YouVersion Logo
Search Icon

Mat 26

26
Shugabanni Sun Ƙulla Shawara Gaba da Yesu
(Mar 14.1-2; Luk 22.1-2; Yah 11.45-53)
1Da Yesu ya gama duk wannan magana, sai ya ce wa almajiransa, 2#Fit 12.1-27 “Kun san Idin Ƙetarewa saura kwana biyu, za a kuma ba da Ɗan Mutum a gicciye shi.”
3Sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka taru a gidan babban firist, mai suna Kayafa. 4Suka ƙulla shawara su kama Yesu da makirci su kashe shi. 5Amma suka ce, “Ba dai a lokacin idi ba, don kada jama'a su yi hargitsi.”
An Shafi Yesu da Man Ƙanshi a Betanya
(Mar 14.3-9; Yah 12.1-8)
6To, sa'ad da Yesu yake Betanya a gidan Saminu kuturu, 7#Luk 7.37,38sai wata mace ta zo wurinsa da wani ɗan tandu na man ƙanshi mai tsadar gaske, ta tsiyaye masa a kā, a lokacin da yake cin abinci. 8Amma da almajiran suka ga haka, sai suka ji haushi suka ce, “Wannan almubazzaranci fa! 9Da ma an sayar da man nan kuɗi mai yawa, an ba gajiyayyu!” 10Yesu kuwa da ya lura da haka, sai ya ce musu, “Don me kuke damun matar nan? Ai, alheri ta yi mini, na gaske kuwa. 11#M.Sh 15.11 Kullum kuna tare da talakawa, amma ba kullum ne kuke tare da ni ba. 12Zuba man nan da ta yi a jikina, ta yi shi ne domin tanadin jana'izata. 13Hakika, ina gaya muku, duk inda za a yi bisharar nan a duniya duka, abin da matar nan ta yi za a riƙa faɗarsa don tunawa da ita.”
Yahuza Ya Yarda Ya Ba Da Yesu
(Mar 14.10-11; Luk 22.3-6)
14Sai ɗaya daga cikin sha biyun nan, mai suna Yahuza Iskariyoti, ya je wurin manyan firistoci, 15#Zak 11.12 ya ce, “Me za ku ba ni, in na bashe shi a gare ku?” Sai suka ƙirga kuɗi azurfa talatin, suka ba shi. 16Tun daga lokacin nan ne ya riƙa neman hanyar da zai bashe shi.
Yesu Ya Ci Idin Ƙetarewa tare da Almajiransa
(Mar 14.12-21; Luk 22.7-14,21-23; Yah 13.21-30)
17To, a ranar farko ta idin abinci marar yisti sai almajiran suka zo wurin Yesu suka ce, “Ina kake so mu shirya maka cin Idin Ƙetarewa?” 18Sai ya ce, “Ku shiga gari wurin wāne, ku ce masa, ‘Malam ya ce lokacinsa ya yi kusa, zai ci Idin Ƙetarewa a gidanka tare da almajiransa.’ ” 19Almajiran kuwa suka yi yadda Yesu ya umarce su, suka shirya Idin Ƙetarewa.
20Da magariba ta yi, sai ya zauna cin abinci tare da almajiran nan goma sha biyu. 21Suna cikin cin abinci, sai ya ce, “Hakika, ina gaya muku, ɗayanku zai bashe ni.” 22Sai suka yi baƙin ciki gaya, suka fara ce masa da ɗaya ɗaya, “Ni ne, ya Ubangiji?” 23#Zab 41.9 Sai ya amsa ya ce, “Wanda muke ci a ƙwarya ɗaya, shi ne zai bashe ni. 24Ɗan Mutum zai tafi ne, yadda labarinsa yake a rubuce, duk da haka kaiton mutumin nan da yake ba da Ɗan Mutum! Da ma ba a haifi mutumin nan ba, da zai fiye masa.” 25Sai Yahuza da ya bashe shi ya ce, “Ko ni ne, ya Shugaba?” Yesu ya ce masa, “Ga shi, kai ma ka faɗa.”
