A.M 1
1
Alkawarin Zuwan Ruhu Mai Tsarki
1 #
Luk 1.1-4
Ya Tiyofalas, tarihin nan na farko wanda na rubuta, ya shafi dukan abubuwan da Yesu ya fara yi, da kuma waɗanda ya fara koyarwa, 2har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi aka kai shi Sama, bayan ya yi umarni ta wurin Ruhu Mai Tsarki ga manzannin da ya zaɓa. 3Ya bayyana kansa gare su a raye bayan shan wuya tasa, tare da tabbatarwa masu yawa, masu ƙarfi kuma, yana bayyana gare su a kai a kai har kwana arba'in, yana zancen al'amuran Mulkin Allah. 4#Luk 24.49 Sa'ad da yake tare da su, ya umarce su kada su tashi daga Urushalima, amma su jira cikar alkawarin nan da Uba ya yi, “wanda kuka ji daga bakina, 5#Mat 3.11; Mar 1.8; Luk 3.16; Yah 1.33domin Yahaya kam, da ruwa ya yi baftisma, amma kafin 'yan kwanaki da Ruhu Mai Tsarki za a yi muku baftisma.”
An Ɗauke Almasihu Sama
(Mar 16.19-20; Luk 24.50-53)
6Saboda haka da suka taru, suka tambaye shi suka ce, “Ya Ubangiji, yanzu ne za ka sāke kafa wa Isra'ila mulki?” 7Ya ce musu, “Sanin lokatai da zamanai, da Uba ya sa cikin ikonsa, ba naku ba ne. 8#Mat 28.19; Mar 16.15; Luk 24.47,48 Amma za ku sami iko sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya sauko muku, za ku kuma zama shaiduna a Urushalima, da duk ƙasar Yahudiya, da ta Samariya, har ya zuwa iyakar duniya.”
9 #
Mar 16.19; Luk 24.50,51 Da ya faɗi haka, suna cikin dubawa, sai aka ɗauke shi Sama, wani gajimare ya tafi da shi, ba su ƙara ganinsa ba. 10Suna cikin zuba ido sama, shi kuma yana tafiya, sai ga mutum biyu tsaye kusa da su, saye da fararen tufafi. 11Sai suka ce, “Ya ku mutanen Galili, don me kuke tsaye kuna duban sama? Yesun nan da aka ɗauke daga gare ku aka kai shi Sama, zai komo ne ta yadda kuka ga tafiyarsa zuwa Sama.”
Wanda Ya Karɓi Matsayin Yahuza
12Sai suka koma Urushalima daga dutsen nan da ake kira Dutsen Zaitun, wanda yake kusa da Urushalima, wajen mil ɗaya. 13#Mat 10.2-4; Mar 3.16-19; Luk 6.14-16 Da suka shiga birnin, suka hau soro inda suke zama, wato Bitrus, da Yahaya, da Yakubu, da Andarawas, da Filibus, da Toma, da Bartalamawas, da Matiyu, da Yakubu na Halfa, da Saminu Zaloti, da kuma Yahuza na Yakubu. 14Duk waɗannan da nufi ɗaya suka nace da addu'a, tare da mata, da Maryamu uwar Yesu, da kuma 'yan'uwansa.
15To, a kwanakin nan Bitrus ya miƙe tsaye cikin 'yan'uwa, (wajen mutum ɗari da ashirin ne a taron), ya ce, 16“Ya ku 'yan'uwana, lalle ne a cika Nassin nan da Ruhu Mai Tsarki ya faɗa a dā ta bakin Dawuda a game da Yahuza, wanda ya yi wa masu kama Yesu jagaba. 17Don an lasafta shi cikinmu dā, an kuma ba shi tasa hidima cikin aikin nan. 18#Mat 27.3-8 (To, shi mutumin nan, da ladan mugun aikinsa ya sayi wani fili, sai ya fāɗi da kā, cikinsa ya fashe, kayan cikinsa duk suka zubo. 19Wannan abu fa ya zama sananne ga dukan mazaunan Urushalima, har ake kiran filin Akaldama da harshensu, wato filin jini.) 20#Zab 69.25; Zab 109.8 Domin a rubuce yake a Zabura cewa,
“ ‘Gidansa yă zama yasasshe,
Kada kowa ya zauna a ciki.’
Da kuma,
‘Matsayinsa wani yă gada.’
21 #
Mat 3.16; Mar 1.9; Luk 3.21;
Mar 16.19; Luk 24.51 Don haka, lalle wani daga cikin mutanen nan da suke tare da mu, duk lokacin da Ubangiji Yesu yake cuɗanya da mu, 22tun daga baftismar da Yahaya ya yi, har ya zuwa ranar da aka ɗauke shi daga wurinmu aka kai shi zuwa Sama, wato ɗaya daga cikin mutanen nan ya zama shaidar tashinsa daga matattu, tare da mu.” 23Sai suka nuna mutum biyu, Yusufu mai suna Barsaba, wanda aka yi wa laƙabi da Yustus, da kuma Matiyas. 24Sai suka yi addu'a, suka ce, “Ya Ubangiji, masanin zuciyar kowa, a cikin waɗannan mutum biyu ka nuna wanda ka zaɓa, 25yă karɓi matsayi cikin aikin nan da manzancin nan da Yahuza ya bauɗe wa, don yă cike gurbinsa.” 26Sai suka yi musu kuri'a, Matiyas ya ci, aka kuma sa shi a cikin manzannin nan goma sha ɗaya.
Currently Selected:
A.M 1: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979