Yohanna 5
5
Warkarwa a tafki
1Bayan an ɗan jima, sai Yesu ya haura zuwa Urushalima don wani bikin Yahudawa. 2To, a Urushalima akwai wani tafki kusa da Ƙofar Tumaki, wanda a yaren Arameyik ake kira Betesda#5.2 Waɗansu rubuce-rubucen hannu na dā suna da Betzata; waɗansu kuma suna da Betsaida ne a nan. an kuma kewaye shi da shirayi biyar. 3A nan naƙasassu da yawa sukan kwanta, makafi, guragu, shanyayyu.#5.3 Waɗansu rubuce-rubucen hannu marar muhimmanci sosai suna da shanyayyu, kuma suka jira a motsa ruwaye. 4 Lokaci-lokaci mala’ikan Ubangiji yakan sauko ya motsa ruwaye. Mutum na farko da ya shiga tafkin bayan motsawa zai warke daga kowace cutar da yake da ita. 5Akwai wani da yake nan ba shi da amfani shekara talatin da takwas. 6Da Yesu ya gan shi kwance a can ya kuma sami labari cewa ya daɗe a wannan hali, sai ya tambaye shi, “Kana so ka warke?”
7Marar amfanin nan ya ce, “Ranka yă daɗe, ba ni da wanda zai taimaka yă sa ni a cikin tafkin sa’ad da aka motsa ruwan. Yayinda nake ƙoƙarin shiga, sai wani yă riga ni.”
8Sai Yesu ya ce masa, “Tashi! Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.” 9Nan take mutumin ya warke; ya ɗauki tabarmarsa ya yi tafiya.
A ranar da wannan ya faru ranar Asabbaci ce, 10saboda haka kuwa Yahudawa suka ce wa mutumin da aka warkar, “Yau Asabbaci ne; doka ta hana ka ɗauki tabarmarka.”
11Amma ya amsa ya ce, “Mutumin da ya warkar da ni shi ya ce mini, ‘Ɗauki tabarmarka ka yi tafiya.’ ”
12Sai suka tambaye shi suka ce, “Wane ne wannan da ya ce maka ka ɗauke ta ka yi tafiya?”
13Mutumin da aka warkar kuwa bai ma san ko wane ne ba ne, gama Yesu ya ɓace cikin taron da yake can.
14Daga baya Yesu ya same shi a haikali ya ce masa, “Ga shi, ka warke. Ka daina yin zunubi, in ba haka ba wani abin da ya fi wannan muni zai iya samunka.” 15Sai mutumin ya je ya gaya wa Yahudawa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
Rai ta wurin Ɗan
16To, domin Yesu yana yin waɗannan abubuwa a ranar Asabbaci, sai Yahudawa suka tsananta masa. 17Yesu ya ce musu, “Ubana yana cikin aikinsa kullum har yă zuwa wannan rana, haka ni ma, ina kan aiki.” 18Don haka Yahudawa suka ƙara nema su kashe shi; ba don yă karya Asabbaci kawai ba, har ma yana ce Allah Ubansa ne, yana mai da kansa daidai da Allah.
19Sai Yesu ya ba su wannan amsa cewa, “Gaskiya nake gaya muku, Ɗan ba ya iya yin kome da kansa; yana yin abin da ya ga Ubansa yake yi ne kawai, gama duk abin da Uban yake yi shi ne Ɗan ma yake yi. 20Gama Uban yana ƙaunar Ɗan yana kuma nuna masa duk abin da yake yi. I, za ku kuwa yi mamaki, gama zai nuna masa abubuwan da suka fi waɗannan girma. 21Gama kamar yadda Uban yake tā da matattu yake kuma ba su rai, haka ma Ɗan yake ba da rai ga wanda ya ga dama. 22Bugu da ƙari, Uban ba ya hukunta kowa, sai dai ya danƙa dukan hukunci a hannun Ɗan, 23don kowa yă girmama Ɗan kamar yadda yake girmama Uban. Wanda ba ya girmama Ɗan ba ya girmama Uban, da ya aiko shi ke nan.
24 “Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ya ji maganata ya kuma gaskata da wanda ya aiko ni yana da rai madawwami ba za a kuma hukunta shi ba; ya riga ya ƙetare daga mutuwa zuwa rai. 25Gaskiya nake gaya muku, lokaci yana zuwa har ma ya riga ya zo sa’ad da matattu za su ji muryar Ɗan Allah waɗanda kuwa suka ji za su rayu. 26Gama kamar yadda Uban yana da rai a cikinsa, haka ya sa Ɗan yă kasance da rai a cikin kansa. 27Ya kuma ba shi iko yă hukunta domin shi Ɗan Mutum ne.
28 “Kada ku yi mamakin wannan, gama lokaci yana zuwa da duk waɗanda suke cikin kaburbura za su ji muryarsa 29su kuma fito, waɗanda suka aikata nagarta za su tashi zuwa ga rai, waɗanda kuma suka aikata mugunta za su tashi zuwa ga hukunci. 30Ni kaɗai dai ba na iya yin kome, ina shari’a ne bisa ga abin da na ji. Shari’ata kuwa mai adalci ce. Gama ba na neman gamsar da kaina, sai dai in gamshi shi wanda ya aiko ni.
Shaidu game da Yesu
31 “In na ba da shaida a kaina, shaidata ba gaskiya ba ce. 32Akwai wani mai ba da shaida mai kyau a kaina, na kuma san cewa shaidarsa game da ni gaskiya ce.
33 “Kun aika wajen Yohanna ya kuma yi shaida a kan gaskiya. 34Ba cewa ina neman shaidar mutum ba ne; sai dai na faɗi haka ne domin ku sami ceto. 35Yohanna fitila ne da ya ci ya kuma ba da haske, kun kuwa zaɓa ku ji daɗin haskensa na ɗan lokaci.
36 “Ina da shaidar da ta fi ta Yohanna ƙarfi. Gama aikin nan da Uba ya ba ni in kammala, wanda kuwa nake yi, yana ba da shaida cewa Uba ne ya aiko ni. 37Uba da ya aiko ni kuwa kansa ya yi shaida game da ni. Ba ku taɓa jin muryarsa ko ganin siffarsa ba, 38maganarsa kuwa ba ta zama a cikinku, gama ba ku gaskata da wanda ya aiko ni ba. 39Kuna ta nazarin Nassosi da himma don kuna tsammani ta wurinsu ne kuna samun rai madawwami. Nassosin nan ne suke ba da shaida a kaina, 40duk da haka kun ƙi zuwa wurina domin ku sami rai.
41 “Ni ba na neman yabon mutane, 42na fa san ku. Na san cewa ba ku da ƙaunar Allah a cikin zukatanku. 43Na zo a cikin sunan Ubana, ba ku kuwa karɓe ni ba; amma a ce wani dabam ya zo a cikin sunan kansa, za ku karɓe shi. 44Ta yaya za ku gaskata in kuna neman yabon junanku, ba kwa kuwa yin ƙoƙarin neman yabon da yake zuwa daga Allah Makaɗaici?
45 “Kada fa ku yi tsammani zan yi ƙararku wurin Uba. Akwai mai yin ƙararku, shi ne Musa, wanda kuke dogara da shi. 46Da a ce kun gaskata da Musa, da kun gaskata ni, domin ya rubuta game da ni. 47Amma da yake ba ku gaskata abin da ya rubuta ba, yaya za ku gaskata maganata?”
Currently Selected:
Yohanna 5: SRK
Highlight
Share
Copy
Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.