Zab 25
25
Addu'a domin Biyarwa, da Gafartawa, da Kiyayewa
1A gare ka nake yin addu'a, ya Ubangiji,
2A gare ka nake dogara, ya Allah.
Ka cece ni daga shan kunyar fāɗuwa,
Kada ka bar magabtana su yi mini duban wulakanci!
3Waɗanda suke dogara gare ka,
Ba za su kasa yin nasara ba,
Sai dai waɗanda suke gaggawa su yi maka tayarwa.
4Ka koya mini al'amuranka, ya Ubangiji,
Ka sa su zama sanannu a gare ni.
5Ka koya mini in yi zamana bisa ga gaskiyarka,
Gama kai Mai Cetona ne.
Dukan yini ina dogara a gare ka.
6Ya Ubangiji, ka tuna da alherinka da madawwamiyar ƙaunarka,
Waɗanda ka nuna tun a dā.
7Ka gafarta zunubaina da kurakuraina masu yawa na ƙuruciyata.
Saboda madawwamiyar ƙaunarka da alherinka,
Ka tuna da ni, ya Ubangiji!
8Ubangiji mai adalci ne, mai alheri,
Yana koya wa masu zunubi tafarkin da za su bi.
9Yana bi da masu tawali'u a tafarkin da suke daidai,
Yana koya musu nufinsa.
10Da ƙauna da aminci yana bi da dukan waɗanda suke biyayya da alkawarinsa da umarnansa.
11Ka cika alkawarinka, ya Ubangiji, ka gafarta zunubaina, gama suna da yawa.
12Waɗanda suke biyayya da Ubangiji
Za su koyi hanyar da za su bi daga gare shi.
13Kullayaumi za su arzuta,
'Ya'yansu kuma za su zauna lafiya a ƙasar.
14Ubangiji yakan amince da waɗanda suke biyayya da shi,
Yakan koya musu alkawarinsa.
15A koyaushe ga Ubangiji nake neman taimako,
Yakan kuɓutar da ni daga hatsari.
16Ka juyo wajena, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai,
Gama ina zaman kaɗaici da rashin ƙarfi.
17Damuwar zuciyata ta yi yawa,
Ka raba ni da dukan damuwa,
Ka cece ni daga dukan wahalata.
18Ka kula da wahalata da azabata,
Ka gafarta dukan zunubaina.
19Ka duba yawan magabtan da nake da su,
Dubi irin ƙiyayyar da suke yi mini!
20Ka yi mini kāriya, ka cece ni,
Gama na zo wurinka neman kāriya.
21Ka sa nagartata da amincina su kiyaye ni,
Gama na dogara gare ka.
22Ka fanshi jama'arka daga dukan wahalarsu, ya Allah!
Currently Selected:
Zab 25: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979