Ya kuma yi wa waɗansu baiwa su zama manzanni, waɗansu annabawa, waɗansu masu yin bishara, waɗansu makiyaya masu koyarwa, domin tsarkaka su samu, su iya aikin hidimar Ikkilisiya, domin a inganta jikin Almasihu, har mu duka mu riski haɗa kan nan na bangaskiya ga Ɗan Allah, da kuma saninsa, mu kai maƙamin cikakken mutum, mu kuma kai ga matsayin nan na falalar Almasihu.