Cin Jibin Ubangiji
(Mar 14.22-26; Luk 22.15-20; 1Kor 11.23-26)
26Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba almajiran, ya ce, “Ungo, ku ci. Wannan jikina ne.” 27Sai ya ɗauki ƙoƙo bayan ya kuma yi godiya ga Allah, sai ya ba su, ya ce, “Dukkanku ku shassha. 28#Fit 24.8; Irm 31.31-34 Wannan jinina ne na tabbatar alkawari, wanda za a zubar saboda mutane da yawa, domin gafarar zunubansu. 29Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranar nan da za mu sha wani sabo tare da ku a Mulkin Ubana.”
30Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.
Bitrus Zai Yi Musun Sanin Yesu
(Mar 14.27-31; Luk 22.31-34; Yah 13.36-38)
31 # Zak 13.7 Sai Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe sabili da ni a wannan dare domin a rubuce yake cewa, ‘Zan bugi makiyayi, tumakin garken kuwa za su fasu.’ 32#Mat 28.16 Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.” 33Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe sabili da kai, ni kam ba zan yi tuntuɓe ba faufau.” 34Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.” 35Bitrus ya ce masa, “Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Haka ma duk almajiran suka ce.
Yesu ya Yi Addu'a a Gatsemani
(Mar 14.32-42; Luk 22.39-46)
36Sa'an nan Yesu ya zo da su wani wuri da ake kira Gatsemani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, Ni kuwa zan je can in yi addu'a.” 37Sai ya ɗauki Bitrus da 'ya'yan nan na Zabadi biyu, ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai. 38Sai ya ce musu, “Raina yana shan wahala matuƙa, har ma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a faɗake tare da ni.” 39Da ya ci gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubana, in mai yiwuwa ne, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalar nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.” 40Ya komo wurin almajiran, ya ga suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Ashe, ba za ku iya zama a faɗake tare da ni ko da na sa'a ɗaya ba? 41Ku zauna a faɗake, ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.” 42Har wa yau a komawa ta biyu, sai ya je ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubana, in wannan ba zai wuce ba sai na sha shi, to, a aikata nufinka.” 43Har yanzu dai ya dawo ya ga suna barci, don duk barci ya cika musu ido. 44Har wa yau ya sāke barinsu, ya koma ya yi addu'a ta uku, yana maimaita maganar dā. 45Sai ya komo wurin almajiran, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi, kuna hutawa? To, ga shi, lokaci ya yi kusa. An ba da Ɗan Mutum ga masu zunubi. 46Ku tashi mu tafi. Kun ga, ga mai bashe ni nan, ya matso!”
An Ba da Yesu, an Kama Shi
(Mar 14.43-50; Luk 22.47-53; Yah 18.3-12)
47Kafin ya rufe baki ga Yahuza, ɗaya daga cikin sha biyun nan, da babban taron mutane riƙe da takuba da kulake, manyan firistoci da shugabanni ne suka turo su. 48To, mai bashe shi ɗin ya riga ya ƙulla da su cewa, “Wanda zan yi wa sumba, shi ne mutumin. Ku kama shi.” 49Nan da nan ya matso wurin Yesu, ya ce, “Salama alaikun, ya Shugaba!” Sai ya yi ta sumbantarsa. 50Yesu ya ce masa, “Abokina, abin da ya kawo ka ke nan?” Suka matso suka ɗanke Yesu, suka kama shi. 51Sai ga ɗaya daga cikin waɗanda suke tare da Yesu ya miƙa hannu ya zaro takobinsa, ya kai wa bawan babban firist sara, ya ɗauke masa kunne. 52Sai Yesu ya ce masa, “Mai da takobinka kube. Duk wanda ya zare takobi, takobi ne ajalinsa. 53Kuna tsammani ba ni da ikon neman taimako gun Ubana ba, nan da nan kuwa ya aiko mini fiye da rundunar mala'iku goma sha biyu? 54To, ta yaya ke nan za a cika Littattafai a kan lalle wannan abu ya kasance?” 55#Luk 19.47; 21.37 Nan take Yesu ya ce wa taron jama'a, “Kun fito ne da takuba da kulake ku kama ni kamar ɗan fashi? Kowace rana nakan zauna a Haikali ina koyarwa, amma ba ku kama ni ba. 56Amma duk wannan ya auku ne domin a cika littattafan annabawa.” Daga nan duk almajiran suka yashe shi, suka yi ta kansu.
