Farawa 35
35
Yaƙub ya koma zuwa Betel
1Sa’an nan Allah ya ce wa Yaƙub, “Haura zuwa Betel ka yi zama a can, ka kuma gina bagade a can wa Allah wanda ya bayyana gare ka sa’ad da kake gudu daga ɗan’uwanka Isuwa.”
2Saboda haka Yaƙub ya ce wa gidansa da kuma dukan waɗanda suke tare da shi, “Ku zubar da baƙin allolin da kuke da su, ku tsarkake kanku, ku kuma canja tufafinku. 3Sa’an nan ku zo, mu haura zuwa Betel, inda zan gina bagade wa Allah wanda ya amsa mini a ranar wahalata, wanda kuma ya kasance tare da ni a dukan inda na tafi.” 4Saboda haka suka ba Yaƙub dukan baƙin allolin da suke da su, da zoban da suke kunnuwansu, sai Yaƙub ya binne su a ƙarƙashin itacen oak a Shekem. 5Sa’an nan suka kama hanya, tsoron Allah kuwa ya kama dukan garuruwan da suke kewayensu har babu wanda ya iya bin su.
6Yaƙub da dukan mutanen da suke tare da shi suka zo Luz (wato, Betel) a ƙasar Kan’ana. 7A can ya gina bagade, ya kuma kira wurin El Betel,#35.7 El Betel yana nufin Allah na Betel. gama a can ne Allah ya bayyana kansa gare shi sa’ad da yake gudu daga ɗan’uwansa.
8To, Debora, ungozomar Rebeka ta rasu aka kuma binne ta a ƙarƙashin itacen oak, ƙasa da Betel. Saboda haka aka kira wurin Allon Bakut.#35.8 Allon yana nufin itacen oak na kuka.
9Bayan Yaƙub ya komo daga Faddan Aram,#35.9 Wato, arewa maso yammancin Mesofotamiya, haka ma a aya 26 sai Allah ya bayyana gare shi, ya kuma albarkace shi. 10Allah ya ce masa, “Sunanka Yaƙub#35.10 Yaƙub yana nufin ya kama ɗiɗɗige, a habaici dai, ya ruɗi. ne, amma ba za a ƙara kira ka Yaƙub ba; sunanka zai zama Isra’ila.”#35.10 Isra’ila yana nufin kokawa da Allah. Saboda haka ya ba shi suna Isra’ila.
11Sai Allah ya ce masa, “Ni ne Allah Maɗaukaki#35.11 Da Ibraniyanci El-Shaddai, ka yi ta haihuwa, ka kuma riɓaɓɓanya. Al’umma da tarin al’ummai za su fito daga gare ka, sarakuna kuma za su fito daga jikinka. 12Ƙasar da na ba wa Ibrahim da Ishaku, zan kuma ba ka, zan kuma ba da wannan ƙasa ga zuriyarka a bayanka.” 13Sa’an nan Allah ya tashi sama daga gare shi a wurin da ya yi magana da shi.
14Yaƙub kuwa ya kafa al’amudin dutse a inda Allah ya yi magana da shi, ya zuba hadaya ta sha a kansa; ya kuma zuba mai a kansa. 15Yaƙub ya kira inda Allah ya yi magana da shi, Betel.#35.15 Betel yana nufin gidan Allah.
Mutuwar Rahila da Ishaku
16Sa’an nan suka tashi daga Betel. Yayinda suna da ɗan nisa da Efrat, sai Rahila ta fara naƙuda ta kuwa sha wahala sosai. 17Sa’ad da take cikin zafin haihuwa, sai macen da ta karɓi haihuwar ta ce mata, “Kada ki ji tsoro, gama yanzu kin sami wani ɗa.” 18Yayinda take jan numfashinta na ƙarshe, sai ta ba wa ɗanta suna Ben-Oni.#35.18 Ben-Oni yana nufin ɗa na wahalata. Amma mahaifinsa ya kira shi Benyamin.#35.18 Benyamin yana nufin ɗa na hannun damana.
19Ta haka Rahila ta rasu, aka kuma binne ta a hanya zuwa Efrata (wato, Betlehem). 20Yaƙub ya kafa al’amudi bisa kabarinta, al’amudin kabarin Rahila ke nan, wanda yake can har wa yau.
21Isra’ila ya yi gaba, ya kafa tentinsa gaba da Migdal Eder. 22Yayinda Isra’ila yana zama a wancan yanki, Ruben ya shiga ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar mahaifinsa, Isra’ila kuwa ya ji labari.
Yaƙub ya haifi ’ya’ya maza goma sha biyu.
23’Ya’yan Liyatu maza,
Ruben shi ne ɗan fari na Yaƙub.
Sauran su ne, Simeyon, Lawi, Yahuda, Issakar da Zebulun.
24’Ya’yan Rahila maza su ne,
Yusuf da Benyamin.
25’Ya’yan Bilha maza, mai hidimar Rahila su ne,
Dan da Naftali.
26’Ya’yan Zilfa maza, mai hidimar Liyatu su ne,
Gad da Asher.
Waɗannan su ne ’ya’yan Yaƙub maza, waɗanda aka haifa masa a Faddan Aram.
27Yaƙub ya dawo gida wurin mahaifinsa Ishaku a Mamre, kusa da Kiriyat Arba (wato, Hebron), inda Ibrahim da Ishaku suka zauna. 28Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin, 29sa’an nan ya ja numfashinsa na ƙarshe, ya kuwa mutu, aka kuma tara shi ga mutanensa da kyakkyawan tsufa da kuma cikakken shekaru. ’Ya’yansa maza, Isuwa da Yaƙub suka binne shi.
Currently Selected:
Farawa 35: SRK
Highlight
Share
Copy

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in
Littafi Mai Tsarki, Sabon Rai Don Kowa™
Neman Rubutaccen Izini © 2009, 2020 ta hannun Biblica, Inc.
An yi amfani da izinin Biblica, Inc. Neman izinin nan ya game dukan Duniya.
Hausa Contemporary Bible™
Copyright © 2009, 2020 by Biblica, Inc.
Used with permission. All rights reserved worldwide.