Luk 24

24
Tashin Yesu daga Matattu
(Mat 28.1-10; Mar 16.1-8; Yah 20.1-10)
1A ranar farko ta mako kuwa, da asussuba, suka je wurin kabarin da kayan ƙanshi da suka shirya. 2Sai suka tarar an mirgine dutsen daga kabarin. 3Suka shiga ciki, amma ba su sami jikin Ubangiji ba. 4Tun suna cikin damuwa da abin, sai kawai ga waɗansu mutum biyu a tsaye kusa da su, saye da tufafi masu ƙyalƙyali. 5Don tsoro, matan suka sunkuyar da kansu ƙasa. Mutanen suka ce musu, “Don me kuke neman rayayye a cikin matattu? 6#Mat 16.21; 17.22,23; 20.18,19; Mar 8.31; 9.31; 10.33,34; Luk 9.22; 18.31-33 Ai, ba ya nan, ya tashi. Ku tuna yadda ya gaya muku tun yana Galili 7cewa, ‘Lalle ne a ba da Ɗan Mutum ga mutane masu zunubi, a gicciye shi, a rana ta uku kuma ya tashi’.” 8Sai suka tuna da maganarsa. 9Da suka dawo daga kabarin suka shaida wa goma sha ɗayan nan, da kuma duk sauransu, dukan waɗannan abubuwa. 10To, Maryamu Magadaliya, da Yuwana, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma sauran matan da suke tare da su, su ne suka gaya wa manzannin waɗannan abubuwa. 11Su kuwa sai maganan nan ta zama musu kamar zance ne kawai, suka ƙi gaskatawa. 12Amma Bitrus ya tashi, ya doshi kabarin da gudu. Ya duƙa, ya leƙa a ciki, ya ga likkafanin lilin a ajiye waje ɗaya. Sai ya koma gida yana al'ajabin abin da ya auku.
Almajirai Biyu a Hanyar Imuwasu
(Mar 16.12-13)
13A ran nan kuma sai ga waɗansu biyu suna tafiya wani ƙauye, mai suna Imuwasu, nisansa daga Urushalima kuwa kusan mil bakwai ne. 14Suna ta zance da juna a kan dukan al'amuran da suka faru. 15Ya zamana tun suna magana, suna tunani tare, sai Yesu da kansa ya matso, suka tafi tare. 16Amma idanunsu a rufe, har ba su gane shi ba. 17Yesu ya ce musu, “Wace magana ce kuke yi da juna a tafe?” Sai suka tsaya cik, suna baƙin ciki. 18Sai ɗayansu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa ya ce, “Ashe, kai kaɗai ne baƙo a Urushalima, da ba ka san abubuwan da suka faru a can, 'yan kwanakin nan ba?” 19Sai ya ce musu, “Waɗanne abubuwa?” Suka ce masa, “Game da Yesu Banazare ne, wanda yake annabi mai manyan ayyuka da ƙwaƙƙwarar magana a gaban Allah da dukan mutane, 20da kuma yadda manyan firistoci da shugabanninmu suka ba da shi don a yi masa hukuncin kisa, suka kuwa gicciye shi. 21Dā kuwa muna bege shi ne zai fanshi Isra'ila. Hakika kuma, bayan wannan duka, yau kwana uku ke nan da aukuwar wannan abu. 22Har wa yau kuma, waɗansu mata na cikinmu, sun ba mu al'ajabi. Don sun je kabarin da sassafe, 23da ba su sami jikinsa ba, suka komo, suka ce har ma an yi musu wahayi, sun ga mala'ikun da suka ce yana da rai. 24Waɗansunsu da suke tare da mu kuma, suka je kabarin, suka tarar kamar yadda matan suka faɗa, amma shi, ba su gan shi ba.” 25Sai Yesu ya ce musu, “Ya ku mutane marasa fahimta, masu nauyin gaskata duk abin da annabawa suka faɗa! 26Ashe, ba wajibi ne Almasihu ya sha wuyar waɗannan abubuwa ba, ya kuma shiga ɗaukakarsa?” 27Sai ya fara ta kan littattafan Musa da na dukan annabawa, ya yi ta bayyana musu abubuwan da suka shafe shi a dukan Littattafai.
