1
Farawa 2:24
Sabon Rai Don Kowa 2020
Wannan ne ya sa mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yă manne wa matarsa, su kuma zama jiki ɗaya.
Bandingkan
Telusuri Farawa 2:24
2
Farawa 2:18
UBANGIJI Allah ya ce, “Bai yi kyau mutumin yă kasance shi kaɗai ba. Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi.”
Telusuri Farawa 2:18
3
Farawa 2:7
Sa’an nan UBANGIJI Allah ya yi mutum daga turɓayar ƙasa, ya kuma hura numfashin rai cikin hancinsa, mutumin kuwa ya zama rayayyen taliki.
Telusuri Farawa 2:7
4
Farawa 2:23
Sai mutumin ya ce, “Yanzu kam wannan ƙashi ne na ƙasusuwana nama kuma na namana. Za a ce da ita ‘mace,’ gama an ciro ta daga namiji.”
Telusuri Farawa 2:23
5
Farawa 2:3
Allah kuwa ya albarkaci kwana ta bakwai, ya kuma mai da ita mai tsarki, saboda a kanta ne ya huta daga dukan aikin halittar da ya yi.
Telusuri Farawa 2:3
6
Farawa 2:25
Mutumin da matarsa, dukansu biyu tsirara suke, ba su kuwa ji kunya ba.
Telusuri Farawa 2:25
Beranda
Alkitab
Rencana
Video