YouVersion Logo
Search Icon

Amos 3

3
Aikin Annabi
1Jama'ar Isra'ila, ku kasa kunne ga wannan saƙo da Ubangiji ya aiko muku, ya ce, “Na fitar da iyalanku duka daga Masar.
2“Daga cikin dukan al'umman da nake
ƙauna a duniya,
Ku kaɗai ne na sani,
Nake kuma kulawa da ku,
Don haka zan hukunta ku saboda
zunubanku.”
3Zai yiwu a ce mutum biyu za su yi
tafiya tare,
Amma su rasa shirya magana?
4Zai yiwu zaki yă yi ruri a jeji
Ba tare da ya kama nama ba?
Zai yiwu sagarin zaki yă yi gurnani a
kogonsa
In bai kama wani abu ba?
5Zai yiwu tsuntsu ya fāɗi ƙasa
In ba a kafa masa tarko ba?
Zai yiwu tarko ya zargu
In bai kama wani abu ne ba?
6Zai yiwu mutane su rasa firgita,
Idan aka busa ƙahon yaƙi a
birni?
Zai yiwu wata babbar masifa ta auko
wa birni
Ba da yardar Ubangiji ba?
7Hakika Ubangiji ba yakan aikata
kome ba,
Sai da sanin bayinsa annabawa.
8Zaki ya yi ruri!
Wa ba zai ji tsoro ba?
Sa'ad da Ubangiji ya yi magana!
Wa zai ƙi yin shelar maganarsa?
Faɗuwar Samariya
9Ka yi shela ga mazaunan fādar Ashdod da Masar, ka ce, “Duk ku taru a Samariya ku ga irin babban shashancin da ake yi a can, ku ga irin laifofin da ake aikatawa a birnin.”
10Ubangiji ya ce, “Waɗannan mutane suka cika gidajensu masu daraja da abubuwan da suka samo ta hanyar zamba, da ta kama-karya. Ta yadda za su yi su yi aminci ma, ba su sani ba.
11“Saboda haka abokan gaba za su
kewaye ƙasarsu,
Su hallakar da kagaransu,
Su washe gidajen nan nasu masu
daraja.”
12Ubangiji ya ce,
“Kamar yadda makiyayi yakan ceci
ƙafafu biyu
Ko kunne ɗaya na tunkiya daga
bakin zaki,
Haka nan kuma kima daga cikin
mutanen Samariya
Waɗanda suke zaman jin daɗi za su
tsira.
13Ku saurara yanzu,
Ku yi wa zuriyar Yakubu kashedi,”
In ji Ubangiji, Maɗaukaki.
14 # 2Sar 23.15 “Ran da na hukunta mutanen
Isra'ila saboda zunubansu,
Zan hallakar da bagadan Betel.
Za a kakkarya zankayen bagaden,
Su fāɗi ƙasa.
15Zan murmushe gidajensu na rani da
na damuna.
Zan hallakar da gidajen da aka
ƙawata da hauren giwa,
Kowane babban gida kuwa za a
rushe shi.”

Currently Selected:

Amos 3: HAU

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in