YouVersion Logo
Search Icon

Mat 21

21
Mutanen Urushalima Sun Marabci Yesu
(Mar 11.1-11; Luk 19.28-40; Yah 12.12-19)
1Da suka kusato Urushalima suka zo Betafaji, wajen Dutsen Zaitun, sai Yesu ya aiki almajiransa biyu, 2ya ce musu, “Ku shiga ƙauyen can da yake gabanku. Da shigarku za ku ga wata jaka a ɗaure, da kuma ɗanta. Ku kwanto su. 3Kowa ya yi muku magana, ku ce, ‘Ubangiji ne yake bukatarsu,’ zai kuwa aiko da su nan da nan.” 4An yi wannan kuwa domin a cika faɗar Annabi Zakariya cewa,
5 # Zak 9.9 “Ku ce wa 'yar Sihiyona,
Ga Sarkinki yana zuwa gare ki,
Mai tawali'u ne,
Yana kan aholaki, wato, ɗan jaki.”
6Sai almajiran suka tafi suka bi umarnin Yesu. 7Suka kawo jakar da ɗanta, suka shimfiɗa masu mayafansu, ya hau. 8Yawancin jama'a suka shisshimfiɗa mayafansu a hanya, waɗansu kuma suka kakkaryo ganye suna bazawa a hanya. 9#Zab 118.25,26 Taron jama'a da suke tafiya a gabansa da kuma a bayansa, sai suka ɗauki sowa suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji! Hosanna ga Allah!” 10Da ya shiga Urushalima dukkan birnin ya ruɗe, ana ta cewa, “Wane ne wannan?” 11Sai jama'a suka ce, “Ai, wannan shi ne Annabi Yesu daga Nazarat ta ƙasar Galili.”
Yesu Ya Tsabtace Haikalin
(Mar 11.15-19; Luk 19.45-48; Yah 2.13-22)
12Sai Yesu ya shiga Haikalin ya kakkori dukkan masu saye da sayarwa a ciki, ya birkice teburorin 'yan canjin kuɗi da kujerun masu sayar da tattabarai. 13#Ish 56.7; Irm 7.11 Ya ce musu, “A rubuce yake cewa, ‘Za a kira gidana ɗakin addu'a,’ amma ku kun maishe shi kogon 'yan fashi.”
14Sai makafi da guragu suka zo wurinsa a Haikalin, ya kuwa warkar da su. 15Amma manyan firistoci da malaman Attaura suka ga abubuwan al'ajabi da ya yi, har yara suna sowa a Haikalin suna cewa, “Hosanna ga Ɗan Dawuda!” sai suka ji haushi. 16#Zab 8.2 Suka ce masa, “Kana jin abin da waɗannan suke faɗa?” Yesu kuwa ya ce musu, “I. Amma ba ku taɓa karantawa ba cewa,
“ ‘Kai ne ka shiryar da 'yan yara da masu shan mama su yabe ka’?”
17Sai ya bar su, ya fita daga birnin, ya tafi Betanya, ya sauka a can.
La'antar da Itacen Ɓaure
(Mar 11.12-14,20-24)
18Kashegari da sassafe yana komowa birni, sai ya ji yunwa. 19Da ya ga wani ɓaure a gefen hanya, ya je wurin, amma bai sami kome ba, sai ganye kawai. Sai ya ce wa ɓauren, “Kada ka ƙara yin 'ya'ya har abada!” Nan take ɓauren ya bushe. 20Da almajiran suka ga haka, suka yi mamaki suka ce, “Yaya ɓauren nan ya bushe haka nan da nan?” 21#Mat 17.20; 1Kor 13.2 Yesu ya amsa musu ya ce, “Hakika, ina gaya muku, in dai kuna da bangaskiya, ba tare da wata shakka ba, ba abin da aka yi wa ɓauren nan kaɗai za ku yi ba, har ma in kun ce wa dutsen nan, ‘Ka ciru, ka faɗa teku,’ sai kuwa ya auku. 22Kome kuka roƙa da addu'a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.”
Ana Shakkar Izinin Yesu
(Mar 11.27-33; Luk 20.1-8)
