YouVersion Logo
Search Icon

Fit 6

6
1Ubangiji kuwa ya ce wa Musa, “Yanzun nan, za ka ga abin da zan yi da Fir'auna. Gama zan tilasta shi ya bar su su fita, har ma ya iza ƙyeyarsu don su bar ƙasarsa!”
An Sāke Kiran Musa
2 # Far 17.1; 28.3; 35.11; Fit 3.13-15 Allah kuma ya yi magana da Musa, ya ce, “Ni ne Ubangiji. 3Na bayyana ga Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu a kan ni Allah Maɗaukaki ne, amma sunan nan nawa, Yahweh, ban sanasshe su ba. 4Na kuma yi musu alkawari zan ba su ƙasar Kan'ana, inda suka yi zaman baƙunci. 5Yanzu na ji nishin Isra'ilawa, waɗanda Masarawa suka bautar, na kuwa tuna da alkawarina. 6Sai ka faɗa wa Isra'ilawa cewa, ‘Ni Ubangiji zan 'yantar da ku daga wulakancin nan da Masarawa suke yi muku. Zan kuɓutar da ku daga bautar Masarawa. Da ƙarfi zan aikata hukuntaina masu iko don in cece ku. 7Zan tallafe ku, ku zama jama'ata, ni kuwa in zama Allahnku. A sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji Allahnku wanda ya 'yanto ku daga wulakancin Masarawa. 8Sa'an nan zan kawo ku cikin ƙasar da na rantse zan bai wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu. Zan ba ku ita ta zama mallakarku. Ni ne Ubangiji.’ ” 9Sai Musa ya faɗa wa Isra'ilawa wannan magana, amma ba su kasa kunne gare shi ba, saboda ɓacin rai da tsananin bauta.
10Ubangiji kuma ya ce wa Musa, 11“Tafi gaban Fir'auna, Sarkin Masar, ka faɗa masa ya bar Isra'ilawa su fita ƙasa tasa.”
12Amma Musa ya amsa wa Ubangiji ya ce, “Duba, tun da yake Isra'ilawa ba su kasa kunne gare ni ba, yaya Fir'auna zai kasa kunne gare ni, ni mutum mai nauyin baki?” 13Ubangiji kuma ya yi magana da Musa da Haruna, su tafi wurin Isra'ilawa da wurin Fir'auna, Sarkin Masar, su ba su umarni, su kuma fito da Isra'ilawa daga cikin ƙasar Masar.
Asalin Musa da Haruna
14Waɗannan su ne shugabannin gidajen kakanninsu. 'Ya'yan Ra'ubainu, maza, ɗan farin Isra'ila, su ne Hanok, da Fallu, da Hesruna, da Karmi. Waɗannan su ne iyalan kabilar Ra'ubainu. 15'Ya'yan Saminu, maza, su ne Yemuwel, da Yamin, da Ohad, da Yakin, da Zohar, da Shawul ɗan Bakan'aniya, waɗannan su ne iyalan kabilar Saminu. 16#L.Ƙid 3.17-20; 26.57,58; 1Tar 6.16-19 Waɗannan su ne sunayen 'ya'yan Lawi bisa ga iyalansu, Gershon, da Kohat, da Merari. Lawi ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai. 17'Ya'yan Gershon, maza kuwa, su ne Libni, da Shimai bisa ga iyalansu. 18'Ya'ya maza na Kohat kuwa, su ne Amram, da Izhara, da Hebron, da Uzziyel. Kohat ya rayu shekara ɗari da talatin da uku. 19'Ya'ya maza na Merari, su ne Mali, da Mushi. Waɗannan su ne kabilar Lawi bisa ga zuriyarsu.
20Amram ya auri Yokabed 'yar'uwar mahaifinsa, ta kuwa haifa masa Haruna da Musa. Amram ya rayu shekara ɗari da talatin da bakwai. 21'Ya'yan Izhara, su ne Kora, da Nefeg, da Zikri. 22'Ya'ya maza na Uzziyel, su ne Mishayel, da Elzafan, da Zitri. 23Haruna ya auri Elisheba, 'yar Amminadab 'yar'uwar Nashon. Sai ta haifa masa Nadab, da Abihu, da Ele'azara, da Itamar. 24'Ya'ya maza na Kora, su ne Assir, da Elkana, da Abiyasaf. Waɗannan su ne iyalin Kora. 25Ele'azara, ɗan Haruna, ya auri ɗaya daga cikin 'ya'ya mata na Futiyel. Ita kuwa ta haifa masa Finehas. Waɗannan su ne shugabannin iyalan kabilar Lawi bisa ga kabilansu.
26Wannan Haruna ne da Musa, waɗanda Ubangiji ya yi musu magana su fito da Isra'ilawa daga cikin ƙasar Masar, ƙungiya ƙungiya. 27Su ne waɗanda suka yi magana da Sarkin Masar ya bar Isra'ilawa su fita daga Masar. Musa da Haruna ne suka yi wannan.
Umarnin Ubangiji ga Musa da Haruna
28Wata rana Ubangiji ya yi magana da Musa a ƙasar Masar ya ce, 29“Ni ne Ubangiji, sai ka faɗa wa Fir'auna, Sarkin Masar, dukan abin da na faɗa maka.”
30Amma Musa ya ce wa Ubangiji, “Ni mai nauyin baki ne, yaya Fir'auna zai kasa kunne gare ni?”

Currently Selected:

Fit 6: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in