YouVersion Logo
Search Icon

Luk 14

14
Warkar da Mai Ciwon Fara
1Wata ranar Asabar, ya shiga gidan wani shugaba Farisiyawa garin cin abinci, mutane kuwa suna haƙwansa. 2Sai ga wani mai ciwon fara a gabansa. 3Yesu ya amsa ya ce wa masanan Attaura da Farisiyawa, “Ya halatta a warkar ran Asabar ko kuwa?” 4Sai suka yi shiru, Yesu kuwa ya riƙe shi, ya warkar da shi, ya kuma sallame shi. 5#Mat 12.11 Sa'an nan ya ce musu, “Misali, wane ne a cikinku in yana da jaki ko takarkari ya faɗa a rijiya ran Asabar, ba zai fitar da shi nan da nan ba?” 6Sai suka kasa ba da amsar waɗannan abubuwa.
Aya ga Waɗanda aka Gayyato Biki da Mai Gayyar
7To, ganin yadda waɗanda aka gayyato sun zaɓi mazaunan alfarma, sai ya ba su misali ya ce, 8#K.Mag 25.6,7“In an gayyace ka zuwa biki, kada ka zauna a mazaunin alfarma, kada ya zamana an gayyato wani wanda ya fi ka daraja, 9wanda ya gayyato ku duka biyu kuma yă zo ya ce maka, ‘Ba mutumin nan wuri.’ Sa'an nan a kunyace ka koma mazauni mafi ƙasƙanci. 10Amma in an gayyace ka biki, sai ka je ka zauna a wuri mafi ƙasƙanci, don in mai gayyar ya zo, sai ya ce maka, ‘Aboki, hawo nan mana.’ Za ka sami girma ke nan a gaban dukan waɗanda kuke zaune tare. 11#Mat 23.12; Luk 18.14 Duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Mai ƙasƙantar da kansa kuma, ɗaukaka shi za a yi.”
12Ya kuma ce da mai gayyar, “In za ka kira mutum cin abinci ko biki, kada ka riƙa kiran abokanka kawai, ko 'yan'uwanka, ko danginka ko maƙwabtanka masu arziki, kada su ma su gayyace ka, su sāka maka. 13Amma in za ka kira biki, sai ka gayyayo gajiyayyu, da musakai, da guragu, da makafi, 14za ka kuwa sami albarka, da yake ba su da hanyar sāka maka. Sai kuwa a sāka maka ranar tashin masu adalci.”
Misali na Babban Biki
15Da jin haka, sai ɗaya daga cikin abokan cinsa ya ce masa, “Albarka tā tabbata ga wanda zai ci abinci a Mulkin Allah.” 16Amma ya ce masa, “Wani mutum ne ya shirya babban biki ya gayyaci mutane da yawa. 17Da lokacin biki ya yi, sai ya aiki bawansa yă ce wa waɗanda aka gayyata, ‘Ku zo, duk an shirya kome,’ 18Sai dukansu baki ɗaya suka fara kawo hanzari. Na farko ya ce masa, ‘Na sayi gona, lalle ne in je in gano ta. Ina roƙonka ka ɗauke mini,’ 19Sai wani ya ce, ‘Na sayi shanun noma guda goma, za ni in gwada su. Ina roƙonka ka ɗauke mini.’ 20Wani kuma ya ce, ‘Na yi aure, don haka ba zan iya zuwa ba.’ 21Bawan ya dawo ya ba ubangijinsa labari. Sai maigidan ya yi fushi, ya ce wa bawansa, ‘Fita maza, ka bi titi-titin birni da kwararo-kwararo, ka ɗebo gajiyayyu, da musakai, da makafi, da guragu.’ 22Sai bawan ya ce, ‘Ya ubangiji, abin da ka umarta duk an gama, amma har yanzu da sauran wuri.’ 23Sai ubangijin biki ya ce wa bawan, ‘Fita, ka bi gwadabe-gwadabe da hanyoyin karkara, ka rinjayi mutane su shigo, don a cika gidana. 24Ina gaya muku, ba ko ɗaya daga cikin mutanen da na gayyata a dā da zai ɗanɗana bikina ba.’ ”
Wuyar Zama Almajiri
25To, taro masu yawan gaske binsa. Sai ya juya ya ce musu, 26#Mat 10.37 “Duk mai zuwa wurina, in bai fi ƙaunata da ubansa, da uwa tasa, da mata tasa, da 'ya'yansa, da 'yan'uwansa mata da maza, har ma ransa ba, ba zai iya zama almajirina ba. 27#Mat 10.38; 16.24; Mar 8.34; Luk 9.23 Duk wanda bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, ba zai iya zama almajirina ba. 28Misali, in wani daga cikinku yana son gina soron bene, da fari ba sai ya zauna ya yi lissafin abin da zai kashe ba, ya ga ko yana da isassun kuɗi da za su ƙare aikin? 29Kada ya zamana bayan da ya sa harsashin ginin, yă kasa gamawa, har duk waɗanda suka gani, su fara yi masa ba'a, 30su riƙa cewa, ‘A! Ka ga mutumin nan ya fara gini, amma ya kasa gamawa!’
31“Ko kuwa wane sarki ne, in za shi yaƙi da wani sarki, da fari ba ya zauna ya yi shawara, ya ga ko shi mai mutum dubu goma zai iya karawa da mai dubu ashirin ba? 32In kuwa ba zai iya ba, to, tun wancan yana nesa, sai ya aiki jakadu, su tambayo sharuɗan amana. 33Haka ma, kowannenku in bai saki duk abin da ya mallaka ba, ba zai iya zama almajirina ba.”
Sānannen Gishiri
(Mat 5.13; Mar 9.50)
34“Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sāne, da me za a daɗaɗa shi? 35Ba shi da wani amfani a gona, ko a taki, sai dai a zubar kawai. Duk mai kunnen ji, ya ji.”

Currently Selected:

Luk 14: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in

YouVersion uses cookies to personalize your experience. By using our website, you accept our use of cookies as described in our Privacy Policy