Farawa 37

37
Mafarkan Yusuf
1Yaƙub ya zauna a ƙasar da mahaifinsa ya zauna, wato, ƙasar Kan’ana.
2Wannan shi ne labarin zuriyar Yaƙub.
Yusuf, saurayi ne mai shekara goma sha bakwai. Shi da ’yan’uwansa, wato, ’ya’yan Bilha maza da kuma ’ya’yan Zilfa maza, matan mahaifinsa suna kiwon garkuna tare. Sai Yusuf ya kawo wa mahaifinsu rahoto marar kyau game da ’yan’uwansa.
3Isra’ila dai ya fi ƙaunar Yusuf fiye da kowanne a cikin sauran ’ya’yansa maza, gama an haifa masa shi a cikin tsufansa. Sai ya yi masa riga mai gwanin kyau.#37.3 Ma’anar Ibraniyanci na mai ado ba tabbatacce ba ne; haka ma a ayoyi 23 da 32. 4Sa’ad da ’yan’uwansa suka ga cewa mahaifinsu ya fi ƙaunarsa fiye da kowanne daga cikinsu, sai suka ƙi jininsa, ba sa kuma maganar alheri da shi.
5Sai Yusuf ya yi mafarki, sa’ad da ya faɗa wa ’yan’uwansa, suka ƙara ƙin jininsa. 6Ya ce musu, “Ku saurari wannan mafarkin da na yi. 7Muna daurin dammunan hatsi a gona, sai nan da nan damina ya tashi ya tsaya, yayinda dammunanku suka taru kewaye da nawa suka rusuna masa.”
8Sai ’yan’uwansa suka ce masa, “Kana nufin za ka yi mulki a kanmu ke nan? Ko kuwa za ka zama sarki, a bisanmu?” Suka ƙara ƙin jininsa saboda mafarkinsa da kuma abin da ya faɗa.
9Sai Yusuf ya sāke yin wani mafarki, ya faɗa wa ’yan’uwansa. Ya ce, “Ku saurara, na sāke yin wani mafarki, a wannan lokaci, na ga rana da wata da taurari goma sha ɗaya suna rusuna mini.”
10Sa’ad da ya faɗa wa mahaifinsa da kuma ’yan’uwansa, sai mahaifinsa ya kwaɓe shi ya ce, “Wanne irin mafarki ne haka da ka yi? Kana nufin ni da mahaifiyarka da ’yan’uwanka za mu zo gabanka mu rusuna maka?” 11’Yan’uwansa suka yi kishinsa, amma mahaifinsa ya riƙe batun nan a zuciya.
’Yan’uwan Yusuf maza sun sayar da shi
12To, ’yan’uwansa suka tafi kiwon garkunan mahaifinsu kusa da Shekem. 13Sai Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Kamar yadda ka sani, ’yan’uwanka suna kiwon garkuna kusa da Shekem. Zo, in aike ka gare su.”
Ya ce, “To.”
14Saboda haka Isra’ila ya ce wa Yusuf, “Jeka ka ga ko kome lafiya yake da ’yan’uwanka da kuma garkunan, ka kawo mini labari.” Sa’an nan ya sallame shi daga Kwarin Hebron.
Sa’ad da Yusuf ya kai Shekem, 15sai wani mutum ya same shi yana yawo a cikin jeji, sai mutumin ya tambaye shi ya ce, “Me kake nema?”
16Yusuf ya amsa ya ce, “Ina neman ’yan’uwana ne. Za ka iya faɗa mini inda suke kiwon garkunansu?”
17Mutumin ya amsa, “Sun yi gaba daga nan. Na ji su suna cewa, ‘Bari mu je Dotan.’ ”
Saboda haka Yusuf ya bi bayan ’yan’uwansa, ya kuwa same su kusa da Dotan. 18Amma da suka gan shi daga nesa, kafin yă kai wurinsu, sai suka ƙulla su kashe shi.
19Suka ce wa juna, “Ga mai mafarkin nan can zuwa! 20Ku zo mu kashe shi mu kuma jefa shi a ɗaya daga cikin rijiyoyin nan, mu ce mugun naman jeji ya cinye shi. Mu ga yadda mafarkinsa zai cika.”
21Sa’ad da Ruben ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă cece shi daga hannuwansu. Ya ce, “Kada mu ɗauki ransa. 22Kada mu zub da wani jini. Mu dai jefa shi cikin wannan rijiya a nan cikin hamada, amma kada mu sa hannu a kansa.” Ruben ya faɗa wannan ne don yă cece shi daga gare su, yă kuma mai da shi ga mahaifinsa.
23Saboda haka sa’ad da Yusuf ya zo wurin ’yan’uwansa, sai suka tuɓe masa rigarsa, rigan nan mai gwanin kyau da ya sa, 24suka kuma ɗauke shi suka jefa a cikin rijiya. To, rijiyar wofi ce, babu ruwa a ciki.
25Da suka zauna don cin abinci, sai suka tā da idanu, suka ga ayarin mutanen Ishmayel suna zuwa daga Gileyad. An yi wa raƙumansu labtu da kayan yaji da na ƙanshi, suna kan hanyarsu za su Masar.
26Yahuda ya ce wa ’yan’uwansa, “Me zai amfane mu in muka kashe ɗan’uwanmu muka ɓoye jininsa? 27Ku zo, mu sayar da shi wa mutanen Ishmayelawan nan, kada mu sa hannuwanmu a kansa; ban da haka ma, shi ɗan’uwanmu ne, jiki da jininmu.” Sai ’yan’uwansa suka yarda.
28Saboda haka sa’ad da Fataken Midiyawa suka iso, sai ’yan’uwansa suka ja Yusuf daga rijiyar, suka sayar da shi a bakin shekel#37.28 Wato, kamar ons 8 (kamar kilo 0.2) ashirin na azurfa wa mutanen Ishmayel, waɗanda suka ɗauke shi zuwa Masar.
29Sa’ad da Ruben ya dawo wurin rijiyar, sai ya tarar cewa Yusuf ba ya can, sai ya kyakkece tufafinsa. 30Ya koma wurin ’yan’uwansa ya ce, “Yaron ba ya can! Ina zan bi yanzu?”
31Sai suka ɗauki rigar Yusuf, suka yanka akuya suka tsoma rigar a cikin jinin. 32Suka ɗauki rigan nan mai gwanin kyau, suka kawo wa mahaifinsu suka ce, “Mun sami wannan. Ka bincika shi ka gani ko rigar ɗanka ne.”
33Ya gane shi, sai ya ce, “Rigar ɗana ne! Waɗansu mugayen namun jeji sun cinye shi. Tabbatacce an yayyaga Yusuf.”
34Sa’an nan Yaƙub ya kyakkece tufafinsa, ya sa tufafin makoki, ya kuma yi makoki domin ɗansa kwanaki masu yawa. 35Dukan ’ya’yansa maza da mata, suka zo don su ta’azantar da shi, amma ya ƙi yă ta’azantu. Ya ce, “A’a, cikin makoki zan gangara zuwa kabari#37.35 Da Ibraniyanci Sheol. wurin ɗana.” Saboda haka, mahaifin Yusuf ya yi kuka saboda shi.
36Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin ’yan gadin fadar Fir’auna.

Цяпер абрана:

Farawa 37: SRK

Пазнака

Падзяліцца

Капіяваць

None

Хочаце, каб вашыя адзнакі былі захаваны на ўсіх вашых прыладах? Зарэгіструйцеся або ўвайдзіце