Luka 8
8
Misalin mai shuka
1Bayan wannan sai Yesu ya zazzaga gari da ƙauye, yana wa’azin bisharar mulkin Allah. Sha Biyun nan kuwa suna tare da shi, 2da kuma waɗansu mata waɗanda aka warkar da su daga cututtukansu, da kuma mugayen ruhohi. Cikinsu akwai Maryamu (wadda ake kira Magdalin) wadda aljanu bakwai suka fito daga cikinta. 3Da Yowanna matar Kuza, manajan iyalin Hiridus; da Suzana; da waɗansu mata da yawa. Waɗannan mata suna taimaka musu cikin hidima, daga cikin abin da suke da shi na zaman gari.
(Mattiyu 13.1-9; Markus 4.1-9)
4Yayinda taron mai girma na taruwa, mutane kuma daga garuruwa dabam-dabam suna zuwa wurin Yesu, sai ya ba da wannan misali ya ce, 5“Wani manomi ya fita domin ya shuka irinsa. Da yana watsa irin, sai waɗansu suka fāɗi a kan hanya, aka tattaka su, tsuntsayen sararin sama kuma suka cinye su. 6Waɗansu suka fāɗi a kan dutse, da suka tsira sai suka yanƙwane don babu ruwa a wurin. 7Waɗansu kuma suka fāɗi a cikin ƙaya. Da suka yi girma tare, sai ƙayan suka shaƙe su. 8Waɗansu kuma har yanzu, suka fāɗi a ƙasa mai kyau, suka yi girma, suka ba da amfani riɓi ɗari-ɗari, fiye da abin da aka shuka.”
Da faɗin haka sai ya ce, “Duk mai kunnen ji, yă ji.”
(Mattiyu 13.10-17; Markus 4.10-12)
9Almajiransa suka tambaye shi ma’anar wannan misali. 10Sai ya ce, “Ku ne aka ba sanin asirin mulkin Allah, amma ga sauran mutane kam, ina magana da misalai, saboda,
“ ‘ko da yake suna kallo, ba za su gani ba,
ko da yake suna ji, ba za su gane ba.’
(Mattiyu 13.18-23; Markus 4.13-20)
11 “Ga ma’anar misalin, irin, shi ne maganar Allah. 12Waɗanda suka fāɗi a kan hanya su ne mutanen da suka ji, amma Iblis, yakan zo ya ɗauke maganar daga zuciyarsu, don kada su gaskata, su sami ceto. 13Na kan dutse kuwa, su ne da jin maganar, sukan karɓa da murna, amma ba su da saiwa. Sukan gaskata na ɗan lokaci, amma lokacin gwaji, sai su ja da baya. 14Irin da suka fāɗi a cikin ƙaya kuwa, su ne mutanen da suka ji, amma a kwana a tashi, tunanin kayan duniya, da neman arziki, da son jin daɗi, sukan hana su ba da ’ya’ya. 15Amma irin da suka fāɗi a ƙasa mai kyau kuwa, su ne mutane masu kyakkyawar zuciya, mai kyau, da suka ji, suka riƙe, suka kuma jimre har suka ba da ’ya’ya.”
Fitila a kan wurin ajiye fitila
(Markus 4.21-25)
16 “Ba mai ƙuna fitila sa’an nan ya ɓoye ta a cikin tulu, ko kuma ya sa ta a ƙarƙashin gado ba. A maimakon haka, yakan sa ta a kan wurin ajiye fitila, saboda mutane masu shigowa su ga haske. 17Ba abin da yake ɓoye da ba za a fallasa ba. Kuma ba abin da yake rufe, da ba za a sani ba, ko a fitar da shi a fili ba. 18Saboda haka, ku yi tunani da kyau yadda kuke saurara. Duk wanda yake da shi, za a ƙara masa, duk wanda ba shi da shi kuma, abin da yake tsammani yana da shi ma, za a karɓe daga gare shi.”
Mahaifiyar Yesu da ’yan’uwansa
(Mattiyu 12.46-50; Markus 3.31-35)
19Sai uwar Yesu da ’yan’uwansa suka zo, domin su gan shi, amma ba su iya zuwa kusa da shi ba, saboda taron. 20Sai wani ya faɗa masa cewa, “Ga uwarka da ’yan’uwanka suna tsaye a waje suna so su gan ka.”
21Ya amsa ya ce, “Mahaifiyata da ’yan’uwana, su ne waɗanda suke jin maganar Allah, suna kuma aikata ta.”
Yesu ya kwantar da ruwa da iska
(Mattiyu 8.23-27; Markus 4.35-41)
22Wata rana Yesu ya ce wa almajiransa, “Mu haye zuwa wancan gefen tafkin.” Sai suka shiga jirgin ruwa suka fara tafiya. 23Da suna cikin tafiya, sai barci ya kwashe shi. Sai wata babban iska ta taso kan tafkin, har ruwa ya fara shiga cikin jirgin. Suka shiga babban hatsari.
24Almajiran suka je suka tashe shi daga barci, suka ce, “Ubangiji, Ubangiji, za mu nutse!”
Ya tashi ya kwaɓe iskar da kuma haukar ruwan. Sai ruwan da iskar suka natsu. Kome ya yi tsit. 25Sai ya tambayi almajiransa, “Ina bangaskiyarku?”
A cikin tsoro da mamaki, suka ce wa junansu, “Wane ne wannan? Yana ba da umarni ga iska da ruwa ma, kuma suna biyayya da shi?”
