Logo YouVersion
Îcone de recherche

Mat 28:12-15

Mat 28:12-15 HAU

Su kuwa da suka taru da shugabannin jama'a suka yi shawara, sai suka ba sojan kuɗi masu tsoka, suka ce, “Ku faɗa wa mutane almajiransa ne suka zo da daddare suka sace shi kuna barci. In kuwa labarin nan ya kai ga kunnen mai mulki, mā rarrashe shi, mu tsare ku daga wahala.” Sai suka karɓi kuɗin, suka yi yadda aka koya musu. Wannan magana kuwa, ta bazu cikin Yahudawa har ya zuwa yau.