Yesu a Gaban 'Yan Majalisa
(Mar 14.53-65; Luk 22.54-55,63-71; Yah 18.13-14,19-24)
57Sai waɗanda suka kama Yesu suka tafi da shi wurin Kayafa, babban firist, inda malaman Attaura da shugabanni suke tare. 58Amma Bitrus ya bi shi daga nesa, har cikin gidan babban firist. Da ya shiga, sai ya zauna tare da dogaran Haikali, don ya ga ƙarshen abin. 59To, sai manyan firistoci da 'yan majalisa duka suka nemi shaidar zur da za a yi wa Yesu don su sami dama su kashe shi. 60Amma ba su samu ba, ko da yake masu shaidar zur da yawa sun zazzaburo. Daga baya sai waɗansu biyu suka matso, 61#Yah 2.19 suka ce, “Wannan ya ce, wai zai iya rushe Haikalin nan na Allah, ya kuma gina shi a cikin kwana uku.” 62Sai babban firist ya miƙe ya ce, “Ba ka da wata amsa? Shaidar da mutanen nan suke yi a kanka fa?” 63Amma Yesu na shiru. Sai babban firist ya ce masa, “Na gama ka da Allah Rayayye, ka faɗa mana ko kai ne Almasihu, Ɗan Allah.” 64#Dan 7.13 Sai Yesu ya ce masa, “Yadda ka faɗa. Ina kuwa gaya muku a nan gaba za ku ga Ɗan Mutum zaune a dama da Mai Iko, yana kuma zuwa a kan gajimare.” 65#L.Fir 24.16 Sai babban firist ya kyakketa tufafinsa, ya ce, “Ya yi saɓo! Wace shaida kuma za mu nema? Yanzu kun ji saɓon da ya yi! 66Me kuka gani?” Suka amsa suka ce, “Ya cancanci kisa!” 67#Ish 50.6 Sai suka tattofa masa yau a fuska, suka bubbuge shi, waɗansu kuma suka mammare shi, 68suna cewa, “Yi mana annabci, kai Almasihu! Faɗi wanda ya buge ka!”
Bitrus Ya Yi Musun Sanin Yesu
(Mar 14.66-72; Luk 22.56-62; Yah 18.15-18,25-27)
69To, Bitrus kuwa yana zaune a tsakar gida a waje, sai wata baranya ta zo ta tsaya a kansa, ta ce, “Kai ma, ai, tare kake da Yesu Bagalile!” 70Amma ya musa a gabansu duka ya ce, “Ni ban san abin da kike nufi ba.” 71Da ya fito zaure, sai wata baranya kuma ta gan shi, ta ce wa waɗanda suke tsaitsaye a wurin, “Ai, mutumin nan tare yake da Yesu Banazare!” 72Sai ya sāke musawa har da rantsuwa ya ce, “Ban ma san mutumin nan ba.” 73Jim kaɗan sai na tsaitsayen suka matso, suka ce wa Bitrus, “Lalle kai ma ɗayansu ne, don irin maganarka ta tona ka.” 74Sai ya fara la'anar kansa, yana ta rantse-rantse, yana cewa, “Ban ma san mutumin nan ba.” Nan da nan sai zakara ya yi cara. 75Sai Bitrus ya tuna da maganar Yesu cewa, “Kafin carar zakara za ka yi musun sanina sau uku.” Sai ya fita waje, ya yi ta rusa kuka.

Currently Selected:

Mat 26: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in