanin hasken da duhu, 5ya ce da hasken, “Yini,” duhu kuwa, “Dare.” Ga maraice, ga safiya, kwana ɗaya ke nan.
6 # 2Bit 3.5 Allah ya ce, “Bari sarari ya kasance tsakanin ruwaye, don ya raba tsakaninsu.” 7Allah kuwa ya yi sarari, ya kuma raba tsakanin ruwayen da suke ƙarƙashin sararin da ruwayen da suke birbishin sararin. Haka nan kuwa ya kasance. 8Allah ya ce da sarari, “Sararin sama.” Ga maraice, ga safiya, kwana na biyu ke nan.
9Allah kuwa ya ce, “Bari ruwayen da suke ƙarƙashin sararin su tattaru wuri ɗaya, bari kuma sandararriyar ƙasa ta bayyana.” Haka nan kuwa ya kasance. 10Allah ya ce da sandararriyar ƙasar, “Duniya,” tattaruwan ruwayen da aka tara kuwa, ya ce da su, “Tekuna.” Allah ya ga yana da kyau. 11Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da 'ya'ya, kowanne bisa ga nasa iri, waɗanda suke da 'ya'ya masu ƙwaya a cikinsu, waɗanda irinsa suke cikin duniya.” Haka nan kuwa ya kasance. 12Ƙasa ta fid da tsire-tsire, na masu ba da 'ya'ya waɗanda suke da ƙwayar irinsu a cikinsu, Allah ya ga yana da kyau. 13Ga maraice, ga safiya, kwana na uku ke nan.
14Allah kuwa ya ce, “Bari haskoki su kasance a cikin sararin, su raba tsakanin yini da dare, su kuma zama alamu, da yanayi na shekara, da wokatai. 15Bari kuma su zama haskoki a cikin sarari su haskaka duniya.” Haka nan kuwa ya kasance. 16Allah kuwa ya yi manyan haskokin nan biyu, haske mafi girma ya mallaki yini, ƙaramin kuwa ya mallaki dare, ya kuma yi taurarin. 17Allah ya sa su a cikin sarari su haskaka duniya, 18su yi mulkin yini da kuma dare, su raba tsakanin haske da duhu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 19Ga maraice, ga safiya, kwana na huɗu ke nan.
20Allah kuwa ya ce, “Bari ruwaye su fid da ɗumbun masu rai, bari tsuntsaye kuma su riƙa tashi bisa duniya ƙarƙashin sarari.” 21Allah kuwa ya halicci manya manyan dodani na teku da kowane irin mai rai da yake motsi, waɗanda suke a cikin ruwaye, da kuma kowane irin tsuntsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau. 22Sai Allah ya sa musu albarka, yana cewa, “Ku hayayyafa, ku kuma riɓaɓɓanya, ku cika ruwayen tekuna, tsuntsaye kuma ku hayayyafa cikin duniya.” 23Ga maraice, ga safiya, kwana na biyar ke nan.
24Allah kuwa ya ce, “Bari duniya ta fid da masu rai bisa ga irinsu, shanu, da abubuwa masu rarrafe, da dabbobin duniya bisa ga irinsu.” 25Allah kuwa ya yi dabbobin gida bisa ga irinsu, da kuma na jeji, manya da ƙanana, da kowane irin mai rarrafe bisa ƙasa bisa ga irinsa. Allah kuwa ya ga yana da kyau.
26 # 1Kor 11.7 Allah kuma ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, da kamanninmu, su mallaki kifayen da suke a cikin teku, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da dukan duniya, da kowane abu mai rarrafe da yake rarrafe bisa ƙasa.” 27#Far 5.1,2#Mat 19.4; Mar 10.6 Haka nan fa, Allah ya halicci mutum cikin siffarsa, cikin siffar Allah, Allah ya halicci mutum, namiji da ta mace ya halicce su. 28Allah kuwa ya sa musu albarka, ya ce musu, “Ku hayayyafa ku riɓaɓɓanya, ku cika duniya, ku yi iko da ita, ku mallaki kifayen teku, da tsuntsayen sararin sama, da kuma dukan abin da yake da rai da yake kai da kawowa cikin duniya.” 29Allah kuwa ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da tsaba da yake bisa fuskar dukan duniya, da kowane itacen da yake da ƙwaya cikin 'ya'yansa su zama abincinku. 30Na ba da kowane irin ɗanyen tsiro domin ci, ga kowace irin dabbar da take duniya, da kowane irin tsuntsun da yake sararin sama, da kowane irin abin da yake rarrafe bisa duniya, da dai iyakar abin da yake numfashi.” Haka nan ya kasance. 31Allah kuwa ya ga dukan abin da ya yi, ga shi kuwa yana da kyau ƙwarai. Ga maraice, ga safiya, kwana na shida ke nan.

Currently Selected:

Far 1: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in