23Ya shiga Haikali yana cikin koyarwa, sai manyan firistoci da shugabannin jama'a suka zo wurinsa, suka ce, “Da wane izini kake yin abubuwan nan, wa ya ba ka izinin?” 24Sai Yesu ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. In kun ba ni amsa, ni ma sai in gaya muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan. 25To, baftismar da Yahaya ya yi, daga ina take? Daga Sama take, ko kuwa ta mutum ce?” Sai suka yi ta muhawwara da juna, suna cewa, “In muka ce, ‘Daga Sama take,’ sai ya ce mana, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 26In kuwa muka ce, ‘Ta mutum ce,’ ai, muna jin tsoron jama'a, don duk kowa ya ɗauki Yahaya a kan annabi ne.” 27Sai suka amsa wa Yesu suka ce, “Ba mu sani ba.” Shi kuma ya ce musu, “Haka ni kuma ba zan faɗa muku ko da wane izini nake yin abubuwan nan ba.”
Misali na Mai 'Ya'ya Biyu Maza
28“To, me kuka gani? An yi wani mutun mai 'ya'ya biyu maza. Ya je wurin na farkon, ya ce, ‘Ɗana, yau je ka ka yi aiki a garkar inabi.’ 29Sai ya ce, ‘Na ƙi.’ Amma daga baya sai ya tuba, ya tafi. 30Sai ya je gun na biyun ya faɗa masa haka. Shi kuwa ya amsa ya ce, ‘To, za ni, baba,’ amma bai je ba. 31To, wane ne a cikin su biyun ya yi abin da ubansu yake so?” Sai suka ce, “Na farkon.” Yesu ya ce musu, “Hakika, ina gaya muku, masu karɓar haraji da karuwai suna riga ku shiga Mulkin Allah. 32#Luk 3.12; 7.29,30 Ga shi, Yahaya ya zo ya bayyana muku hanyar adalci, ba ku gaskata shi ba. Amma masu karɓar haraji da karuwai sun gaskata shi, duk da ganin haka kuma, daga baya ba ku tuba kun gaskata shi ba.”
Misali na Manoman da Suka Yi Sufurin Garkar Inabi
(Mar 12.1-12; Luk 20.9-19)
33 # Ish 5.1,2 “To, ga kuma wani misali. An yi wani maigida da ya yi garkar inabi, ya shinge ta, ya haƙa ramin matse inabi a ciki, ya kuma gina wata 'yar hasumiyar tsaro. Ya ba waɗansu manoma sufurin garkar, sa'an nan ya tafi wata ƙasa. 34Da kakar inabi ta kusa, sai ya aiki bayinsa wurin manoman nan su karɓo masa gallar garkar. 35Manoman kuwa suka kama bayinsa, suka yi wa ɗaya dūka, suka kashe ɗaya, suka kuma jajjefi ɗaya. 36Har wa yau ya sāke aiken waɗansu bayi fiye da na dā, suka kuma yi musu haka. 37Daga baya sai ya aiki ɗansa gare su, yana cewa, ‘Sā ga girman ɗana.’ 38Amma da manoman suka ga ɗan, suka ce wa juna, ‘Ai, wannan shi ne magajin, ku zo mu kashe shi, gādonsa ya zama namu.’ 39Sai suka kama shi, suka jefa shi bayan shinge, suka kashe shi. 40To, sa'ad da ubangijin garkar nan ya zo, me zai yi wa manoman nan?” 41Sai suka ce masa, “Zai yi wa mutanen banzan nan mugun kisa, ya ba waɗansu manoma sufurinta, waɗanda za su riƙa ba shi gallar garkar a lokacin nunanta.”
42 # Zab 118.22,23 Yesu ya ce musu, “Ashe, ba ku taɓa karantawa a Littattafai ba? cewa,
“ ‘Dutsen da magina suka ƙi,
Shi ne ya zama mafificin dutsen gini.
Wannan aikin Ubangiji ne,
A gare mu kuwa abin al'ajabi ne.’
43“Domin haka ina gaya muku, za a karɓe Mulkin Allah daga gare ku, a bai wa wata al'umma wadda za ta ba da amfani nagari. 44Kowa ya faɗo a kan dutsen nan, sai ya ragargaje. Amma wanda dutsen nan ya faɗa wa, niƙe shi zai yi kamar gari.”
45Da manyan firistoci da Farisiyawa suka ji misalan nan da ya yi, sai suka gane, ashe, da su yake. 46Amma da suka nemi kama shi, suka ji tsoron jama'a, don su sun ɗauke shi shi annabi ne.

Currently Selected:

Mat 21: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in