1
Yohanna 19:30
Sabon Rai Don Kowa 2020
Da ya tsotsi abin sha ɗin, sai Yesu ya ce, “An gama.” Da wannan fa, ya sunkuyar da kansa ya saki ruhunsa.
Compare
Explore Yohanna 19:30
2
Yohanna 19:28
Bayan haka, sanin cewa an cika kome, kuma domin a cika Nassi, sai Yesu ya ce, “Ina jin ƙishirwa.”
Explore Yohanna 19:28
3
Yohanna 19:26-27
Sa’ad da Yesu ya ga mahaifiyarsa a can, da kuma almajirin nan da yake ƙauna tsaye kusa, sai ya ce wa mahaifiyarsa, “Mace, ga ɗanki,” ga almajirin kuwa ya ce, “Ga mahaifiyarka.” Tun daga wannan lokaci fa almajirin nan ya kai ta gidansa.
Explore Yohanna 19:26-27
4
Yohanna 19:33-34
Amma sa’ad da suka zo kan Yesu suka tarar ya riga ya mutu, ba su karya ƙafafunsa ba. A maimako, sai ɗaya daga cikin sojojin ya soki Yesu a gefe da māshi, nan take jini da ruwa suka fito.
Explore Yohanna 19:33-34
5
Yohanna 19:36-37
Waɗannan abubuwa sun faru don a cika Nassi ne cewa, “Ba ko ɗaya daga cikin ƙasusuwansa da za a karya,” kuma kamar yadda wani Nassi ya ce, “Za su dubi wanda suka soka.”
Explore Yohanna 19:36-37
6
Yohanna 19:17
Ɗauke da gicciyensa, ya kuwa fita zuwa wurin Ƙoƙon Kai (wanda a harshen Arameya ana ce da shi Golgota).
Explore Yohanna 19:17
7
Yohanna 19:2
Sai sojojin suka tuƙa rawanin ƙaya suka sa masa a kā, suka kuma yafa masa wata riga mai ruwan shunayya.
Explore Yohanna 19:2
Home
Bible
Plans
Videos