28Sai suka kusato ƙauyen da za su. Ya yi kamar zai ci gaba, 29suka matsa masa suka ce, “Sauka a wurinmu, ai, magariba ta doso, rana duk ta tafi.” Sai ya sauka a wurinsu. 30Sa'ad da yake cin abinci tare da su, sai ya ɗauki gurasa, ya yi wa Allah godiya, ya gutsura, ya ba su. 31Idonsu ya buɗe, suka kuma gane shi. Sai ya ɓace musu. 32Suka ce wa juna, “Ashe, zuciyarmu ba ta yi annuri ba, sa'ad da yake a hanya, yana bayyana mana Littattafai?”
33Anan take, suka tashi suka koma Urushalima, suka sami sha ɗayan nan tare gu ɗaya, da kuma waɗanda suke tare da su, 34suna cewa, “Hakika Ubangiji ya tashi, har ya bayyana ga Bitrus!” 35Su kuma suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane shi a wajen gutsura gurasa.
Yesu ya Bayyana ga Almajiransa
(Mat 28.16-20; Mar 16.14-18; Yah 20.19-23; A.M 1.6-8)
36Suna cikin faɗar waɗannan abubuwa, sai ga Yesu da kansa tsaye a tsakiyarsu, ya ce musu, “Salama alaikun!” 37Amma suka firgita, tsoro ya kama su, suka zaci fatalwa suke gani. 38Sai ya ce musu, “Don me kuka firgita, kuke kuma tantama a zuciyarku? 39Ku dubi hannuwana da ƙafafuna, ai, ni ne da kaina. Ku taɓa ni, ku ji, don fatalwa ba ta da nama da ƙashi, yadda kuke gani nake da su.” 40Da ya faɗi haka, ya nuna musu hannuwansa da ƙafafunsa. 41Amma tun suna da sauran shakka saboda tsananin farin ciki da mamaki, sai ya ce musu, “Kuna da wani abinci a nan?” 42Sai suka ba shi wata tsokar gasasshen kifi. 43Ya kuwa karɓa, ya ci a gabansu.
44Ya kuma ce musu, “Wannan ita ce maganata da na gaya muku tun muna tare, cewa lalle ne a cika duk abin da yake rubuce game da ni a Attaura ta Musa, da littattafan annabawa, da kuma Zabura.” 45Sa'an nan ya wayar da hankalinsu su fahimci Littattafai, 46ya kuma ce musu, “Haka yake a rubuce, cewa wajibi ne Almasihu ya sha wuya, a rana ta uku kuma ya tashi daga matattu, 47a kuma yi wa dukan al'ummai wa'azi su tuba, a gafarta musu zunubansu saboda sunansa. Za a kuwa fara daga Urushalima. 48Ku ne shaidun waɗannan abubuwa. 49#A.M 1.4 Ga shi, ni zan aiko muku da abin da Ubana ya alkawarta. Amma ku dakata a birni tukuna, har a yi muku baiwar iko daga Sama.”
An Ɗauke Yesu zuwa Sama
(Mar 16.19-20; A.M 1.9-11)
50 # A.M 1.9-11 Sai ya kai su waje har jikin Betanya. Ya ɗaga hannuwansa ya sa musu albarka. 51Yana sa musu albarka ke nan, sai ya rabu da su, aka ɗauke shi zuwa sama. 52Su kuwa suka yi masa sujada, suka koma Urushalima, suna matuƙar farin ciki. 53Ko yaushe kuma suna a Haikali suna yabon Allah.

Chwazi Kounye ya:

Luk 24: HAU

Pati Souliye

Pataje

Kopye

None

Ou vle gen souliye ou yo sere sou tout aparèy ou yo? Enskri oswa konekte