Farawa 3

3
Fāɗuwar mutum
1To, maciji dai ya fi kowane a cikin namun jejin da Ubangiji Allah ya yi wayo. Ya ce wa macen, “Tabbatacce ne Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga kowane itace a lambu’?”
2Macen ta ce wa macijin, “Za mu iya ci daga ’ya’ya itatuwa a lambun, 3amma Allah ya ce, ‘Kada ku ci daga ’ya’yan itacen da yake tsakiyar lambu, kada kuma ku taɓa shi, in ba haka ba kuwa za ku mutu.’ ”
4Maciji ya ce wa macen, “Tabbatacce ba za ku mutu ba. 5Gama Allah ya san cewa sa’ad da kuka ci daga itacen idanunku za su buɗe, za ku kuma zama kamar Allah, ku san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu.”
6Sa’ad da macen ta ga ’ya’yan itacen suna da kyau don abinci, abin sha’awa ga ido, abin marmari kuma don samun hikima, sai ta tsinka ta ci, ta kuma ba da waɗansu wa mijinta wanda yake tare da ita, shi ma ya ci. 7Sa’an nan idanun dukansu biyu suka buɗe, suka kuma gane tsirara suke; saboda haka suka ɗinɗinka ganyayen ɓaure suka yi wa kansu sutura.
8Da mutumin da matarsa suka ji motsin Ubangiji Allah yana takawa a lambun a sanyin yini, sai suka ɓuya daga Ubangiji Allah a cikin itatuwan lambu. 9Amma Ubangiji Allah ya kira mutumin ya ce, “Ina kake?”
10Ya ce, “Na ji ka a cikin lambu, na kuwa ji tsoro gama ina tsirara, saboda haka na ɓuya.”
11Sai ya ce, “Wa ya faɗa maka cewa kana tsirara? Ko dai ka ci daga itacen da na umarce ka kada ka ci ne?”
12Mutumin ya ce, “Macen da ka sa a nan tare da ni, ita ta ba ni waɗansu ’ya’ya daga itacen, na kuwa ci.”
13Sai Ubangiji Allah ya ce wa matar, “Me ke nan kika yi?”
Matar ta ce, “Macijin ne ya ruɗe ni, na kuwa ci.”
14Saboda haka Ubangiji Allah ya ce wa macijin, “Saboda ka yi haka,
“Na la’anta ka cikin dukan dabbobi da kuma cikin dukan namun jeji!
Daga yanzu rubda ciki za ka yi tafiya
turɓaya kuma za ka ci
dukan kwanakin rayuwarka.
15Zan kuma sa ƙiyayya
tsakaninka da macen,
tsakanin zuriyarka da zuriyarta.
Zai ragargaje kanka,
kai kuma za ka sari ɗiɗɗigensa.”
16Sa’an nan ya ce wa macen,
“Zan tsananta naƙudarki ainun,
da azaba kuma za ki haifi ’ya’ya.
Za ki riƙa yin marmarin mijinki
zai kuwa yi mulki a kanki.”
17Ga Adamu kuwa ya ce, “Saboda ka saurari matarka, ka kuma ci daga itacen da na ce, ‘Kada ka ci,’
“Za a la’anta ƙasa saboda kai.
Da wahala za ka ci daga cikinta dukan kwanakin rayuwarka.
18Za tă ba ka ƙayayyuwa da sarƙaƙƙiya
za ka kuwa ci ganyayen gona.
19Da zuffan goshinka za ka ci abincinka har ka koma ga ƙasa,
da yake daga cikinta aka yi ka.
Gama kai turɓaya ne,
kuma ga turɓaya za ka koma.”
20Mutumin ya sa wa matarsa suna, Hawwa’u, gama za tă zama mahaifiyar masu rai duka.
21 Ubangiji Allah ya yi tufafin fata domin Adamu da Hawwa’u, ya kuma yi musu sutura. 22Ubangiji Allah ya kuma ce, “To, fa, mutum ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, ya san abin da yake mai kyau da abin da yake mugu. Kada a yarda yă miƙa hannunsa yă ɗiba daga itacen rai yă ci, yă kuma rayu har abada.” 23Saboda haka Ubangiji Allah ya kore shi daga Lambun Eden domin yă nome ƙasa wadda aka yi shi. 24Bayan da ya kori mutumin, sai ya sa kerubobi da takobi mai harshen wuta yana jujjuyawa baya da gaba a gabashin Lambun Eden don yă tsare hanya zuwa itacen rai.

Currently Selected:

Farawa 3: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in