1
Mat 16:24
Littafi Mai Tsarki
Sai Yesu ya ce wa almajiransa, “Duk mai son bina, sai ya ƙi kansa, ya ɗauki gicciyensa, ya bi ni.
Compare
Explore Mat 16:24
2
Mat 16:18
Ina dai gaya maka, kai ne Bitrus, a kan dutsen nan ne zan gina ikilisiyata, wadda ikon Hades ba zai rinjaye ta ba.
Explore Mat 16:18
3
Mat 16:19
Zan ba ka mabuɗan Mulkin Sama. Kome ka ƙulla a duniya, zai zama abin da aka riga ƙullewa a Sama ne. Kome ka warware a duniya, zai zama abin da aka riga warwarewa a Sama ne.”
Explore Mat 16:19
4
Mat 16:25
Duk mai son tattalin ransa, zai rasa shi. Duk kuwa wanda ya rasa ransa saboda ni, zai same shi.
Explore Mat 16:25
5
Mat 16:26
Me mutum ya amfana in ya sami duniya duka a bakin ransa? Me kuma mutum zai iya bayarwa ya fanshi ransa?
Explore Mat 16:26
6
Mat 16:15-16
Ya ce musu, “Amma ku fa, wa kuke cewa, nake?” Sai Bitrus ya amsa, ya ce, “Kai ne Almasihu, Ɗan Allah Rayayye.”
Explore Mat 16:15-16
7
Mat 16:17
Yesu ya amsa masa ya ce, “Kai mai albarka ne, Saminu, ɗan Yunusa! Domin ba ɗan adam ne ya bayyana maka wannan ba, sai dai Ubana da yake cikin Sama.
Explore Mat 16:17
Home
Bible
Plans
Videos