1
Farawa 37:5
Sabon Rai Don Kowa 2020
Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa.
Compare
Explore Farawa 37:5
2
Farawa 37:3
Isra’ila dai ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowanne a cikin sauran ’ya’yansa maza, gama an haifa masa shi a cikin tsufansa. Sai ya yi masa riga mai gwanin kyau.
Explore Farawa 37:3
3
Farawa 37:4
Sa’ad da ’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.
Explore Farawa 37:4
4
Farawa 37:9
Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”
Explore Farawa 37:9
5
Farawa 37:11
’Yan’uwansa suka yi kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe batun nan a zuciya.
Explore Farawa 37:11
6
Farawa 37:6-7
Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi. Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”
Explore Farawa 37:6-7
7
Farawa 37:20
Ku zo mu kashe shi mu kuma jefa shi a ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, mu ce mugun naman jeji ya cinye shi. Mu ga yadda mafarkinsa zai cika.”
Explore Farawa 37:20
8
Farawa 37:28
Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai ’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar.
Explore Farawa 37:28
9
Farawa 37:19
Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can zuwa!
Explore Farawa 37:19
10
Farawa 37:18
Amma da suka gan shi daga nesa, kafin yă kai wurinsu, sai suka ƙulla su kashe shi.
Explore Farawa 37:18
11
Farawa 37:22
Kada mu zub da wani jini. Mu dai jefa shi cikin wannan rijiya a nan cikin hamada, amma kada mu sa hannu a kansa.” Ruben ya faɗa wannan ne don yă cece shi daga gare su, yă kuma mai da shi ga mahaifinsa.
Explore Farawa 37:22
Home
Bible
Plans
Videos