Luka 4:9-12

Luka 4:9-12 SRK

Sai Iblis, ya kai shi Urushalima ya sa ya tsaya a kan wuri mafi tsayi na haikali ya ce, “In kai Ɗan Allah ne, ka yi tsalle daga nan zuwa ƙasa. Gama a rubuce yake, “ ‘Zai umarci mala’ikunsa game da kai, su kiyaye ka da kyau; za su tallafe ka da hannuwansu, don kada ka buga ƙafarka a kan dutse.’” Yesu ya amsa ya ce, “An ce, ‘Kada ka gwada Ubangiji Allahnka.’”