YouVersion Logo
Search Icon

Mar 9

9
1Sai ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, akwai waɗansu tsaitsaye a nan da ba za su mutu ba, sai sun ga Mulkin Allah ya bayyana da iko.”
Sākewar Kamanninsa
(Mat 17.1-13; Luk 9.28-36)
2 # 2Bit 1.17,18 Bayan kwana shida Yesu ya ɗauki Bitrus, da Yakubu, da Yahaya, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. Sai kamanninsa ya sāke a gabansu, 3tufafinsa suka yi fari fat suna sheƙi, yadda ba mai wankin da zai iya yinsu haka a duniya. 4Sai Iliya da Musa sun bayyana a gare su, suna magana da Yesu. 5Sai Bitrus ya sa baki, ya ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, ya kyautu da muke nan wurin, mu kafa bukkoki uku, ɗaya taka, ɗaya ta Musa, ɗaya kuma ta Iliya.” 6Ya rasa abin da zai faɗa ne, don sun tsorata da gaske. 7#Mat 3.17; Mar 1.11; Luk 3.22 Sai ga wani gajimare ya zo ya rufe su, aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena. Ku saurare shi.” 8Farat haka da suka dudduba, ba su ƙara ganin kowa ba, sai Yesu kaɗai tare da su.
9Suna cikin gangarowa daga dutsen, sai ya kwaɓe su kada su gaya wa kowa abin da suka gani, sai bayan Ɗan Mutum ya tashi daga matattu. 10Sai suka bar maganar yasu-yasu, suna tambayar juna komece ce ma'anar tashi daga matattu. 11#Mal 4.5; Mat 11.14Suka tambaye shi suka ce, “To, yaya kuwa malaman Attaura suke cewa, lalle ne Iliya yă fara zuwa?” 12Sai ya ce musu, “Lalle ne Iliya ya fara zuwa ya raya dukan abubuwa. Yaya kuwa yake a rubuce a kan Ɗan Mutum, cewa zai sha wuya iri iri, a kuma wulaƙanta shi? 13Amma ina gaya muku, Iliya ya riga ya zo, sun kuma yi masa abin da suka ga dama, yadda labarinsa yake a rubuce.”
Yesu Ya Warkar da Yaro Mai Beben Aljan
(Mat 17.14-21; Luk 9.37-43)
14To, da suka komo wurin almajiran, sai suka ga babban taro ya kewaye su, malaman Attaura kuma na muhawara da su. 15Da ganin Yesu sai duk taron suka yi mamaki ƙwarai da gaske, suka ɗungumo wurinsa a guje, suna gaishe shi. 16Ya tambaye su, “Muhawarar me kuke yi da su?” 17Sai ɗaya daga cikin taron ya amsa masa ya ce, “Malam, ga shi, na kawo maka ɗana, don yana da beben aljan. 18Duk inda ya hau shi, sai ya doka shi har ƙasa, bakinsa na kumfa, yana tsukun haƙoransa, yana sandarewa. Na kuma yi wa almajiranka magana su fitar da shi, suka kasa.” 19Sai Yesu ya amsa musu ya ce, “Ya ku mutanen zamani marar bangaskiya! Har yaushe zan iya zama da ku? Har yaushe kuma zan iya jure muku? Ku dai kawo mini shi.” 20Suka kawo masa yaron. Da aljanin ya gan shi, nan da nan sai ya buge yaron, jikinsa na rawa, ya fāɗi yana ta birgima, bakinsa na kumfa. 21Yesu ya tambayi uban yaron, “Tun yaushe wannan abu ya same shi?” Uban ya ce, “Tun yana ƙarami. 22Ya kuwa sha jefa shi a wuta da ruwa, don ya hallaka shi. Amma in za ka iya yin wani abu, ka ji tausayinmu ka taimake mu.” 23Sai Yesu ya ce masa, “In zan iya? Ai, dukkan abu mai yiwuwa ne ga mai ba da gaskiya.” 24Nan da nan sai uban yaron ya ɗaga murya ya ce, “Na ba da gaskiya. A kore mini rashin bangaskiyata!” 25Da Yesu ya ga taro na ɗungumowa a guje, sai ya tsawata wa baƙin aljanin ya ce masa, “Kai, beben aljan, na umarce ka ka rabu da shi, kada kuma ka ƙara hawansa.” 26Bayan aljanin nan ya yi ihu, sai ya buge shi da gaske, jikinsa na rawa, ya rabu da shi. Yaron kuma ya zama kamar matacce, har ma yawancin mutane suka ce, “Ai, ya mutu!” 27Amma Yesu ya kama hannunsa ya tashe shi, ya kuwa tashi tsaye. 28Da Yesu ya shiga gida, almajiransa suka tambaye shi a keɓe suka ce, “Me ya sa mu muka kasa fitar da shi?” 29Sai ya ce musu, “Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a.”
