YouVersion Logo
Search Icon

Yun 2

2
Addu'ar Yunusa ta Godiya
1Sai Yunusa ya yi addu'a ga Ubangiji Allah a cikin cikin kifin, 2ya ce,
“A cikin wahalata na yi kira gare ka,
ya Ubangiji,
Ka a kuwa amsa mini.
Daga can cikin lahira na yi kira,
Ka kuwa ji muryata.
3Ka jefa ni cikin zurfi,
Can cikin tsakiyar teku,
Inda igiyoyin ruwa suka kewaye ni,
Kumfa da raƙuman ruwanka suka
bi ta kaina.
4Na ce, an kore ni daga wurinka,
Duk da haka zan sāke ganin
Haikalinka mai tsarki.
5Ruwa ya sha kaina,
Tekun ta rufe ni ɗungum.
Tsire-tsiren teku suka naɗe kaina.
6Na tafi can ƙasa ƙarƙashin tussan
duwatsu.
Ƙasar da ƙofarta take rufe har abada,
Amma ka fitar da ni daga cikin
ramin, ya Ubangiji Allahna.
7Sa'ad da na ji raina yana rabuwa da
ni,
Sai na tuna da kai, ya Ubangiji.
Addu'ata kuwa ta kai gare ka a
Haikalinka tsattsarka.
8Su waɗanda suke yin sujada ga gumaka
marasa amfani
Sun daina yi maka biyayya.
9Amma ni zan raira yabbai gare ka,
Zan miƙa maka sadaka,
Zan cika wa'adin da na yi.
Ceto daga wurin Ubangiji yake.”
10Ubangiji kuwa ya umarci kifin, kifin kuwa ya amayar da Yunusa a gaɓar teku.

Currently Selected:

Yun 2: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in