Don daga ciki ne, wato daga zuciyar mutum, mugayen tunani yake fitowa, kamar su fasikanci, da sata, da kisankai, da zina, da kwaɗayi, da mugunta, da ha'inci, da fajirci, da kishi, da yanke, da girmankai, da kuma wauta. Duk waɗannan mugayen abubuwa daga ciki suke fitowa, suna kuwa ƙazanta mutum.”