Mutane ba sa ƙuna fitila su rufe ta da murfi. A maimako, sukan ajiye ta a kan wurin ajiye fitila, takan kuma ba da haske ga kowa a cikin gida. Haka ma, bari haskenku yă haskaka a gaban mutane, domin su ga ayyukanku masu kyau, su kuwa yabi Ubanku da yake cikin sama.