YouVersion Logo
Search Icon

Luka 20

20
An yi shakkar ikon Yesu
(Mattiyu 21.23-27; Markus 11.27-33)
1Wata rana da Yesu yana koyar da mutane, yana musu wa’azin bishara a filin haikalin, sai manyan firistoci da malaman dokoki, tare da dattawan suka zo wurinsa. 2Suka ce masa, “Gaya mana, da wane iko kake yin waɗannan abubuwa. Wa ya ba ka wannan ikon?”
3Ya amsa ya ce, “Ni ma zan yi muku wata tambaya. Ku faɗa mini, 4baftismar Yohanna, daga sama ne ta fito, ko kuwa daga wurin mutane ne?”
5Sai suka yi shawara da junansu, suka ce, “In muka ce, ‘Daga sama ne,’ zai tambaya, ‘To, don me ba ku gaskata shi ba?’ 6Amma in kuma muka ce, ‘Daga mutane ne,’ dukan mutanen za su jajjefe mu da duwatsu, domin sun tabbata cewa, Yohanna annabi ne.”
7Don haka, sai suka amsa cewa, “Ba mu san inda ta fito ba.”
8Yesu ya ce, “To, ni ma ba zan gaya muku, ko da wane iko ne, nake yin waɗannan abubuwa ba.”
Misalin ’yan haya
(Mattiyu 21.33-46; Markus 12.1-12)
9Sai ya ci gaba da gaya wa mutanen wannan misali ya ce, “Wani mutum ya yi gonar inabi, sai ya ba da hayarta ga waɗansu manoma, sa’an nan ya yi wata doguwar tafiya. 10A lokacin girbi, sai ya aiki bawa zuwa wurin masu hayan, don su ba shi daga cikin ’ya’yan inabin. Amma ’yan hayan suka yi wa bawan nan dūka, suka kore shi hannu wofi. 11Ya sāke aikan wani bawa, shi ma suka yi masa dūka, suka kunyata shi, suka kuma kore shi hannu wofi. 12Har yanzu, ya sāke aikan na uku, amma suka ji masa rauni, suka jefar da shi waje.
13 “Sai mai gonar inabin ya ce, ‘Me zan yi? Zan aiki ɗana da nake ƙauna, wataƙila za su girmama shi.’
14 “Amma da ’yan hayan suka gan shi, sai suka tattauna zancen, suka ce, ‘Wannan shi ne magājin, mu kashe shi sa’an nan gādon zai zama namu!’ 15Sai suka fitar da shi waje, suka kashe shi.
“To, me mai gonar inabin zai yi da su? 16Zai zo ya karkashe masu hayan nan, ya ba wa waɗansu gonar inabin.”
Da mutanen suka ji wannan, sai suka ce, “Allah ya sawwaƙa!”
17Yesu ya zura musu ido ya ce, “To, mene ne ma’anar abin da aka rubuta cewa,
“ ‘Dutsen da magina suka ƙi,
shi ne kuwa ya zama dutsen kan ginin’ # 20.17 Ko kuwa dutsen kusurwa # 20.17 Zab 118.22
18 Duk wanda ya fāɗi a kan dutsen nan, zai kakkarye. Kuma in dutsen nan ya fāɗi a kan wani, zai murƙushe shi.”
19Malaman dokoki da manyan firistoci, suka nemi hanyar kama shi nan da nan, domin sun san cewa, ya yi wannan misali a kansu ne, amma suna jin tsoron mutane.
Biyan haraji ga Kaisar
(Mattiyu 22.15-22; Markus 12.13-17)
20Sai suka sa masa ido, suka aiki ’yan leƙen asiri, waɗanda suka nuna kamar su masu gaskiya ne, suna nufin su kama shi game da abin da zai faɗa, domin su ba da shi ga gwamna mai mulki, da mai iko. 21Sai ’yan leƙen asirin suka tambaye shi, suka ce, “Malam, mun sani kana faɗin, kuma kana koyar da abin da yake daidai, ba ka kuma nuna bambanci, amma kana koyar da hanyar Allah bisa ga gaskiya. 22Daidai ne mu biya haraji ga Kaisar, ko babu?”
