1Sam 2
2
Waƙar Hannatu
1 #
Luk 1.46-55
Hannatu kuwa ta yi addu'a ta ce,
“Ubangiji ya cika zuciyata da murna.
Ina farin ciki da abin da ya yi.
Ina yi wa maƙiyana dariya,
Ina matuƙar murna domin Allah ya taimake ni.
2“Babu wani mai tsarki kamar Ubangiji,
Babu wani mai kama da shi,
Ba mai kiyaye mu kamar Allahnmu.
3Kada ku ƙara yin magana ta girmankai,
Ku daina maganganunku na fariya,
Gama Ubangiji Allah shi ne masani,
Yana kuma auna dukkan aikin da mutum ya yi.
4An kakkarya bakunan ƙarfafan sojoji,
Amma rarrauna ya zama mai ƙarfi.
5Ƙosassun mutane suna ƙodago saboda abinci,
Masu fama da yunwa kuwa sun daina jin yunwa.
Bakarariya ta haifi 'ya'ya bakwai,
Wadda ta haifi 'ya'ya da yawa kuwa
ta rasa su duka.
6Ubangiji ne yake kashewa, ya kuma rayar,
Yana kai mutane kabari,
Ya kuma tā da su.
7Yakan sa waɗansu mutane su zama
matalauta,
Waɗansu kuwa attajirai.
Yakan ƙasƙantar da waɗansu,
Ya kuma ɗaukaka waɗansu.
8Yakan tā da matalauci daga cikin ƙura,
Yakan ɗaga mai bukata daga zaman baƙin ciki.
Ya sa su zama abokan 'ya'yan sarki,
Ya ɗora su a wurare masu maƙami.
Harsashin ginin duniya na Ubangiji ne,
A kansu ya kafa duniya.
9“Zai kiyaye rayukan amintattun
mutanensa,
Amma mugayen mutane za su lalace cikin duhu,
Ba ƙarfin mutum yake sa ya yi nasara ba.
10Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji,
Zai yi musu tsawa daga Sama.
Ubangiji zai hukunta dukan duniya,
Zai ba sarkinsa iko,
Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zama
mai nasara.”
11Sa'an nan Elkana ya koma gidansa a Rama, amma yaron ya zauna a Shilo, yana aikin Ubangiji a hannun Eli, firist.
'Ya'yan Eli Maza
12'Ya'yan Eli, maza kuwa, ba su da kirki, ba su kula da Ubangiji ba, 13Ko ka'idodi game da abin da firistoci za su karɓa a hannun jama'a. A maimakon haka, lokacin da mutum ya je domin ya miƙa hadayarsa, sai baran firist ya zo da rino a hannunsa a sa'ad da ake dafa naman. 14Sai ya caka rinon a cikin tukunyar, to, duk abin da ya cako wannan ya zama na firist. Haka suka yi ta yi wa dukan Isra'ilawa da suka zo miƙa hadaya a Shilo. 15Tun kuma kafin a ƙona kitse, baran firist ɗin yakan zo ya ce wa wanda yake yin hadayar. “Ka ba ni wanda firist zai gasa, gama ba zai karɓi dafaffen nama daga gare ka ba, sai dai ɗanye.”
16Idan mutumin ya ce, “To, bari a ƙona kitsen tukuna, sa'an nan ka ɗibi iyakar abin da kake bukata,” sai baran firist ɗin ya ce, “A'a, tilas ne ka ba ni yanzu, idan kuwa ba haka ba, zan ɗiba ƙarfi da yaji!”
17Zunubin 'ya'yan nan maza na Eli ya yi yawa a gaban Ubangiji, gama sun wulakanta hadayar Ubangiji ƙwarai da gaske.
Sama'ila a Shilo
18Yaron nan Sama'ila yana ta aiki gaban Ubangiji, yana sāye da falmaran. 19A kowace shekara mahaifiyarsa takan ɗinka 'yar rigar ado, ta kai masa a sa'ad da ita da mijinta sukan tafi miƙa hadayarsu ta shekara shekara. 20Eli kuwa yakan sa wa Elkana da matarsa albarka, ya ce, “Ubangiji ya ba ka waɗansu 'ya'ya ta wurin matan nan a maimakon wanda kuka ba Ubangiji.”
