A.M 7:59-60
A.M 7:59-60 HAU
Suna ta jifan Istifanas, shi kuwa yana ta addu'a, yana cewa, “Ya Ubangiji Yesu, ka karɓi ruhuna.” Sa'an nan ya durƙusa, ya ɗaga murya da ƙarfi, ya ce, “Ya Ubangiji, kada ka ɗora musu wannan zunubi.” Da faɗar haka sai ya yi barci.