“Ku yi hankali da malaman dokoki. Sukan so sa manyan riguna suna zaga, suna sha’awan karɓan gaisuwa a wuraren kasuwanci, da kuma wuraren zama mafi daraja a majami’u, da wuraren bangirma a bukukkuwa. Suna mamaye gidajen gwauraye, kuma don burga, suna dogayen addu’o’i. Ga irin waɗannan mutane, za a yi musu hukunci mai tsanani sosai.”