Luka 21:25-26

Luka 21:25-26 SRK

“Za a yi alamu a cikin rana, da cikin wata, da cikin taurari. A duniya, al’ummai za su yi baƙin ciki, su kuma rikice don tsoro, saboda ruri da kuma tafasar teku. Mutane za su suma don tsoro, za su kuma yi fargaba, a kan abin da yake zuwa a bisan duniya, gama za a girgiza duniyar taurarin sararin sama.