YouVersion Logo
Search Icon

Afi 5

5
Ku Yi Zaman Haske
1Saboda haka sai ku zama masu koyi da Allah, in ku ƙaunatattun 'ya'yansa ne. 2#Fit 29.18; Zab 40.6Ku yi zaman ƙauna kamar yadda Almasihu ya ƙaunace mu, ya kuma ba da kansa dominmu, sadaka mai ƙanshi, hadaya kuma ga Allah.
3Kada ma a ko ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin kuwa bai dace da tsarkaka ba. 4Haka ma alfasha, da zancen banza da wauta, don bai kamata ba, sai dai a maimakon haka ku riƙa gode wa Allah. 5Kun dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayi (wanda shi da mai bautar gumaka duk ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Almasihu da na Allah. 6Kada wani ya hilace ku da maganar wofi, gama sabili da waɗannan zunubai ne fushin Allah yake aukawa a kan kangararru. 7Saboda haka, kada ku yi cuɗanya da su, 8domin dā ku duhu ne, amma a yanzu ku haske ne a cikin Ubangiji. Ku yi zaman mutanen haske, 9domin haske shi ne yake haifar duk abin da yake nagari, na adalci, da na gaskiya. 10Ku dai tabbata abin zai gamshi Ubangiji. 11Ku yi nesa da ayyukan duhu na banza da wofi, sai dai ku tona su. 12Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da suke yi a asirce. 13Duk abin da aka kawo a gaban haske a san ainihinsa, gama duk abin da aka san ainihinsa ya haskaka. 14Saboda haka aka ce,
“Farka, ya kai mai barci, ka tashi daga matattu.
Almasihu kuwa zai haskaka ka.”
15Saboda haka, sai ku mai da hankali ƙwarai ga zamanku, kada ku zama kamar marasa hikima, sai dai masu hikima. 16#Kol 4.5 Ku yi matuƙar amfani da lokaci don kwanaki mugaye ne. 17Don haka kada ku zama marasa azanci, sai dai ku fahimci abin da yake nufin Ubangiji. 18Kada kuma ku bugu da giya, hanyar masha'a ke nan. Sai dai ku cika da Ruhu, 19#Kol 3.16,17 kuna zance da junanku da kalmomin zabura, da waƙoƙin yabo, da waƙoƙi na ruhu, kuna raira waƙoƙi da zabura ga Ubangiji da yabo a zukatanku. 20Kullum ku riƙa gode wa Allah Uba da sunan Ubangijinmu Yesu Almasihu a kan ko mene ne.
Maza da Mata
21Ku bi juna saboda ganin girman Almasihu. 22#Kol 3.18; 1Bit 3.1 Ku matan aure, ku yi biyayya ga mazanku, Ubangiji ke nan kuke yi wa. 23Don miji shi ne shugaban matarsa, kamar yadda Almasihu yake shugaban Ikkilisiya, wato, jikinsa, shi kansa kuma shi ne Mai Ceton jikin. 24Kamar yadda Ikkilisiya take bin Almasihu, haka kuma mata su bi mazansu ta kowane hali. 25#Kol 3.19; 1Bit 3.7 Ku maza, ku ƙaunaci matanku kamar yadda Almasihu ya ƙaunaci ikkilisiya, har ya ba da kansa dominta, 26domin ya miƙa ta ga Allah, tsarkakakkiya bayan da ya wanke ta da ruwa ta wurin Kalma, 27domin shi kansa yă ba kansa Ikkilisiya da ɗaukakarta, ba tare da tabo ko tamoji ba, ko wani irin abu haka, tă dai zamo tsattsarka marar aibu. 28Ta haka ya wajaba maza su ƙaunaci matansu, jikinsu ke nan suke yi wa. Ai, wanda ya ƙaunaci matarsa, ya ƙaunaci kansa ke nan. 29Domin ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai ya rene shi, ya yi tattalinsa, kamar yadda Almasihu yake yi wa Ikkilisiya, 30domin mu gaɓoɓin jikinsa ne. 31#Far 2.24 “Saboda haka ne, mutum sai ya bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, ya manne wa matarsa, su biyu su zama jiki guda.” 32Wannan asiri muhimmi ne, ni kuwa ina nufin Almasihu ne da ikkilisiya. 33Duk da haka dai, sai kowane ɗayanku ya ƙaunaci matarsa kamar kansa, ita matar kuwa ta yi wa mijinta ladabi.

Currently Selected:

Afi 5: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in