YouVersion Logo
Search Icon

Farawa 15

15
Alkawarin Allah da Abram
1Bayan wannan, maganar Ubangiji ta zo wa Abram cikin mafarki cewa,
“Kada ka ji tsoro, Abram.
Ni ne garkuwarka,
kuma ladanka zai zama mai girma.”
2Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mene ne za ka ba ni, ganin cewa ba na haihuwa, wanda kuma zai gāji gādon gidana shi ne Eliyezer mutumin Damaskus?” 3Abram ya kuma ce, “Ga shi ba ka ba ni ɗa ba, don haka bawan da aka haifa a gidana ne zai zama magājina.”
4Sa’an nan maganar Ubangiji ta zo gare shi cewa, “Wannan mutum ba zai zama magājinka ba, ɗa da yake zuwa daga jikinka ne zai zama magājinka.” 5Sai Ubangiji ya fito da kai shi waje ya ce, “Ka dubi sammai ka kuma ƙirga taurari, in har za ka iya ƙirga su.” Sa’an nan ya ce masa, “Haka zuriyarka za tă zama.”
6Abram ya gaskata, Ubangiji kuma ya lasafta shi adalci ga Abram.
7 Ubangiji ya kuma ce wa Abram, “Ni ne Ubangiji wanda ya fitar da kai daga Ur na Kaldiyawa, domin in ba ka wannan ƙasa ka mallake ta.”
8Amma Abram ya ce, “Ya Ubangiji Mai Iko Duka, yaya zan san cewa zan mallake ta?”
9Saboda haka Allah ya ce masa, “Kawo mini karsana, akuya, da kuma rago kowanne yă kasance shi shekara uku ne, da kurciya da kuma ɗan tattabara.”
10Abram ya kawo waɗannan duka a gaban Allah, ya raba kowannensu a tsakiya, ya ajiye su gab da juna, amma bai tsaga tsuntsayen a tsaka ba. 11Sai tsuntsaye masu cin nama suka sauko a kan gawawwakin, amma Abram ya kore su.
12Yayinda rana tana fāɗuwa, sai Abram ya yi barci mai zurfi, sai wani duhu mai kauri mai kuma bantsoro ya rufe shi.
13Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Abram, “Ka sani tabbatacce cewa shekaru ɗari huɗu, zuriyarka za tă zama baƙi a ƙasar da ba tasu ba, za a mai da su bayi, a kuma wulaƙanta su. 14Amma zan hukunta al’ummar da suka yi bauta kamar bayi, daga baya kuma za su fita da mallaka mai yawa. 15Amma kai za ka koma wurin kakanninka cikin salama a kuma binne ka da kyakkyawan tsufa. 16A tsara ta huɗu zuriyarka za tă komo nan, saboda zunubin Amoriyawa bai riga ya cika ba.”
17Sa’ad da rana ta fāɗi, aka kuwa yi duhu, sai wata tukunya mai hayaƙi, mai harshen wuta mai ci, ta bayyana, ta kuma wuce tsakanin abubuwan nan da aka tsaga. 18A wannan rana, Ubangiji ya yi alkawari da Abram ya ce, “Ga zuriyarka na ba da wannan ƙasa, daga kogin Masar zuwa babban kogi, Yuferites ke nan, 19ƙasar Keniyawa, Kenizziyawa, Kadmoniyawa, 20Hittiyawa, Ferizziyawa, Refahiyawa, 21Amoriyawa, Kan’aniyawa, Girgashiyawa da kuma Yebusiyawa.”

Currently Selected:

Farawa 15: SRK

Highlight

Share

Copy

None

Want to have your highlights saved across all your devices? Sign up or sign in