23Ya gane makircinsu, sai ya ce musu, 24“Nuna mini dinari. Hoton wane ne, kuma rubutun wane ne a kai?”
Suka amsa, “Na Kaisar.”
25Sai ya ce musu, “Ku ba wa Kaisar abin da yake na Kaisar, ku kuma ba wa Allah abin da yake na Allah.”
26Ba su iya kama shi a kan abin da ya faɗa a fili ba. Amsarsa ya ba su mamaki, shi ya sa suka yi shiru.
Ba aure a tashin matattu
(Mattiyu 22.23-33; Markus 12.18-27)
27Waɗansu Sadukiyawa da suke cewa, ba tashin matattu, suka zo wurin Yesu da tambaya cewa, 28“Malam, Musa ya rubuta mana cewa, ‘In ɗan’uwan wani mutum ya mutu, ya bar mata amma ba ’ya’ya, dole mutumin ya aure gwauruwar, ya samo wa ɗan’uwansa ’ya’ya.’ 29To, an yi waɗansu ’yan’uwa bakwai. Na fari ya auri wata mace, ya mutu ba ’ya’ya. 30Na biyun, 31da na ukun suka aure ta. Haka nan dukansu bakwai suka mutu babu ’ya’ya. 32A ƙarshe, ita macen ma ta mutu. 33Shin, a tashin matattu, matar wa za tă zama? Tun da su bakwan nan, sun aure ta.”
34Yesu ya amsa ya ce, “Mutanen zamanin nan suna aure, suna kuma ba da aure, 35amma su waɗanda aka ga sun cancantar kasancewa a zamanin can, da kuma na tashin matattu, ba za su yi aure, ko su ba da aure ba. 36Kuma ba za su sāke mutuwa ba, gama su kamar mala’iku ne. Su ’ya’yan Allah ne, tun da su ’ya’yan tashin matattu ne. 37Amma bisa ga labari na bishiya nan, mai cin wuta da Musa ya gani a jeji, ko Musa ma, ya nuna cewa, matattu suna tashi. Gama ya kira Ubangiji, ‘Allah na Ibrahim, da Allah na Ishaku, da kuma Allah na Yaƙub.’ 38Shi ba Allah na matattu ba ne, amma na masu rai ne, gama a gare shi, duka na da rai.”
39Sai waɗansu malaman dokoki suka amsa suka ce, “Ka faɗi daidai, malam!” 40Kuma ba wanda ya sami ƙarfin halin yin masa waɗansu tambayoyi.
Kiristi ɗan wane ne?
(Mattiyu 22.41-46; Markus 12.35-37)
41Sai Yesu ya ce musu, “Yaya suke cewa, ‘Kiristi ɗan Dawuda ne?’ 42Dawuda da kansa ya faɗa a cikin Zabura,
“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina,
“Zauna a hannun damana,
43 sai na sa abokan gābanka
su zama matashin sawunka.” ’ # 20.43 Zab 110.1
44 Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji.’ Ta, yaya zai zama ɗansa?”
(Mattiyu 23.1-36; Markus 12.38-40; Luka 11.37-54)
45Yayinda dukan mutane suna cikin sauraronsa, sai Yesu ya ce wa almajiransa, 46“Ku yi hankali da malaman dokoki. Sukan so sa manyan riguna suna zaga, suna sha’awan karɓan gaisuwa a wuraren kasuwanci, da kuma wuraren zama mafi daraja a majami’u, da wuraren bangirma a bukukkuwa. 47Suna mamaye gidajen gwauraye, kuma don burga, suna dogayen addu’o’i. Ga irin waɗannan mutane, za a yi musu hukunci mai tsanani sosai.”

Currently Selected:

Luka 20: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in