Yah 1

1
Kalman Ya Zama Mutum
1Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. 2Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah. 3Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi. 4Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. 5Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.
6 # Mat 3.1; Mar 1.4; Luk 3.1,2 Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya. 7Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa. 8Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.
9Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum. 10Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. 11Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba. 12Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah, 13wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.
14Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.
15Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ” 16Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri. 17Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance. 18Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.
Shaidar Yahaya Maibaftisma
(Mat 3.1-12; Mar 1.1-8; Luk 3.1-18)
19Wannan kuwa ita ce shaidar Yahaya, wato, sa'ad da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi, ko shi wane ne. 20Sai ya faɗi gaskiya, bai yi musu ba, gaskiya ya faɗa ya ce, “Ba ni ne Almasihu ba.” 21#Mal 4.5; M.Sh 18.15,18 Sai suka tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A'a, ba shi ba ne.” Suka ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A'a.” 22Sai suka ce masa, “To, wane ne kai, domin mu sami amsar da za mu mayar wa waɗanda suka aiko mu? Me kake ce da kanka?” 23#Ish 40.3 Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”
24Su kuwa, Farisiyawa ne suka aiko su. 25Sai suka tambaye shi suka ce, “To, don me kake yin baftisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?” 26Sai Yahaya ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake baftisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba, 27shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in ɓalle ba.” 28An yi wannan a Betanya ne, a hayin Kogin Urdun, inda Yahaya yake yin baftisma.
“Ga Ɗan Rago na Allah”
29Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya! 30Wannan shi ne wanda na ce, ‘Wani yana zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ 31Dā kam, ban san shi ba, sai domin a bayyana shi ga Isra'ila na zo, nake baftisma da ruwa.” 32Yahaya ya yi shaida ya ce, “Na ga Ruhu na saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa. 33Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’ 34Na kuwa gani, na kuma yi shaida, cewa wannan Ɗan Allah ne.”
Almajiran Yesu na Farko
35Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu. 36Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!” 37Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu. 38Yesu ya waiwaya ya ga suna biye da shi, sai ya ce musu, “Me kuke nema?” Suka ce masa, “Ya Rabbi, wato Malam ke nan, ina kake da zama?” 39Sai ya ce musu, “Ku zo ku gani.” Sai suka je suka ga inda yake da zama, suka kuwa yini tare da shi. Wajen ƙarfe huɗu na yamma ne kuwa. 40Ɗaya daga cikin biyun nan da suka ji maganar Yahaya suka kuma bi Yesu, Andarawas ne, ɗan'uwan Bitrus. 41Sai ya fara samo ɗan'uwansa Bitrus, ya ce masa, “Mun sami Almasihu,” wato shafaffe. 42Sai ya kai shi wurin Yesu. Yesu ya dube shi, ya ce, “Wato kai ne Saminu ɗan Yahaya? Za a kira ka Kefas,” wato Bitrus.
Yesu Ya Kira Filibus da Nata'ala
43Kashegari Yesu ya yi niyyar zuwa ƙasar Galili. Sai ya sami Filibus, ya ce masa, “Bi ni.” 44Filibus kuwa mutumin Betsaida ne, garin su Andarawas da Bitrus. 45Filibus ya sami Nata'ala, ya ce masa, “Mun sami wanda Musa ya rubuta labarinsa a Attaura, annabawa kuma suka rubuta labarinsa, wato Yesu Banazare, ɗan Yusufu.” 46Nata'ala ya ce masa, “A iya samun wani abin kirki a Nazarat kuwa?” Sai Filibus ya ce masa, “Taho dai, ka gani.” 47Yesu ya ga Nata'ala na nufo shi, sai ya yi zancensa ya ce, “Kun ga, ga Ba'isra'ile na gaske wanda ba shi da ha'inci!” 48Nata'ala ya ce masa, “A ina ka san ni?” Yesu ya amsa masa ya ce, “Tun kafin Filibus ya kira ka, sa'ad da kake gindin ɓaure, na gan ka.” 49Sai Nata'ala ya amsa masa ya ce, “Ya Shugaba, kai Ɗan Allah ne! Kai Sarkin Isra'ila ne!” 50Yesu ya amsa ya ce, “Wato, domin na ce maka na gan ka a gindin ɓaure ne kake ba da gaskiya? Ai, za ka ga al'amuran da suka fi haka ma.” 51#Far 28.12 Yesu kuma ya ce masa, “Lalle hakika, ina gaya muku, za ku ga sama ta dāre, mala'ikun Allah suna hawa da sauka ga Ɗan Mutum.”

Valið núna:

Yah 1: HAU

Áherslumerki

Deildu

Afrita

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in