Bayan wannan sai su koma gida.
21Ubangiji ya sa wa Hannatu albarka, ta haifi 'ya'ya maza uku da mata biyu. Yaron nan Sama'ila kuwa ya girma a gaban Ubangiji.
Eli da 'Ya'yansa Maza
22Eli kuwa ya tsufa ƙwarai, yana kuma jin dukan abin da 'ya'yansa maza suke yi wa Isra'ilawa, da yadda suke kwana da matan da suke aiki a ƙofar alfarwa ta sujada. 23Sai ya ce musu, “Me ya sa kuke irin waɗannan abubuwa? Gama kowa yana faɗa mini irin mugayen abubuwan da kuke aikatawa. 24Haba 'ya'yana, ku bari! Jama'ar Ubangiji suna ta magana a kan wannan mugun abu. 25Idan mutum ya yi wa wani laifi, Allah yakan kāre shi, amma idan mutum ya yi wa Ubangiji zunubi, wa zai kāre shi?”
Amma ba su ji maganar mahaifinsu ba, gama Ubangiji ya riga ya yi shirin kashe su.
Annabci a kan Gidan Eli
26 #
Luk 2.52
Yaron nan Sama'ila ya yi ta girma da samun tagomashi a gaban Ubangiji da kuma mutane.
27Wani annabi ya zo wurin Eli da saƙo daga wurin Ubangiji ya ce, “Sa'ad da kakanka Haruna da iyalinsa suke bauta wa Fir'auna a Masar, na bayyana kaina gare shi. 28#Fit 28.1-4; L.Fir 7.35,36 Na zaɓi iyalinsa daga dukan kabilan Isra'ila domin su zama firistocina, su riƙa aiki a bagade, suna ƙona turare, su riƙa ɗaukar keɓaɓɓen akwatina cikin yi mini aiki. Na kuma yardar musu su sami rabonsu daga hadayun da aka ƙona a kan bagade. 29Me ya sa kuke haɗama a kan hadayuna da sadakokin da na umarta? Eli, don me kake girmama 'ya'yanka fiye da ni, ka bar su suna ta cinye rabo mafi kyau na hadayun jama'ata Isra'ila? 30Ni Ubangiji Allah na Isra'ila, na yi alkawari a dā cewa, ‘Kai da iyalinka da danginka za ku yi mini aikin firist har abada.’ Amma yanzu na ce ba zan yarda da wannan ba. Waɗanda suke girmama ni, zan girmama su. Waɗanda suke raina ni zan ƙasƙantar da su ƙwarai. 31Ga shi, lokaci yana zuwa da zan karkashe samari cikin iyalinka da danginka, har da ba za a sami wanda zai rayu har ya tsufa a gidanka ba. 32Za ka kasance da damuwa da jin kishi, za ka duba dukan albarkun da zan sa wa Isra'ila, amma a gidanka ba za a taɓa samun wanda zai rayu har ya tsufa ba. 33Zan dai bar ɗaya daga zuriyarka da rai, zai yi mini aikin firist, amma zai makance ya fid da zuciya ga kome. Dukan sauran zuriyarka kuwa za su yi mutuwa ƙarfi da yaji. 34#1Sam 4.11 Lokacin da 'ya'yanka biyu, Hofni da Finehas, za su mutu rana ɗaya wannan zai nuna maka abin da na faɗa sai ya cika. 35Zan zaɓar wa kaina amintaccen firist wanda zai aikata abin da nake so ya yi, zan kuwa ba shi zuriya da ko yaushe za su yi aiki a gaban zaɓaɓɓen sarkina. 36Dukan wanda ya ragu daga zuriyarka zai je wurin sarki ya roƙi kuɗi da abinci, zai kuma roƙa a yardar masa ya taimaki firistoci da aiki domin ya sami abin da zai ci.”
Currently Selected:
1Sam 2: HAU
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
@Bible Society of Nigeria 1979