Luka 14:28-30

Luka 14:28-30 SRK

“In wani daga cikinku yana so ya gina gidan sama, ai, yakan fara zama ne, ya yi lissafin abin da ginin zai ci tukuna, don yă ga ko yana da isashen kuɗi da zai gama ginin. Gama in ya sa tushen gini, amma bai iya gamawa ba, duk wanda ya gani zai yi masa ba’a, yana cewa, ‘Wannan mutum ya fara gini, amma bai iya gamawa ba.’