YouVersion Logo
Search Icon

Amos 5

5
Kira Zuwa Tuba
1Ku kasa kunne, ku jama'ar
Isra'ila, ga waƙar makoki da zan yi
a kanku.
2Isra'ila ta fāɗi,
Ba kuwa za ta ƙara tashi ba.
Tana fa kwance a ƙasa,
Ba wanda zai tashe ta.
3Ubangiji ya ce,
“Wani birnin Isra'ila ya aika da soja
dubu,
Ɗari ne kaɗai suka komo,
Wani birni kuma ya aika da soja ɗari
ne,
Amma goma kaɗai suka komo.”
4Ubangiji ya ce wa jama'ar Isra'ila,
“Ku zo gare ni, za ku tsira.
5Kada ku tafi ku yi sujada a Biyer-sheba.
Kada ku yi ƙoƙarin nemana a
Betel,
Gama Betel lalacewa za ta yi.
Kada ku tafi Gilgal,
Gama an ƙaddara wa jama'arta su
yi ƙaura.”
6Ku tafi wurin Ubangiji ku tsira.
Idan kuwa kun ƙi,
Shi zai babbaka jama'ar Yusufu
Kamar yadda a kan babbaka da
wuta.
Wuta za ta ƙone jama'ar Betel,
Ba kuwa mai kashe wutar.
7Abin tausayi ne ku da kuke ɓata
shari'a,
Kuna hana wa mutane hakkinsu.
8 # Ayu 9.9; 38.31 Ubangiji ne ya yi taurarin
Kaza da 'ya'yanta
Da mai farauta da kare.
Ya mai da duhu haske,
Rana kuwa dare.
Shi ya kirawo ruwan teku ya
bayyana,
Ya shimfiɗa shi a bisa ƙasa.
Sunansa Ubangiji ne.
9Ya kawo halaka a kan ƙarfafa,
Da a kan birane masu garu.
10Kun ƙi wanda ya tsaya a kan
adalci,
Da mai faɗar ainihin gaskiya a gaban
shari'a.
11Kun matsa wa talakawa lamba,
Kun ƙwace musu abincinsu.
Saboda haka kyawawan gidajen nan
da kun gina da dutse,
Ba za ku zauna a cikinsu ba,
Ba kuwa za ku sha ruwan inabin
nan
Daga kyawawan gonakin inabinku
ba.
12Na san irin zunuban da kuke yi,
Da mugayen laifofin da kuka aikata.
Kuna wulakanta mutanen kirki,
Kuna cin hanci,
Kuna hana a yi wa talakawa shari'ar
adalci a majalisa.
13Ashe, ba abin mamaki ba ne,
Da masu hankali suka kame bakinsu
A waɗannan kwanaki na mugunta.
14Ku yi ƙoƙari, ku yi nagarta, ba
mugunta ba,
Domin ku tsira.
Sa'an nan ne Ubangiji Allah
Maɗaukaki
Zai kasance tare da ku sosai,
Kamar yadda kuka ɗauka!
15Ku ƙi mugunta, ku ƙaunaci
nagarta,
Ku yi adalci cikin majalisar
alƙalanku!
Watakila Ubangiji Allah Mai
Runduna
Zai yi wa sauran da suka ragu na
wannan al'umma alheri.
16Haka Ubangiji Allah Mai Runduna
ya ce,
“Za a yi kuka, a yi kururuwa a
titunan birninku saboda azaba.
Daga ƙauyuka za a kirawo
mutane
Su zo su yi makokin.
Waɗanda suka mutu, tare da masu
makoki da aka ijarar da su.
17Za a yi kuka ko'ina cikin dukan
gonakin inabinku
Gama zan zo in yi muku horo.”
18Taku ta ƙare, ku da kuke marmarin
zuwan ranan nan ta Ubangiji!
Wane amfani wannan rana za ta yi
muku?
Rana ta baƙin ciki ce,
Ba ta murna ba.
19Zai zama kamar wanda ya tsere wa
zaki
Ya fāɗa a bakin beyar!
Ko kuwa kamar wanda ya komo
gida,
Ya dāfa bango, maciji ya sare shi.
20Ranar Ubangiji za ta kawo baƙin
ciki,
Ba murna ba.
Rana ce ta damuwa ba ta fara'a ba.
21 # Ish 1.11-14 Ubangiji ya ce,
“Na ƙi bukukuwanku na addini.
Ina ƙyamarsu!
22Sa'ad da kuka kawo mini hadayun
ƙonawa
Da hadayunku na tsaba, ba zan
karɓa ba.
Ba kuma zan karɓi turkakkun
dabbobinku
Waɗanda kuka miƙa mini hadayun
godiya ba.
23Ku yi shiru da yawan hargowar
waƙoƙinku.
Ba na so in saurari kaɗe-kaɗenku da
bushe-bushenku.
24Sai ku sa adalci da nagarta su gudano
a yalwace
Kamar kogin da ba ya ƙafewa.
25 # A.M 7.42,43 “Ya ku, jama'ar Isra'ila, ai, a waɗannan shekaru arba'in da kuka yi cikin jeji kuka kawo mini sadaka da hadayu, 26duk da haka, kuka ɗauki siffofin gumakanku na taurari, wato Sakkut da Kaiwan, waɗanda kuka yi wa kanku. 27Ni kuwa zan sa ku yi ƙaura zuwa wata ƙasa gaba da Dimashƙu.” Ubangiji, Allah Mai Runduna, shi ne ya faɗa.

Currently Selected:

Amos 5: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in