Luka 13
13
A tuba ko a hallaka
1A yanzun fa, akwai waɗansu da suka kasance a lokacin can, suka ba Yesu labarin Galiliyawa da Bilatus ya gauraye jininsu tare da jinin hadayunsu. 2Yesu ya amsa ya ce, “Kuna tsammani waɗannan Galiliyawan sun fi dukan sauran Galiliyawa zunubi ne, shi ya sa suka sha irin wannan wahala? 3Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka. 4Ko kuwa kuna tsammani, sha takwas ɗin nan da suka mutu lokacin da hasumiya a Silowam ya fāɗi a kansu, sun fi dukan sauran mutanen Urushalima laifi ne? 5Ina gaya muku, a’a! Amma in ba ku tuba ba, ku ma duka za ku hallaka.”
6Sai ya ba su wannan misali ya ce, “Wani mutum yana da itacen ɓaure, da aka shuka a gonar inabinsa. Da ya je cire ’ya’yan itacen, sai ya tarar ba tă yi ’ya’ya ba. 7Sai ya ce wa mai lura da gonar inabin, ‘Yau shekara uku ke nan ina zuwa neman ’ya’yan ɓaure daga itacen nan, amma ba na samun kome. Sare shi! Don me za a bar shi ya tare wuri.’
8 “Mutumin ya amsa ya ce, ‘Ranka yă daɗe, ka bar shi, in yi masa banƙasa, in kuma zuba masa taki har na shekara ɗaya. 9In kuwa ya ba da ’ya’ya shekara mai zuwa, yana da kyau! In kuwa ba haka ba, sai ka sare shi.’ ”
Yesu ya warkar da mace gurguwa a ranar Asabbaci.
10Wata ranar Asabbaci, Yesu yana koyarwa a wata majami’a, 11a wurin kuwa, akwai wata mace wadda aljani ya gurgunta, har na shekaru goma sha takwas. Duk ta tanƙware, ba ta ma iya miƙewa ko kaɗan. 12Da Yesu ya gan ta, sai ya kirata gaba, ya ce mata, “Mace, an ’yantar da ke daga rashin lafiyarki.” 13Sai ya ɗibiya hannuwansa a kanta, nan da nan sai ta miƙe, ta yabi Allah.
14Amma mai mulkin majami’ar ya ji haushi da Yesu ya yi warkarwa a ranar Asabbaci. Sai ya ce wa mutanen, “Akwai ranaku shida da ya kamata a yi aiki. Saboda haka, ku zo a ranakun nan a warkar da ku, ba ranar Asabbaci ba.”
15Ubangiji ya amsa masa ya ce, “Ku munafukai! Ashe, kowannenku ba yakan kunce bijiminsa ko jakinsa, yă kai shi waje yă ba shi ruwa, a ranar Asabbaci ba? 16Ashe, bai kamata a ’yantar da macen nan, diyar zuriyar Ibrahim, wadda Shaiɗan ya daure, har shekara goma sha takwas, a ranar Asabbaci, daga abin da ya daure ta ba?”
17Sa’ad da ya faɗi wannan, sai duka masu gāba da shi suka kunyata. Amma mutane kuwa suka yi murna saboda dukan abubuwan banmamaki da yake yi.
Misalai na ƙwayar mustad da na yisti
(Mattiyu 13.31-33; Markus 4.30-32)
18Sai Yesu ya yi tambaya ya ce, “Yaya mulkin Allah yake? Da me zan kwatanta shi? 19Yana kama da ƙwayar mustad, wadda wani mutum ya ɗauka, kuma ya shuka a gonarsa. Ta yi girma, ta zama itace, kuma tsuntsayen sararin sama suka huta a rassansa.”
20Ya sāke tambaya, “Da me zan kwatanta mulkin Allah? 21Yana kama da yisti wadda mace ta ɗauka, ta kwaɓa garin alkama mai yawa da shi, har sai da yistin ya gauraye kullun duka.”
Matsattsiyar ƙofa
(Mattiyu 7.13,14,21-23)
22Sa’ad da Yesu yana kan hanyarsa zuwa Urushalima, sai ya bi ta cikin garuruwan da ƙauyukan, yana koyarwa. 23Sai wani ya tambaye shi ya ce, “Ya Ubangiji, shin, wai mutane kima ne kawai za su sami ceto?”
Ya ce musu, 24“Ku yi matuƙar ƙoƙari ku shiga ta matsattsiyar ƙofa, domin ina faɗa muku, mutane da yawa za su yi ƙoƙarin shiga, amma ba za su iya ba. 25Da zaran maigidan ya tashi ya rufe ƙofar, za ku tsaya a waje kuna ƙwanƙwasawa, kuna roƙo cewa, ‘Ranka yă daɗe, buɗe mana ƙofa.’
“Amma shi zai amma ya ce, ‘Ni ban san ku, ko inda kuka fito ba.’
26 “Sa’an nan za ku ce, ‘Haba, mu da muka ci, muka sha tare da kai, har ka yi koyarwa a cikin titi-titi namu.’
27 “Amma shi zai amma ya ce, ‘Ban san ku, ko inda kuka fito ba. Ku rabu da ni, dukan ku masu aikata mugunta!’
28 “Za a yi kuka a can, da cizon haƙora, sa’ad da kuka ga Ibrahim, da Ishaku, da Yaƙub, da dukan annabawa a mulkin Allah, amma ku kuwa, za a jefar da ku a waje. 29Mutane za su zo daga gabas, da yamma, da kudu, da arewa, su ɗauki wuraren zamansu a bikin, a cikin mulkin Allah. 30Tabbatacce, akwai waɗansu da suke na ƙarshe, da za su zama na farko, na farko kuma, da za su zama na ƙarshe.”
Baƙin cikin Yesu domin Urushalima
(Mattiyu 23.37-39)
31A wannan lokaci, waɗansu Farisiyawa suka zo suka ce wa Yesu, “Ka bar nan ka tafi wani wuri dabam. Hiridus yana so ya kashe ka.”
32Ya amsa ya ce, “Ku je ku gaya wa dilan nan, wato, mai makirci cewa, ‘Da yau da kuma gobe, zan fitar da aljanu, in kuma warkar da mutane, sa’an nan a rana ta uku in cika burin aikina. 33Duk da haka, dole in ci gaba da aikin a yau, da kuma gobe, sa’an nan in ci gaba da yin haka kashegari kuma, gama tabbatacce, ba annabi da yakan mutu a bayan birnin Urushalima!’
34 “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kika kashe annabawa, kuma kika jefa wa waɗanda aka aika gare ki da duwatsu. Sau da yawa na yi kewan in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, kamar yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma ba ki yarda ba! 35Duba, an bar muku gidanku fanko. Ina kuwa faɗa muku, ba za ku sāke ganina ba, sai kun ce, ‘Mai albarka ne shi wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”
Currently Selected:
Luka 13: SRK
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.