YouVersion Logo
Search Icon

Mar 16

16
Tashin Yesu daga Matattu
(Mat 28.1-10; Luk 24.1-12; Yah 20.1-10)
1Da Asabar ta wuce, Maryamu Magadaliya, da Maryamu uwar Yakubu, da kuma Salome, suka sayo kayan ƙanshi, domin su je su shafa masa. 2A ranar farko ta mako, da assussuba suka tafi kabarin, da fitowar rana sai suka isa. 3Suna ce wa juna, “Wa zai mirgine mana dutsen nan daga bakin kabarin?” 4Da suka ɗaga kai, suka ga, ashe, an mirgine dutsen waje ɗaya, ga shi kuwa, ƙato ne ƙwarai. 5Suna shiga kabarin, sai suka ga wani saurayi a zaune daga dama, saye da farar riga. Sai suka firgita. 6Shi kuwa ya ce musu, “Kada ku firgita. Yesu Banazare kuke nema, wanda aka gicciye. Ai, ya tashi, ba ya nan. Kun ga ma wurin da suka sa shi! 7#Mat 26.32; Mar 14.28 Amma ku tafi ku gaya wa almajiransa, duk da Bitrus, cewa zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi, kamar yadda ya faɗa muku.” 8Sai suka fita, suka ruga a guje daga kabarin, suna rawar jiki a ruɗe. Ba su kuma ce wa kowa kome ba, domin suna tsoro.
Yesu Ya Bayyana ga Maryamu Magadaliya
(Yah 20.11-18)
9[Da ya tashi da rai da wuri ranar farko ta mako, ya fara bayyana ga Maryamu Magadaliya, wadda ya fitar wa da aljannu bakwai. 10Ita kuwa ta tafi ta faɗa wa waɗanda dā suke tare da shi, ta tarar suna baƙin ciki, suna kuka. 11Amma da suka ji yana da rai, har ma ta gan shi, sai suka ƙi gaskatawa.
Yesu Ya Bayyana ga Almajirai Biyu
(Luk 24.13-35)
12Bayan haka ya bayyana da wata kama ga waɗansu biyu daga cikinsu, sa'ad da suke tafiya ƙauye. 13Suka koma suka gaya wa sauran, su ma kuwa ba su gaskata su ba.
Umarnin Yesu ga Goma Sha Ɗayan
(Mat 28.16-20; Luk 24.36-49; Yah 20.19-23; A.M 1.6-8)
14Daga baya ya bayyana ga sha ɗayan nan, su kansu, sa'ad da suke cin abinci. Sai ya tsawata musu a kan rashin bangaskiyarsu da taurinkansu, domin ba su gaskata waɗanda suka gan shi bayan ya tashi ba. 15#A.M 1.8 Sai ya ce musu, “Ku tafi ko'ina a duniya, ku yi wa dukkan 'yan adam bishara. 16Duk wanda ya ba da gaskiya, aka kuma yi masa baftisma, zai sami ceto. Amma wanda ya ƙi ba da gaskiya za a hukunta shi. 17Za a ga waɗannan mu'ujizai wurin masu ba da gaskiya, wato da sunana za su fitar da aljannu, za su yi magana da waɗansu baƙin harsuna, 18za su iya ɗaukar maciji, kowace irin guba kuma suka sha, ba za ta cuce su ba ko kaɗan, za su kuma ɗora wa marasa lafiya hannu, su warke.”
An Ɗauke Yesu zuwa Sama
(Luk 24.50-53; A.M 1.9-11)
19 # A.M 1.9-11 To, bayan da Ubangiji Yesu ya yi musu jawabi, aka ɗauke shi aka kai shi Sama, ya zauna dama ga Allah. 20Su kuwa suka tafi, suka yi ta wa'azi ko'ina, Ubangiji yana taimakonsu, yana kuma tabbatar da maganarsu ta mu'ujizan nan da suke biye da maganar.]

Currently Selected:

Mar 16: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in