Yesu Ya Sāke Faɗar irin Mutuwar da Zai Yi
(Mat 17.22-23; Luk 9.43-45)
30Sai suka tashi daga nan, suka ratsa ƙasar Galili, bai kuwa so kowa ya sani ba, 31domin yana koya wa almajiransa ne, yana ce musu, “Za a ba da Ɗan Mutum ga mutane, za su kuwa kashe shi, sa'ad da aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.” 32Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambaya tasa.
Wane ne Mafi Girma?
(Mat 18.1-5; Luk 9.46-48)
33Suka zo Kafarnahum. Da ya shiga gida sai ya tambaye su, “Muhawarar me kuka yi a hanya?” 34#Luk 22.24 Amma suka yi shiru, don a hanya sun yi muhawarar ko wane ne babbansu. 35#Mat 20.26,27; 23.11; Mar 10.43,44; Luk 22.26 Sai ya zauna, ya kira sha biyun nan, ya ce musu, “Kowa yake son yă zama shugaba, lalle ne yă zama na ƙarshe duka, baran kowa kuma.” 36Sai ya ɗauki wani ƙaramin yaro, ya sa shi a tsakiyarsu, ya rungume shi, ya ce musu, 37#Mat 10.40; Luk 10.16; Yah 13.20 “Duk wanda ya karɓi ƙaramin yaro kamar wannan saboda sunana, ni ya karɓa. Wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”
Wanda ba ya Gāba da Mu, Namu Ne
(Luk 9.49-50)
38Sai Yahaya ya ce masa, “Malam, mun ga wani na fitar da aljannu da sunanka, mun kuwa hana shi, domin ba ya binmu.” 39Amma Yesu ya ce, “Kada ku hana shi. Ai, ba wanda zai yi wata mu'ujiza da sunana, sa'an nan, nan da nan ya kushe mini. 40#Mat 12.30; Luk 11.23 Ai, duk wanda ba ya gāba da mu, namu ne. 41#Mat 10.42 Kowa kuma ya ba ku ruwan sha moɗa guda saboda ku na Almasihu ne, hakika ina gaya muku, ba zai rasa ladansa ba ko kaɗan.
Sanadodin Yin Zunubi
(Mat 18.7-9; Luk 17.1-2)
42“Da dai wani yă sa ɗaya daga cikin waɗannan 'yan yara masu gaskatawa da ni yă yi laifi, zai fiye masa a rataya wani babban dutsen niƙa a wuyansa, a jefa shi cikin teku. 43#Mat 5.30 In kuwa hannunka na sa ka laifi, to, yanke shi. Zai fiye maka ka shiga rai dungu, da ka shiga Gidan Wuta da hannu biyu, wuta marar kasuwa kuwa. 44[A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.] 45In kuwa ƙafarka na sa ka laifi, to, yanke ta. Zai fiye maka ka shiga rai da gurguntaka, da a jefa ka Gidan Wuta da ƙafa biyu. 46[A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta.] 47#Mat 5.29 In kuma idonka na sa ka laifi, to, ƙwaƙule shi. Zai fiye maka ka shiga Mulkin Allah da ido ɗaya, da a jefa ka Gidan Wuta da ido biyu. 48#Ish 66.24 A wurin tsutsotsi masu cinsu ba sa mutuwa, wutar kuma ba a kashe ta. 49Da wuta za a tsarkake kowa, kamar yadda ake tsarkake abu da gishiri. 50#Mat 5.13; Luk 14.34,35 Gishiri abu ne mai kyau, amma in gishiri ya sane, dame za a daɗaɗa shi? Sai ku kasance da gishiri a zuciyarku, ku yi zaman lafiya da juna.”

Currently Selected:

Mar 9: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in