Warkar da mai aljanu
(Mattiyu 8.28-34; Markus 5.1-20)
26Suka shiga jirgin ruwa zuwa yankin Gerasenawa da yake a hayin tafkin, daga wajen Galili. 27Da Yesu ya sauka daga jirgin, sai ga wani mutum mai aljanu daga garin. Mutumin ya daɗe bai sa tufafi ba, kuma ba ya zama a gida. Yana zama a cikin kaburbura. 28Da ya ga Yesu, sai mutumin ya ɗaga murya da ƙarfi, ya fāɗi a gabansa, yana ihu cewa, “Ina ruwanka da ni, Yesu, Ɗan Allah Mafi Ɗaukaka? Ina roƙonka, kada ka ba ni wahala!” 29Gama Yesu ya riga ya umarci mugun ruhun ya fita daga mutumin. Sau da yawa mugun ruhun ya sha kamunsa. Ko da yake akan daure shi hannu da ƙafa, da sarƙa, a kuma yi gadinsa, amma yakan tsinke sarƙoƙinsa, aljanun kuma su kore shi zuwa wuraren kaɗaici, inda ba kowa.
30Yesu ya tambaye shi, “Mene ne sunanka?”
Sai ya amsa, “Tuli,”#8.30 Lejiyon yana nufin Tuli. gama aljanu masu ɗumbun yawa ne suna cikinsa. 31Suka yi ta roƙonsa kada yă umarce su su shiga ramin Abis.
32A wurin kuwa, akwai babban garken aladu da suke kiwo a gefen tudu. Aljanun suka roƙi Yesu ya bar su, su shiga cikin aladun, ya kuwa yardar musu. 33Da aljanun suka fita daga cikin mutumin, sai suka shiga cikin aladun. Garken kuma ya gangara daga kan tudun zuwa cikin tafkin, kuma suka nutse.
34Da masu kiwon aladun suka ga abin da ya faru, sai suka ruga da gudu zuwa garin da kewaye suka kai labari. 35Mutanen kuma suka fito don su ga abin da ya faru. Da suka iso wurin Yesu, sai suka tarar da mutumin da aljanun suka fita daga cikinsa, yana zaune kusa da Yesu sanye da tufafi, kuma cikin hankalinsa, sai tsoro ya kama su. 36Waɗanda suka ga abin da faru, suka gaya wa mutanen yadda aka warkar da mai aljanun. 37Sai dukan mutanen yankin Gerasenawa suka roƙi Yesu ya bar su, don sun tsorata sosai. Sai Yesu ya shiga jirgin ruwa ya tafi.
38Mutumin da aka fitar da aljanun daga cikinsa, ya roƙi Yesu don yă tafi tare da shi, amma Yesu ya sallame shi ya ce, 39“Koma gida, ka shaida babban alherin da Allah ya yi maka.” Sai mutumin ya tafi yana faɗin abin da Yesu ya yi masa a duk garin.
Yarinya da ta mutu da mace marar lafiya
(Mattiyu 9.18-26; Markus 5.21-43)
40Da Yesu ya koma, taron suka marabce shi, don dā ma duk suna jiransa. 41Sai wani mutum mai suna Yayirus, wani mai mulkin majami’a, ya zo ya fāɗi a gaban Yesu, yana roƙonsa ya zo gidansa, 42domin diyarsa ɗaya tak, wadda ta kai shekara goma sha biyu, tana bakin mutuwa. Da Yesu yake kan hanyarsa, taron mutane masu yawa suka yi ta matsa shi a kowane gefe. 43A wurin kuwa, akwai wata mace wadda tana da ciwon zubar da jini, har na shekara goma sha biyu, amma babu wanda ya iya warkar da ita. 44Sai ta zo ta bayansa, ta taɓa bakin rigarsa. Nan da nan, zubar da jininta ya tsaya.
45Yesu ya yi tambaya, “Wa ya taɓa ni?”
Bayan kowa ya yi musu, sai Bitrus ya ce, “Ubangiji, ai, mutane da yawa suna matsinka ta kowane gefe.”
46Amma Yesu ya ce, “Wani ya taɓa ni, na san cewa iko ya fita daga wurina.”
47Sai macen, da ta ga ba halin ɓoyewa, sai ta fita, jikinta na rawa, ta fāɗi a gabansa. A gaban dukan mutanen, ta faɗi dalilin da ya sa ta taɓa shi, da yadda ta warke nan take. 48Sai Yesu ya ce mata, “Diyata, bangaskiyarki ta warkar da ke. Ki sauka lafiya.”
49Yayinda Yesu na cikin magana har yanzu, sai ga wani daga gidan Yayirus, mai mulkin majami’ar ya ce, “Kada ka ƙara damun malam, diyarka ta rasu.”
50Da Yesu ya ji wannan, sai ya ce wa Yayirus, “Kada ka ji tsoro, ka gaskata, za a kuma warkar da ita.”
51Da ya iso gidan Yayirus, sai ya hana kowa yă bi shi cikin ɗakin, sai dai Bitrus, da Yohanna, da Yaƙub, da kuma mahaifin da mahaifiyar. 52Ana cikin haka, dukan mutanen kuma sai kuka da makoki suke ta yi, domin yarinyar. Sai Yesu ya ce, “Ka daina yin kuka, ba tă mutu ba, tana barci ne.”
53Sai suka yi masa dariya, da yake sun san cewa, ta mutu. 54Amma Yesu ya kama ta a hannu ya ce, “Diyata, tashi.” 55Ruhunta ya dawo, kuma ta tashi, nan take. Yesu ya ce musu, su ba ta wani abu tă ci. 56Iyayenta suka yi mamaki, amma ya ba su umarni kada su faɗa wa kowa abin da ya faru.
Currently Selected:
Luka 8: SRK
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.